NOVELSUncategorized

MAMUHGEE 5

*_Buri daya_*
*_Mamuhgee5_*
Cikinta na wata bakwai Abu yayi tsanani Dan kuwa kumburi ne tayi tako Ina Wanda ya sauya kamanninta tsaf Dan kuwa ko qafafuwanta daqyar take dagawa.


Lokacinda abin yayi tsamari yahada kudi daqyar yakaita asibitin kudi atake Suka Bata gado sbd ganin mummunan halinda take ciki Suka tabbatar masa lallai dole za’ayi mata aiki acire abinda ke cikinta Dan kuwa za’a iya rasasu su biyun sbd sanyi yakama qashi da bargon jikinta sosai ta yanda yazamo ha’dari ga rayuwarta data abindake cikin,

Kudi naira dubu saba’in Suka masa total tareda basa telar biyan kudin.

Kallon telar yasakeyi tareda rintse idanuwansa dasukai mugun jajir suna neman zubo ruwan tausayin ruqayyarsa.

Fitowa yayi asibitin Yana tafiya da qafa kan hanya Yana tunanin shida ko dubu ‘daya baida ina zai samo dubu saba’in?.

Zama yayi bakin wani babban shagon siyarda kayan masarufi ya rafka tagumi baiko damu da ranar dake dukansaba.

Yafi awa biyu zaune agurin har wasu na basa sadaka idan sun fito atunaninsu bara yakeyi.

NEYO”””yaji ankira sunansa ya dago ahankali cikeda sanyin jiki.

Yayi saurin miqewa Yana qoqarin tattaro kuzari yake kallon Wanda yakira sunansa Yana cewa”

Dikko Kaine nake gani haka????

Rungume juna sukayi dikko na sakin wata dariyar jin dadi ya janye Yana kallon neyo daga qasa zuwa sama yadan yamutsa fuska Yana cewa”

Neey what’s happening?
You look terrible??

Numfashi neyo yasaki tareda gyara zaman rigarsa data gama yimasa yawa yace”

Dikko matata na asibiti aiki za’ayi mata sbd ceto ranta da abinda ke cikinta Kuma ana neman kudi nera dubu saba’in Wanda wlh banidasu banida inda zan samesu.

Jansa dikko yayi sukaje mota yashiga tareda bude masa shima yashigo ya tayarda motar Suka fara tafiya 
Batareda ya juyo daga kallon hanyaba yace”

Neyo kasan ni,
Kasan yanda nake Kuma bazan taba canxawaba,
Bana aikinda nasan banada riba Dan haka bazan iya baka dubu saba’in ba kyauta Saidai zanbaka wani aiki dazakai kasamu dubu ‘dari biyar Wanda zaka biya kudin aikin matarka harma kayi lalurar komai na bayan haihuwar.

Kallonsa NEYO yayi batareda mamakiba sbd yasan waye dikko
Yasan akan kudi baida yarda ko ragi ko akan waye,
Duk aikinda zaiwa dikko yabashi dubu dari biyar yasan ba qananan maqudan kudi shi dikkon zaisamuba Saidai yasan aikin dikko Babu Wanda ba gur6atacce neba
Dole wani mugun abun ne zai masa.

Sauke numfashi yayi yakallesa yace”

Wani irin aikine??

Wani sample na maganin chloeziadenes zaka samomin a matatar magunan qasa dake cikin Lagos 
Na dauko 6oyayyun ma’aikatan daga qasar China zasumin irinsa a sirrintaccen kamfanin buga maganin bugina zamu sakarwa mutaneshi duk da Sha kawai zasu riqayi basusan bugineba Babu maganin cutar dazai ringa musu.

Kallonsa NEYO yayi tsawon mintuna hudu Yana jinjina Rashin Imani da mugun son abin duniya na dikko sbd kowace gurbatacciyar sana’a ya iya bayako jin shakku da fargabar yanda mutane ke rasa rayukansu akan abubuwan dayakeyi.

Girgiza Kai yayi kawai sbd shi yanxu bayako sha’awar rayuwa da dikkon,

Kai tsaye yace”

Fadamin inda zanje nakaima idan nasamo,
Kuma ka tabbatarda kudina nanan ajiye hannunka ayau zan kawo maka sample din da yardar Allah.

Dariyar jin dadi dikko yayi sbd shiyasa yake mutuwar son mu’amala da neyo ya iya aiki ba tsoro ba shakka ga sa’a dayakeda ita.

Bakin wani qaton factory dikko ya tsaya da motarsa yacewa neyo”

Idan kadauko kasameni bayan gari gidan mai mai suna Dilla filling station,
Best of luck.

Maimakon yaga neyo ya fita saiyaga ya fada wajen motar Yana mulmulawa kamar baida Rai take kansa dake bubbuguwa da dutse yafara fashewa bai damuba sbd ganin masu tsaron gurin suntaso suna qoqarin taimakosa sbd sunga lokacin aka jefosa daga cikin motar data gudu.

Dikko bai tsaya komaiba ya fige motarsa da mugun speed Yana wani shuumin murmushi sbd yasan aikine neyo yafara.


Daqyar Suka taresa suna qoqarin dagosa sbd tuni fuskarsa ta baci da jini kamar Wanda aka Dade ana ganawa azaba,

Sam basuga numfashi atareda shiba nan Suka daukosa sukayo ciki dashi sbd basuda fargaba ko tunanin komai akan factory dinsu tunda sumsan tsaftataccen aiki sukeyi ba gurbatacceba bare suji shakkar shigoda wani.

‘yan lokitocin dake cikin factory din Suka dubasa sukai masa dressing shidai yanajinsu yaqi motsawa Saidai numfashinsa dake fita ahankali alamar dawowar numfashin.

Bayan futar dukkaninsu daga ‘dan dakinda Suka taimaka masa ya miqe da sauri tareda fara bincike cikin dakin cikin sa’a yasamu uniform din ma’aikatan gurin yadauki daya yasa da sauri tareda Jan hular uniform din yarufe fuskarsa yafito Yana sunkuyar dakai sbd kar aganesa atake ya saje da ‘dinbin ma’aikatan dake gurin.

Kai tsaye computer room dinsu ya nema ya sidada yabude qofa ya leqa yaga numbern room dinda samples suke yafito ta nufi room 17 inda yaci babbar sa’ar security din qofar abude yake wani doctor Yana ciki da sauri yafada dakin 
Doctorn na juyowa yakai masa wani mugun duka a hanci atake likitan ya yanke jiki ya some 

Nan yafara dudduba sample dinda dikko yace
Yanayi Yana kallon qofa.

Takun tahowa yaji daidai lokacinda yagansa yayi saurin dauka daga cikin wani box mai kamar fridge yasaka cikin wandonsa yayi saurin ficewa.

Daqyar ya mayarda kansa dakinda aka barsa yayi saurin cire uniform din ya mayarda kayansa yakoma Yana kwantawa aka bude qofar.

Yanaji an buga alarm na danger ya miqe ya fito da satar jiki ya iso gate sukuwa security Suka bude masa ya fice.


Gudu yakeyi sosai sbd wajen garine sosai
Kusan kilometers tara ne tsakaninsu da cikin gari.

Daqyar ya kawo titi Yana hango mota tafe yayi sauri daga hannu Saidai bai gama aje hannunba motar tayi sama dashi yafado gefen titi jini na fita jikinsa sosai.

Atake mai motar ya gudu yabarsa nan
Rai hannun Allah.

Jini yake fitarwa sosai gashi ko motsi baya iyayi atake yasan mutuwa zaiyi Saidai yayi baqin cikin mutuwa cikin wannan yanayin gashi ruqayya da cikinta baisan wane hali zasu shigaba..

Dishi dishi yake gani idanuwansa na neman rufewa yaga dikko yazo kansa ya tsaya tareda wasu yaransu biyu.

Cikin Rashin tausayi dikko ya girgiza Kai yace”

I’m really sorry best friend Amma Kona daukeka yanxu lalura zaka zamarmin gskia sbd dai mutuwa zakayi Dan haka bazanyi hasarar kudina gurin kaika asibiti muyita wahalar banxaba koba komai kaga Allah nasona da yawa shiyasa hakan tafara sbd kar kudina dazan baka suzama west…

Kai ku cajesa kuciromin sample Dina.

Yanaji Yana gani Suka ciro sample din daga jikinsa Suka wuce Suka barsa hawaye na gangarowa daga idanuwansa harsuka rufe.Asibiti sunyi jiran dawowarsa har kwana biyu ba labarinsa tuni Suka sallameta nan hankalinta yayi mummunan tashi tafara nemansa lungu da saqo cikin abeokuta
Ga ciwo ga nauyin ciki Amma haka take yawon nemansa Takoma kamar mahaukaciya tun ana Bata sadaka tana qin karba harta fara karba.

Bayan wata daya wani abokin aikinsa daya gaji da zaryar datakeyi gashi yace Takoma gida taqi ita saitaga neyo
Kawai sai yazo yasanar mata anga gawarsa hanyan Lagos sunje sunmasa sallah sun rufesa
Ban yabata kudin mota yace Takoma gida arewa.

Tanajin haka tayi tawakkali Bata tsaya Bata lokaciba bayan kwana biyar tadawo arewa.

Ranar data isa agalabaice ta isa sbd kwana biyu ahanya suna tafiya kodata iso tafara ficewa hayyacinta.

Talatu na zaune tsakiyar gida da tsohon cikinta tana Shan radio taganta tashigo tana daddafa bango.

Gyara zama tayi tareda kallonta dakyau ta tabbatarda ita dince ruqayya.

Batayi mamakiba ta kalli qofar dakinta tace”

Dattiya saika fito kaga baqin magribar dasuka sauka 
Dama nafada komai Daren dadewa saita dawo 
Gashinan harda ‘dan kawu aka samo maka.


Fitowa yayi Yana saka hula akai Yana ganin ruqayya ya zaro qananun idanuwansa akan cikinta hankali tashe yace”

Ruqayya mezan gani ajikinki?
Nida nasaki jiki duk Randa Zaki dawo da ‘dibbin dukiya Zaki dawomin shine kika kwaso min wannan iskancin Lagos ‘din???to wlh ko zama bazakiyiba dashi acikin gidannan maza wuce tun kafin nayiwa shegen jikinki duka…

Wato tunda na hanaki auren tubabbe shine kika ‘daukomin abinda yafi auren tubabben kunya da takaici.


Wata dariya talatu tasaki tana cewa”

Dan Allah da gaske dattiya kasan kunya dahar kake gudun abin kunya?

Rufe ido yayi yafara zazzaga mata Rashin mutunci sbd shi cikin bai wani damesaba kamar yanda tadawo hannu rabbana kamarma wata mabaraciya…

Cikin tsananin azaba ta durkushe gurin sbd naqudar data dirar mata lokaci ‘daya.

Beda yanda zaiyi Dole yaje yakirawo shafa’atu matar idi da innaje sukazo dole akai cikin dakinta tun na budurcinta Suka fara qoqarin karbar haihuwarta.

Cikin ikon Allah ana Kiran magriba ta haifi yaronta Wanda yake fari tas jinin Igbo tamkar mahaifinsa.

Cikin qanqanin lokaci aka shiryata 
Dattiya da fada dakomai yasiyo kala biyu da sabulun jarirai guda daya da man jarirai yakawo aka sawa yaron.

Dattiya kuwa Duk yanda yake fada da kukan baida dole yake yimata wasu abubuwan itada jaririnda da kanta tayiwa yaronta huduba da sunan mahaifinsa wato *_ALEEYU HAYDAR NEYO_*.

Yanaji yana gani ya yanka mata ‘dan ragonsa Yana sake jaddada mata aro yabata zata biyasa kudinsa tace taji idan ta warke zata biyasa.


Ahaka suka fara Gina wata sabuwar rayuwar mai cikeda qalubale gashi bayan haihuwarta da wata biyu talatu ta haifi namiji itama aka saka masa suna dahiru.

Dole ta mayarda hankali tafara sana’a sbd lalurarta data Zaki Dan kuwa tun Yana yaro take kiransa Zaki tunda sunan babansa yaci,

Babu Wanda yataba tambayarta ya akayi tasamu cikin Zaki sai itama Bata bi takan zancenba tafara sanointa Dan tallafawa rayuwar ‘danta daya girma harta sakashi makarantar primary.

Zaki ya taso a cikakken marajin yaro sbd ganin irin rayuwarda akeyi acikin  gidansu ta Rashin taimako da tausayi kowa tasa ta fishesa akeyi a gidan,

Idan kanada kaci idan bakada ka kwana da yunwa,
Ga shegen son kudi da abun duniya tsakanin talatu da dattiya baasan Wanda yafi waniba.
#MAMUH

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button