Uncategorized

MATAR UBA 22

 ????????????????????????????????     *MATAR UBA*

????????????????????????????????

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*????MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION????????️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

 “`NOT EDITED“`

 “`CHAPTER 22“` 

????????????????????????????????

Karfe Tara chip suka Isa asibitin a office d’inta ta ajiye ta kana ta fita don duba patient d’inta masu matsala irin na asiyah, bayan ta gama ta koma office, zaman ta ke da wuya ta ga Kiran hashim, cikin sauri tayi picking Bai jira tace komai ba yace “Kina Ina? Na shigo asibitin ku?”

Tace “Ina office d’ina gani nan zuwa”

” No ki fad’a min inda kike kawaii am coming” 

Nan ta Masa kwatance,ya katse wayar.

????????????????????????????????

……….. Asiyah Tace “Aunty Ina Jin fitsari”

Tace amsa da to, da taimakon ta ta shiga ban d’aki kana ta fito tana jiran ta, knocking d’in kofan da akayi ne ya dawo da ita daga tunanin da ta Lula, da sauri ta bud’e kofar ganin muradin ranta sai da taji kirjin ta ya buga, Shima haka Hashim d’in yaji gani yayi a cikin shekara uku duk ta sauya ta Kara kyau kamar ba ita, gyaran murya yayi yace “Ina yarinyar take?”

“Tana ban d’aki, baza ka shigo bane?”

“Da na so ganin ta ne amma Shikenan kizo Muje mota na Baki cheque ko?”

Ta amsa da “toh, barina da duba ta”

” Okay idan Kun Gama Ina mota a parking space” ta amsa da “okay”

Yana kaina ya juya ya fita.

Asiyah shiru tayi tana sauraron muryar kamar tasan muryan nan, ta Kira sunan Badiyya Amma dake kofan a rufe yake shiysa Bata jiba, knocking kofar tayi Tace “Asiyah kin gama?”

Ta amsa da “eh”

Shigowa tayi ta fito da ita daga ban d’akin ta zaunar da ita Tace “d’an jirani Ina zuwa ko?”

Ta amsa da “Toh”

Bayan ta fito bud’e motar tayi ta zauna a gaba da sallama ta shiga ta zauna ya amsa chan chaki,kamshin tiraren jikinta ne ya buga hancin sa har Saida ya koma ya d’an kwanta, sun dad’e a Haka kana ya d’ago ya kalle ta yace “Million biyu zai ishe ku?” 

Chan ciki ta amsa da “Eh zai Isa”

Check ya zaro a aljihun motarsa ya rubata check d’in three million ya Mika Mata,mamaki ne ta kamata Tace “Hash 3 mil? yayi yawa fa”

“Wannan ba komai bane Badiyya, anything for you”

‘dago wa tayi da sauri tace “Anything for me?”

Kallon ta yayi Ido ciki Ido yace “Yes anything for you”

Marairaice fuska tayi Tace ” But why? Why Hashim baza ka yafe min laifin da nayi maka ba” idon ta fal da kwalla.

Kad’a Kai yayi idon sa Nan da Nan idon sa yayi jaa yace “Taya kike so na manta abinda idanuna suka gane min ba? Bazan tab’a manta da wannan ba”

” Hashim na fad’a maka wallahi ba abinda kake tunani bane ba”

” Look Badiyya, kin bukaci kud’i a wurina na baki, please get out of my car”

” Hash….”

” Get out…..” A tsawace,har Saida ta tsorota cikin sauri ta bud’e kofar ta fita,tana share kwallan da suka zubo Mata a ido.

Kai tsaye office d’inta ta nufa ta tarar da Asiya ta had’a Kai da gwiwa sai aikin kuka take, cikin sauri ta karasa inda take, Tace “Asiyah… Asiya me ya same ki?”

Cikin shesshekar kuka Tace “Aunty Ina tausayawa Rayuwata ne bani da kowa banda komai,mutum d’ayane ya rage min a rayuwa ta na tabbata Yana nema na, Ina son ganin sa Amma bana so ya ganni a haka”

” Wanene wannan ki fad’a min sunan shi ko zan Nemo Miki shi?”

” Hashim  Ahmad…..”

Kwankwasa kofar da akayine ya same ta kasa karasa maganar ta, Badiyya ce tace “Yes come in…”

Ganin Wanda ya shigo ya sa tayi saurin mikewa, gyaran murya yayi yace “Kin manta wayar kin motata” Yana maganar had’e da Mika Mata,har ya juya zai fita Tace “Hash ganan yarinyar da za’ayi wa surgery” 

A hankali ya juya ganin wacce idonsa ke nuna Masa yasa yayi suman tsaye, Badiyya Tace “Sunan ta Asiyah”

Ganin baya Jin ma maganar da take Tace “Hashim”

A razane Asiyah ta tashi ta tsaya, Badiyya banda kallon su ba abinda take Baki na rawa Asiyah Tace “Hashim? Aunty wani Hashim kike magana akai?” Ta karasa maganar tana kuka, Badiyya ta rike ta ta Maida ita ta zauna Tace “Asiyah lafiyan ki kuwa?”

Asiyah kasa Bata amsa tayi sai kuka, Badiyya kallon Hashim tayi cikin Rawar murya Tace “Kasanta Ne?”

Amma Bai Bata amsa ba,tashi tayi tana d’an tab’a shi a kafad’a ya d’an zabura Tace “Hashim ya ina magana kamin shiru?”

Kad’ai Kai yayi yace “bakomai” shi duk a tunanin sa Asiyah gizo take masa, kukan da yaji ne ya sa ya Maida hankali sa gunta sa hannu yayi a fuskar sa ya goge idonsa ya Kara kallon inda Asiyah take cikin murya Mai sanyi ya Kira sunan ta “Asiyah?”

Tana Jin haka ta fashe da kukan farin ciki, da saurin ya nufi inda take ta durkusa a gaban ta yace “Asiyah kece?”

Fashe wa tayi da kuka tace “Ya Hashim” riko hannayen ta yayi ya had’a da nasa ya sumbaci hannunta, ya sumbaci hannunta yafi a  irga Kuma cikin sauri yake hakan yace “Asiyah Ina Kika shiga,wa ya Miki haka?”

Nan ta bud’e sabon babin kuka,kuka take sosai kuka Mai tab’a ran Mai sauraro.

Rungumarta yayi tsam a jikin sa, Yana d’an bubbuga bayan ta kamar wata ‘yar baby, sun dad’e a Haka Bata daina kukan ba Shima Kuma bai sake ta ba,nitsuwane ya Zo Mata a lokaci guda da ta tuna cewa tana tare da Rabin ranta, Kara shigewa tayi jikinsa tana shesshekar kuka Saida ya tabbata hankali ta ha kwanta kana ya sake ta,ya riko hannayen ta yace “Asiyah Ina sauraron ki Dan Allah ki fad’a min me ya same ki? Wa ya Miki haka?”

Cikin kuka ta kwashe dukkanin abinda ya Faru ta fad’a Masa, huci yayi, ya Fara rarrashin ta Yana Mata nasiha a yayin da a zuciyar sa yana Shirin d’aukan fansa ne.

Badiyya ta karasa inda suke Tace “Dan Allah ki fad’a min wai me ke faruwane anan? Hashim dama kasan Asiyah ne?”

Kallonta kawaii yayi baice Mata komai ba, Asiyah da farin ciki ya Riga ya mamaye ta Tace “Aunty shine Hashim da muke maganar sa d’azo”

A zabure ta mike Tace ” Hashim? Kina nufin shine masoyin naki?”

” Eh Aunty…….. Akwai matsala ne?”

Cikin rawar murya Tace ” A….A’a ba bakomai bakomai,kwai dai shine Wanda ya biya Miki kud’in surgery da za a Miki”

Murmushi tayi Tace “Allah sarki nagode sosai Ya Hashim Allah ya saka” 

Ya amsa da ” ameen” babu Wanda ya sake Cewa komai Knocking d’in kofar da akayi ne yasa Badiyya tayi saurin share hawayen dake fuskar ta Tace “Come in”

Baba Mai gadi ne a gaba,Abban Yesmin na biye dashi”

Mamakine ya rufe Badiyya cikin Rawar murya Tace “Baba….baba Kaine? Asiyah ga baba”

Asiyah cikin sauri ta cire hannunta a cikin na Hashim ta Fara lalube tana ambatan sunan sa.

Cikin sauri ya karasa inda take yace “Na’am Asiyah gani Nan” Yana maganar ya riko hannunta fashe wa tayi da kuka Tace ” Baba Ina ka shiga? Ka barni ni kad’ai?”

Kad’a Kai yayi yace  “gani  na dawo ban barki ba”

“To Amma mun dad’e muna neman ka da Aunty Badiyya Amma bamu ganka ba”

” Bani da lafiya ne Asiya Amma yanzu Alhamdulillah naji sauki sosai”

Tace ” To Allah yasa kaffarane duk suka amsa da  “ameen” 

“Baba kaje gun Aunty Rukayya kuwa?”

Huci yayi yace “Eh naje” 

“Alhamdulillah ka same ta kuwa”

“A’a ban same ta ba”

Asiyah Nan da Nan fara’ar dake fuskar ta ya gushe Murmushi Baba yayi ya d’aura da fad’in “Amma da naje ta bawa Mai gadin ta sako a Baki,a fad’in sa Tace tasan Zaki Zo neman ta”

Murmushi tayi Tace ” wani sako ta bani?”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button