Uncategorized

MATAR UBA 21

Ad

_____

💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

 “`NOT EDITED

CHAPTER 21“`

💦💦💦💦💦💦💦💦

NOT EDITED

” To am sorry yanzu me abunyi?”

Iska ya hura Mai zafi kana yace “zan Fara zuwa aikin”

Mamakine ya kama faisal anfi shekara uku Ana bin say ya karb’i aikin Nan Amma Taki kwasam Rana d’aya ya amince tabbas Yana kaunar yarinyar Nan sosai.

“Toh hakan yayi Amma ka Fara Samar da hajiya tukanna kaji me zata ce”

” Okay insha Allah zanyi hakan,sai da safe”

A tare suka katse wayar.

💦💦💦💦💦💦💦💦

“Gaskiya nana al’amarin mutummin Nan ya fara bani tsoro yau ki manin sati biyu kenan Yana bacci sannan babu Wanda yazo neman sa”

” Abban Yesmin Nima abin na damina ,ace babu Wanda yazo neman sa,Allah dai ya bashi lafiya”

Ya Asma da “Ameren”

Faisal da Hashim na gani zaune,Hashim ya bugu uban tagumi,Faisal Ne ya dafe kafad’ar sa yace “Take it easy man,komai yayi zafi maganin sa Allah”

Huci yayi Mai zafi kana yace “yazanyi Faisal,wallahi duk duniyar ta daina min dad’i,na tsani yarinyar Nan na tsane ta and now I have to pretend Ina son ta duk bugun numfashina soyayyar Asiya ke karuwa a zuciya ta a yayin da kiyayya da tsanar Safiyya ke karuwa a Raina,wallahi wallahi idan wani Abu ya same ta sai na ga gatan su wallahi sai na say a d’aure ta da ita da uwarta”

“Allah shi kyauta,Amma ya kukayi da mummy ne ta amince da maganar auren kuwa?”

” Bata amince ba” Yana maganar ya d’auki juice dake gaban sa ya tsiyaya a glass cup sai da yayi sipping kana ya d’aura da fad’in “Na rasa yanda zanyi yau da two weeks Kenan,Ina gudun Kar Safiyya ta gane cewar game muke”

“Kar ka damu insha Allah baza ta gane  ba,Kai ma dai Hash baka jin shawara wallahi,tun da ka dawo daga kasar waje ake ta binka ka Fara zuwa company kaki zuwa ka bar bare akai baka san rayuwar Nan tamu ta lalace

ba mutum ba abin yarda bane ba”

“A wannan halin zan Fara aiki? Ta ina zan Fara bazan ma iya concentrating ba”

” Hakane Amma Ina da shawara,Ina ga shine kad’ai mafita da ya rage Mana”

Ajiye glass cup d’in dake hannun sa yayi yace “uhmn Ina sauraron ka”

Magana suke kasa kasa Wanda na kasa ji, (nace idan tayi tsami zanji)

Murmushi Hashim yayi yace “Kai Alhamdulillah nagodewa Allah da ya had’a Ni da aboki irin ka hakan kawaii za a yi”

” Toh yanzu kaga bamu ga ta Zama ba,tashi zakayi  Muje mu nemi mafita”

Tashin su ke da with wayar Hashim ta Fara ringing Ciro wayar yayi daga aljihun sa Yar karamar tsaki ya jaa like, Faisal ke kallon sa irin kallon wa ke Kiran ka? 

Chan ciki yace “yarinyar Nan ta dame ta takurawa Rayuwata”

Cikin kallon rashin fahimta Faisal yace ” Wace yarinya Kenan fa?”

“Badiyya Mana ban San me take nema a guna ba,kwanaki ta daina kirana yanzu kusan sati uku Kenan take damina kullum sai ta Kiran Sam Bata da zuciya wallahi mtsww”

Murmushin gefen Baki Faisal yayi yace ” Haba Kai kuwa sati uku fa kace? Kuma baka damu da kaji Kiran da take maka ba?”

” Ban damu ba,bana son ta ita Kuma ta makale min,Ni ban San meyasa matan yanzu Basu da kunya ba,Wai ace su Rika bin na miji da wanne zanji Dan Allah,da shaid’aniyar Nan Safiya zanji ko da ita?”

” Duk da hakan dai Badiyya Bata chanchanci Haka daga gare ka ba, yarinyar Nan ta nuna maka so iya so sabida laifi kalilan da ta maka sai is d’auki Karan tsana ka d’aura Mata, Allah da kansa kullun cikin sab’a Masa muke kuma yake yafe Mana,kayi hakuri ka saurare ta ko da kuwa baza ku cigaba da soyayya ba”

Huci Hashim yayi yace “Amma Faisal kasan babu macen Dana so a Rayuwata kamar Badiyya,naso ta irin son da ban tab’a yiwa wata ‘ya mace a duniya ba,Amma taci amanata”

” Na sani, na sani Hashim let the bygones be gone please kamanta da duk wannan ya kamata ka saurareta kaji me ke faruwa”

” Toh naji zan kirata Amma ba yanzu ba”

” To ba matsala take your time but jar fa ya wuce yau d’in Nan”

” Naji naji mu tafi ko?”

Murmushi kawaii Faisal yayi yabi bayan Hashim.

Kwance take ajikin Sa suna kallon American film Mai suna RUSH HOUR, wayar Abban Yesmin ke ringing tun d’azu ankira yafi sau uku,ganin sabon number shiysa bai d’aga ba,Nana ganin Kiran yayi yawa Tace “Ya kamata ka d’aga Kiran Nan Naga Mai Kiran a matse yake”

Yar karamar tsaki yayi yace Miko min please” tashi tayi Mika Masa kana ta koma ta kwanta a jikin sa, kwanciyar ta yayi dai dai da shigowar wata Kiran, duka biyu ya d’aga da “assalamualaikum”

Daga d’ayan ‘bangaren aka amsa da ” wassalam am sorry to disturb you sir”

“Is ok who am I talking to?”

Ya amsa da “Dr Hassan from Doma hospital”

” Oh am so sorry,how may I help you?”

“Good news sir, the person you brought to our hospital just woke up”

Abban Yesmin min baisan sanda ya ture ta ya zauna ba yace “Are serious? When did he woke up?”

“About an hour ago”

” Okay okay am on my way now”

Sai da ya katse wayar yaga ya ture ta har kasa ita kuwa sai tura Baki take Taki tashi Yana ganin halin say take ciki da sauri ya nufe ta Yana fad’in “am sorry baby” had’e da d’aga ta ya d’aura ta akan dugawar sofar da suke zaune akai, bata ce Masa komai ba a Karo na biyu ya kuma fad’in “sorry baby Baki ciwo bako?”

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button