MATAR UBA 21

Tace “Bara naje na d’auko”
” A’a Bari zan d’auko da kaina,ki je ki zauna tare dashi sannan Ki tabbata yaci abinci musmman fruits d’in Nan”
Ta amsa da to,Yana tafiya Yana jinjina halin Baraka sannan ya d’auki alwashin d’aukawa Asiya fansa ko ba komai sunyi zaman mutunci da Sadeeq (mahifin Asiyah) Kan ya rasu,cikin wannan tunanin ya je ya d’auko paper ya dawo ya tarar da dasu Yana cin ayaba kamar Wanda ya shekara baici abinci ba.
Tambayoyi ya shiga yi Masa akan Baraka Yana bashi amsa baba Mai gadi yace “Nan wani asibiti ne?”
Nana Tace “Doma hospital”
Baba Mai gadi ajiye lemon da ke hannun sa yayi yana kokarin tashi har ya mike yaji kafarsa ta Masa nauyi Bai San sanda ya koma da baya ba, Abban Yesmin dake kusa dashi yayi saurin taro shi Yana fad’in “Baba lafiya kuwa? Inna Kuma zaka?”
“Asiyah, Asiyah na asibitin Nan,Nan na kawo ta”
Nana da Abban Yesmin kallon juna sukayi,Abban Yesmin yace “in ko hakane Banga ta Zama ba bara naje Na duba, record yaje ya bada sunan ta nurse dake aiki a gun Tace “Asiyah Sadeeq yarinya Mai ciwon idon na ko?”
” Eh…eh ita”
” Ai ko an Kore ta sabida Basu da kud’in biyan aiki”
Dafe Kai yayi yace “Amma kin San inda take Ne yanzu?”
“A’a ban sani ba”
Ta cigaba da harkan gaban ta,komawa yayi ya fad’a musu yanda ake ciki,hanne ban da aikin kallon su ba abinda take you.
Baba Mai gadi yace “An Koreta Kuma? Amma zan so ganin Dr Badiyya maybe tasan inda take”
” Wace ce ita d’in?”
” Itace take kula da ita,likitar Ido ce”
Abban Yesmin yace ” Na gane,bara na je Na duba”
Yana zuwa office d’in ta ya samu a rufe tambayar nurse da ke kokarin wucewa ta gefen sa yayi saurin ce mata “Dan Allah baiwar Allah, Dr Badiyya bata fito bane?”
“Ta fito da safe Amma ta tashi”
” Okay Amma yaushe zata dawo?”
” Inaga sai Kuma da safe”
” Okay nagode”
“Baba Dr Badiyya bata Nan Amma gobe zata shigo”
” Toh Shikenan Allah ya Kai mu goben”
Duk suka amsa da ameen.
Sai da suka Kai har bayan sallar Isha suka koma gida sannan Nana ta Hawa hanne kunne da ta kula da shi yanda ya kamata.
Hashim tunda suka fita Basu dawo ba har sai da sukayi sallar Isha ko wanne ya koma gidan su,Yana shiga bayan yayi Sallama da hajiyar say ya shige d’akin sa,ban d’aki ya fad’a ya watsa ruwa bayan ya watsa ruwa ya zurma jallabiyarsa ta bacci ya kwanta,kwasam ya tuno tun safe Tau basuyi ways da Safiyya ba,d’auko wayar sa yayi yaga missed calls ‘din Safiyya har uku, Badiyya missed call ya Kai goma,tsaki ya jaa yace “jarababbu”
Kiran Safiyya yayi magana take kamar baza tayi ba,irin an b’ata Mata Rai din Nan,hakuri ya shiga bata had’e da kiranta ta dad’ad’an suna kana ta huce ta saki ranta,sun dad’e suna waya sun d’auki kusan mintuna talatij yace Mata bacci yake ji Nan ma da kyar ya rarrashe ta ya kashe wayar,Yana kashe wayar yayi dialing number Badiyya,har ta Fara bacci Asiya yace ta tada ita cikin sanyin murya take Kiran sunan ta had’e da tab’a ta,” Aunty,aunty” ta amsa da “na am” cikin muryar bacci da alamu taka Jin dad’in baccin nata,har wayar ta katse ya Kuma Kira a Karo na biyu, d’an Kara bugata Asiya tayi Badiyya ha don taso ba ta nufi inda tayi plugging wayar ta achaji ganin Wanda ke Kirane yasa tayi sauri picking call d’in, murya Na rawa Tace “Ass..ssalmmu alaikum”
Ya amsa da “wassalam Dr Badiyya ya kike?”
” Ta amsa da lafiya Lau ya gida”
” Lafiya lau, lafiya kuwa Naga kike ta kirana?”
Yar karamar huci tayi Tace “Gaskiya ba lafiya ba”
“Uhmn Ina sauraron ki me ya Faru?”
Maida kallon ta tayi ga Asiya sai tayi saurin shiga ban d’aki ta rufe kofar ta ciki,Jin tayi shiru yace “Hello kina jina kuwa?”
“Eh Ina Jin ka” murya kasa kasa.
“Ya Kuma kikayi shiru?”
“Am sorry bani kad’ai bace na d’an keb’e ne”
“Okay ba matsala to ya akayi?”
” Hashim haryanzu kana fushi Dani ko?”
” Look Badiyya wannan dalilin ne yasa bana d’aga Kiran ki na fad’a Miki bana so kina tinkarata da wannar maganar idan Baki da abin fad’i Ni zan kashe wayata”
” Am sorry dama taimako nake nema a gun ka”
“Taimako ta me Kennan fa?”
Murmushin takaici tayi sabida yanayin yanda yake amsa Mata maganar cikin fushi,tsawa da Kuma takama.
Tace “akwai wata yarinya asibitin mu,idon tane ya samu matsala Ana bukatar kud’i Mai yawa,kuma marainiyace aikin ma baza a iya yi Mata a kasar Nan ba sai India shine nake so Dan Allah inda Hali ko zaka taimaka mata,yau kimanin sati uku Kenan nake neman ka tun ciwon baiyi chronic ba Amma baka saurareni ba”
A zuciyar sa yace “Allah sarki” Amma a fili yace “Sorry for that yanzu kud’in ya Kai nawa ne?”
” Da dai Rabin million ne Amma yanzu zai Kai d’aya harda rabi”
” Karki damu zan taimaka Mata,a wane asibiti kike aiki?”
” Doma hospital ne”
” Okay tana asibitin ne?”
” A a yanzun muna gidan mu,sabida gudun Kar a wulakanta ta a asibin”
“Kin kyauta,yanzu abinda za’a yi mu had’u gobe da karfe goma a asibin”
” Toh insha Allah nagode sosai Allah ya saka”
” Kar ki damu,sai da safe”
Ta amsa da “Allah ya tashe mu lafiya”
Ya katse wayar,Yana Jin wani irin yanayi a kanta Wanda shi kansa Bai San mene Ne ba.
Badiyya kuwa ji take so da kaunar sa Na karuwa a cikin zuciyar ta had’e da murna Asiyah zata samu sauki,tana komawa d’akin da niyar fad’a Mata Albishir ta tarar har tayi bacci,shafa kanta tayi sannan ta gyara mata bargon da ta rufe jikin ta dashi.
WASHE GARI
Tun karfe takwas Badiyya ta shirya sannan ta shirya Asiya, Asiya Tace “Aunty Ina zamuje ne”
Murmushi tayi tayin da take Kama Mata gashin kanta da ribbon “Asiyah kin kusa samun sauki insha Allah”
“Bangen ba aunty? Baba Mai gadi ya dawo ne?”
” A’ a, Amma akwai Wanda mukayj magana dashi yayi alkawarin yau d’in Nan zai biya Miki kud’in aikin Nan”
Asiyah Baki har wuya ” Dan Allah aunty dagaske kike?”
” Eh Asiyah dagake nake”
” Alhamdulillah Allah nagode maka ,aunty nagode sosai ban San me zance Miki ba sai dai ince Allah ya biya Miki bukatun ki na Alhairi”
” Ameen ameen Asiyah,to tashi mu tafi” ta gyara mata hijab d’in jikinta tasa Mata bakar eyeglass tayi kyau matuka,kamar ba makauniya ba.
Karfe Tara chip suka Isa asibitin a office d’inta ta ajiye ta kana ta fita don duba patient d’inta masu matsala irin na asiyah, bayan ta gama ta koma office, zaman ta ke da wuya ta ga Kiran hashim, cikin sauri tayi picking Bai jira tace komai ba yace “Kina Ina? Na shigo asibitin ku?”
Tace “Ina office d’ina gani nan zuwa”
” No ki fad’a min inda kike kawaii am coming”
Nan ta Masa kwatance,ya katse wayar.
????????????????????????????????
Kuyi hakuri da rashin post d’ina bawai bana son typing din bane Ni kaina na kosa Naga na gama Amma Kun San harkar makaranta sai a hankali musamman ‘bangaren da nake karanta duk Wanda yasan pharmacy yasan karatun ba sauki
Sannan da rashin comments dinku Yana Kara kashe min jiki
Please kuyi comments sannan kuyi sharing
[ad_2]