MAMUHGEE 3

*_Mamuhgee3_*
Jan qafarsa data riqe yayi Yana ‘dingisawa a duduqe ya nufi qofar gidan nasa Yana tura qyauren yaji yabude yasaki wata irin qwafa yana cewa”
Nibansan menayiwa ruqayya ba zataimin wannan sakayyar ta ha’do zuri’a da dangin marasa Imani gashinan ‘danta zai kasheni kwanana Basu qareba.
Tunda yaji qofar abude yasan sunkama bingo dinsu shiyasa yashigo Kai tsaye
Itama iya talatu tsabar Rashin ‘da’a ga miji sai yanxu daya gama hasarewa zata bude qofar dakinta.
Tsuke fuska yayi ya kwadawa Nadiya Kira tafito tana sunkuyar dakai sbd sanin dazu Bata fitoba daya kirata.
Ciki ciki yayi da qananun idanuwansa yafara zuba mata fadan Rashin arziki kafin yasata ta debo masa ruwa ya wanke jikinsa da duk yabaci da kwata ya dudduqa ya qarasa ‘daki Yana sakarwa talatu nata fadan a kaikaice itadai Bata kulasaba sbd gabaki daya ranta har lokacin abace yake.
Haka Suka kwana kowa na hararar Dan uwansa.
Qarfe 6 na safe ta Dora ruwan kunu a babbar tukunya tahau aikin sharar gidan kafin ta bude dakin kaji da akuyoyin iya talatu Suka fito Suka hau walwalarsu a tsakar gidan tana cikin wanke wanke yashigo gidan wuyansa rataye da towel milk da brush tareda Colgate toothpaste.
Kallo daya tayi masa taci gaba da aikinta sbd batada muryar ko gaisuwa shiyasa iyakacinta da kowa ido.
Ruwa yadiba a qaramin plastic bucket yakoma dakinsa ya zura heater ya kunna ya fito qofar gidan inda yake cikeda yaransa wasu na karyawa wasu na wasa makamansu sbd taron yau.
Wata kujerar busashen katakoce dake kafe acikin qasar gurin alamar tariga tashiga qasa bazata taba daukuwaba ga sulbi sbd alamar dadewarta da qarkonta
JJ yayi saurin dauke wuqar daya Dora gurin Zaki ya zauna ya karbar wuqar Yana bin bakin kaifinta da ido yace”
JJ wannan qwamar taka yau cikin takalmina zan sata akwai Wanda dikko keson nayiwa zanen yorbawa agurin taron.
Dariya JJ yayi shida Nanu..
Nanu yace”
Sarki kowaye wannan za’ayiwa na yorbawa tasa taqare tunda sarkine dakansa zai masa aiki.
Wani irin murmushin gayya yayi Wanda ya lotsarda kumatunsa ya ‘daga wuqar Yana kallo yace”
Yau uwarsa bacci zatayi tana sauke ajiyar zuciyar kukan dazata yini tanayi.
Dukkaninsu dariya Suka sheqe da ita suna”””Allah ya tarwatsa maqiyanka sarki.
Ruwa Nanu yakawo masa yafara brush dinsa daganan zaune sukuwa nan wasu Suka cigaba da gyara makamansu.
Kallon JJ daya qura masa ido yayi yasaki wani slow murmushi Yana jingina da bayan kujerar yace”
Yaya akayine magajin Zaki.
Cikeda jin dadi jj yashafo tarin sumar kansa da akayiwa kitson cuku bayan anyi dying dinta zuwa baqi da brown yace”
Neyo yau kwarjinin naka bazai Barima ko alh dikko yafika cikawa mutane idoba.
Murmushi yasakeyi Yana shafo gemunsa na tsantsar ta’addancinsa dayake tarawa ya miqe tsaye tareda nufar qofar gida zai shige yace”
Magajin Zaki Kaine kadai kakewa Zaki kwarjini bayan Kai Babu ubanda bazan ketawa rigar mutunci ba ciki kuwa harda tsohon najadun gidan nan.
Shigewa yayi jj yabi bayansa da kallo Yana girmama girman qauna da matsayinda neyo yakedashi arayuwarsa sbd shine yamaidasa mutum yacirosa daga basifa da balain dayafi ta’addanci,
Yazame masa uwa uba tareda cike duk wani gurbi na Dan uwa dayake buqata aduniya shi
yasa zai iya sadaukarwa da neyo rayuwarsa.
Wanka yayo yafito daga bayin tsakar gidan sanyeda threequater wando da qaramin tawul rataye a wuyansa.
Kallo daya Nadiya tayiwa qaqqarfan jikinsa dake bayyanarda qarfinsa,
Wani dogon tabone da sarar Adda yake zane a qirjinsa har zuwa gefen qugunsa Wanda aka ta6a yimasa lokacin daya fara haduwa da JJ sadai Wanda yayi masa sarar yananan yarasa qafafuwansa har abada Dan kuwa Saran rage yaran neyon sukaiwa qafafuwansa Allah yasa yanada kwana agaba.
Wannan tabo shine tabo ‘daya dake jikin neyo sbd tsananin tsaron dake taredashi na yaransa Wainda Suka sadaukarda rayukansu akan sarkinsu.
Cikin wani tsinannan army three quarter da baqar riga Mara hannu data bayyanarda qwandarsa dake bawa baba tsoro yafito fuskarnan sanyeda baqin goggles yafito inda qofar gidan take cike dam da duk wani ‘dan daba dake qarqashin ikonsa agarin kowane da kalar mugun makaminda ke soke ajikinsa atake guri yadau ihu da kirarin sai sarki…..
Wuqarda JJ ke miqo masa ya karba Yana sokewa cikin takalminsa Yana qarasawa jikin motocinda alh dikko ya Basu Dan hidima
Yana shiga JJ yashiga nan kowa yasamu Suka shiga atake Suka cike golf guda da bus biyu tareda Hilux ‘daya Suka wuce cikin wani matsiyacin gudu dayasa mutane kakkaucewa da gudu suna matsarda kayan sana’arsu.
Baba ma Yana tashi yau din yaji qafarsa taqara tsami radadi take masa sosai ya dingisa ya fito tsakar gidan iya talatu dake zaune suna lissafin kudin kunu da Nadiya ta kallesa a dage tana dakatawa daga lissafin tace”
Wannan Kuma wane irin sabon salone kake mana gurgunta?
Qin tankata yayi yakalli Nadiya data sauke Kai Yana hada ‘yan biyar biyar guri ‘daya yace”
Ke tashi kaimin ruwa bayi nayi wanka inada gurin zuwa.
Tashi tayi ta nufi bokiti
Iya talatu tasake kallonsa tace”
Magana fa nayi kanaji kayi uwar shegiya Dani.
Tsuke fuska yayi Yana sake dingisawa yace”
Talatu wlh wata Rana Saidai kijiki cikin takaba tsundum matuqar ba rabuwa mukayi da Zaki ba,
Wannan masifa tayi yawa
Gabaki daya tsufa neman damqata yakeyi sbd masifar gidan nan,
Ga naki gana ‘yayanki gana wannan sarkin dababu rawani sai neman gigita rayuwata yakeyi.
Kallonsa talatun tayi tana girgiza Kai tace”
Ai wlh kwadayinkane da zalamarka ta abin duniya takaimu ga haka,
Qiri qiri katura ruqayya aikatau qasar inyamurai gashinan takawo Mana abinda yaci uwar uban kwadayinmu ta mutu ta barmu da jidalin qaqa nikayi
Gashi kaikuma Allah bai samaka danganar tsayawa inda kakeba shiyasa muke azabtuwa muda tattalin arzikinmu konace tattalin arzikina tunda Kai bayan matacciyar tsohuwar rigar ba abinda ka aje.
Sake tsuke fuska yayi yace”
Wannan tattalin arzikin naki na hainci gwara na mutu da tsohuwar rigar tawa danayi irinta.
Yanxu dai naji wannan Ina kake cewa zakaje da gurguwar qafar?
‘dan sake fuska yayi Yana cewa”
Yau wani gagarumin taro za’ayi daya hada kaf dukkanin qusoshin qasa dasukaci Suka tada wuya musamman sbd taron na alh dikko Dilla ne
Dan haka dole naje Dan kuwa yau ‘yan maula ma kasuwarsuce
Bazan zauna acinye duniya badaniba koba komai da ‘dingisarnan zan qara lankwashewa nafi kowa samu.
Baka daddara ba kenan””tafada tana hararar gefensa.
Yana kama hanyar bayi yace”
Daka mutu gwara kazama biri.
Bayin yashege Bata sake kulasaba Suka cigaba da lissafi sbd kullum ita arayuwarta a lissafi ta qare.
Cikin wani yadin ‘dan Madina kalar baqi da siminti yafito da babbar rigarsa ta kullum ya sanyo hularsa datai mugun masa yawa wadda itama gurin maular yasamota.
Wani irin zaku’do kafada yakeyi Yana gyara babbar rigarsa da hularsa qafafunsa da fuskarsa kuwa tsaf sukaji Vaseline sai maiqo sukeyi ya kalli Nadiya dake gefen talatu tana gyaran shinkafa yace Ina takalmin Zaki na jiya daya zuciya ya wurgo?
Kallonsa sukayi atare itada iya talatu Saidai Kuma basuyi mamakiba saboda sanin waye baban.
Miqewa tayi ta nufi inda ta ajiyesu kusada dakinsa ta dauko takawowa baban ya karba Yana cewa”
Wannan dinkin dakikayi bai tsukuba Amma hakan zaiyi maleji.
Sakawa yayi batareda yakalli talatu ba ya baza rigarsa ya wuce sbd ganin baqin ciki talatun ke yimasa.
#MAMUH