Uncategorized

MATAR UBA 22

Iska Mai zafi ya hura kana yace ” Kiyi hakuri Asiya,motace ta buge Ni a wannar ranar Kuma wasikar na hannu na a wannan lokacin tun daga lokacin ban San inda nake ba sai shekaran jiya na farfad’o”

Murmushin gefen baki tayi Tace “Bakomai baba tunda kana da lafiya ai shi yafi muhimmanci a yanzu”

Abban Yesmin a Karo na farko ya yi magana yace “wasikar da kake magana akai d’azun Nan na d’auko shi a mota da niyar zan baka,Amma bara na Kira Matata ta kawo muga ko shi d’in ne” Yana maganar ya zaro waya ya kirata, tana picking yace  ‘dan kawo min envope “d’in Nan Mana a office d’in Dr Badiyya”

Ba ‘bata lokaci ta Karo dake bai da wani nisa, da Sallama ta shiga ta Mika masa,ganin Asiyah ta Kama Baki ta ambaci sunanta “Asiyah kece?”

Ta amsa da “eh Amma pley Wace Ce?”

Murmushin gefen baki tayi Tace “Haba Asiya har kin manta Ni?”

Dr Badiyya ce Tace “Ai ta makance Bata gani?”

“Eh na sani,baba Mai gadi ya fad’a min, na d’auka zata d’auki muryatane”

Murmushi Asiya tayi Tace ” Aunty Nana? Ko ba Maman Yesmin bace?”

Ita ma Murmushi tayi Tace “Eh nice nice”

” Hmm ai bazan tab’a manta dake ba Aunty Nana bazan tab’a manta ki da mummy ba”

Nana harkasa ta durkusa Tace “nasan bakya gani na,yanzu haka a gwiwowina na ke,Asiyah na cutar dake, na biyewa son zuciya ta,Amma wallahi yanzu na tuba ba Nanar da Kika sani bace yanzu haka na manta ranar da na sa Baraka a cikin idona Dan Allah na roke ki,ki yafe min,Kuma a shirye nake na taimaka Miki wajen ganin kin d’au fansar abinda Baraka ta Miki”

” Na yafe miki Aunty Nana har cikin zuciya ta dama chan ban kullace ki da komai ba”

” To nagode Asiya” tashi tayi ta mikawa baba Mai gadi wasikan yana gani yace “Tabbas shine wasikar ne,don ga sunan ta a jikin” Yana nunawa Abban Yesmin shi duk dad’ewar wasikar a gun sa bai San akwai sunna akai ba, mikawa Asiya wasikar yayi yace “Asiyah ga wasikar Nan”

Murmushi tayi tace “Baba da wani idon zan karanta? Kawaii ka karanta min naji”

“To bande ke da abinki Asiyah ai Ni ban iya karatu ba, sunan kin ma da nace Wanda ya bani wasikar ne yace min ga Nan sunan ki a rubuce” duk sukayi dariya sai ya ce ” To ai gaskiya ne,yanzu Ke gashi ki karanta Mana” Yana Miki wa Dr Badiyya, hannu buya tasa ta karb’a cikin girmamawa.

Karanta sakon ta Fara yi kamar haka.

 “`”Assalamu alaiki Asiya,da fatan kina lafiya, Kiyi hakuri Asiya da irin halin da Kika tsinci Kanki, ko kad’an bana Jin dad’in abinda ke faruwa daku,tun bayan mutuwar Anisa da Mahaifin ku Baraka take yin abinda ta ga dama har gidana tazo ta ci mutunci na da na Miji abin bai min dad’i ba Sam,har tayi ikrarin zata kashe ni idan na kuskura na Tako inda kuke shine dalilin da yasa na daina zuwa in da kike.

        Baraka Bata da imani Bata tsoron Allah, Asiyah ina ji Ina gani ta sawa Yar uwata Maryam (Mahaifiyar Asiyah) guba a cikin abincin ta Amma na kasa fad’awa kowa a wannan lokacin ma ta yi min barazanar zata kashe ku sannan Nima ta kashe ni idan na kuskura na fad’a wa kowa maganar Nan, wannan shine dalilin da yasa ban fad’awa kowa ba.

       A duk lokacin da sakon Nan ya iso gare ki,ga Nan number ta ki kirani Dan Allah ina Nan Ina zaman jiran kirin ki,sannan akwai Flash drive da na ajiye Miki acikin envelope d’in Video ne na lokacin da Baraka tasawa mahaifiyar ki guba sannan akwai recording na lokacin da take min bazarana” 

      Taki a kullum Rukayya

“` 

Asiyah fashewa tayi da kuka a yayin da, Badiyya tasa hannu ta Ciro flash drive d’in, Hashim ne yace “Alhamdulillah Allah ya kawo karshen azzuluamar Nan, yanzun Nan zan shigar da kararta kotu ba sai anjima ba” ya zaro wayar sa da niyar yin Kira.

Abban Yesmin yace ” Dakata Dakata bawan Allah, wannan ba abin gaggawa bane Baraka shu’uma ce Dole mu bita a hankali,ba abun mamaki bane ta kashe mu duka ko Kuma ta haukatar da mu” Maida kallon sa yayi ga Badiyya yace” Bani flash d’in Nan” ba musu ta mika Masa ya d’aura da fad’in “wannan zan Kai was aboki na babban lawyer ne Barrister Nabeel Yunusa nasan Kun San shi tunda shi ba ‘boyayye bane a garin gombe”

Hashim yace “Ni a gani na tunda an samu wannan opportunity d’in Kar muyi Wasa dashi gara a kamata kawaii a Mata hukuncin da ya dace”

Baba yace “Hashim Ina ga maganar officer na Kan hanya kasan Shima jami’i ne mubar maganar Nan a hannun sa”

Abban Yesmin yace “Hakane malam Hashim yanzu mu Maida hankali wurin ganin yarinyar Nan ta samu lafiya”

” Hakane yallab’ai goben Nan zan kaita England da kaina,yanzun ma abinda zai Hana baza mu tafi yau ba sabida Bata da passport Amma yanzun Nan zan had’a komai” Yana Kai Nan ya sa Kai ya fice.

Badiyya kanta ne ya d’aure ganin yanda Hashim ya rikice “Yana son d’aukar fansar abinda akayi mata,duk yanda akayi soyyayaar yarinyar Nan ta Kai kololuwa a zuciyar sa,bazan tab’a Bari yarinyar Nan ta kwace min masoyi ba”

Shiru tayi tana tunanin abubuwan da suka Faru shekaru biyu da suka wuce. 

 *SHIN MENE NE A TSAKANIN HASHIM DA BADIYYA?* 

Harvard University United State of America, Yana d’aya d’aga cikin manyan University a United States, anam courses da dama both art and science.

Zaune take ta a Kan stairs, jikinta sanye take da atamfa kalar curfew brown an Masa design da da milk color anyi Masa d’inkin girma, crystal stones aka zuba a gaban rigar daga sama har kasa,kanta kuwa d’aurin Aisha buhari tayi Ana iya ganin bakin gashin ta a waje, Rolling tayi da karamar gyalle milk haka ma takalmin da ke kafarfa, hannun ta rike yake da littafi da alama karatu take ganin yanda ta Maida dukkanin hankalin ta akai.

Da sallama ya Kara sa inda take ya zauna a gefen ta,a hankali ta d’ago kanta ta kalle shi Murmushi tayi Wanda ya bayyana dimple d’in dake fuskar ta,rufe littafin tayi tana kallon sa ba tare da ta ce masa komai ba yace “Angel dama anan kike tun d’azu nake ta neman ki?”

“Eh wallahi Ina d’an duba practical d’in da makayine d’azu”

” Shine akace ki manta da mijin ki? Wace irin matace haka da ba ta damu da mijin ta ba?”

Had’a hannun tayi with guda alamun bada hakuri Tace ” Tuba nake rankashidad’e”

‘daga kafad’a yayi Yana kwaikwayon muryar ta “A’a nikam ban hakura” dariya ta shiga yi sosai tana fad’in ” Na fad’a maka ka daina kwakwayona sai ka Zama kamar mace dama kamannin ka na Mata ne”

“laa Ni d’in kike cewa na Miji?”

Ya Kai hannu zai rankwashe ta,ta watsar da littafan dake hannun ta, ta gudu tashi yayi ya bi bayan ta sai guje guje suke acikin makaranta,Yan cikin makarantar inda Sabo sun Saba ganin wannan masoyan Wato Hashim da Badiyya soyyayar su ta Kai so sun Zama abin kwatance hakan yasa wasu ke Kiran su da Romeo and Juliet.

Karatun su suke sosai, soyyayar su Bata Hana su karatu ba duk da already an musu baiko, Hashim na karanta Business yayin da ita Kuma take karantar _ophthalmology_ (Likitan Ido). Shekarun su biyar Kenan suna soyayya basu samun sab’a ni idan kuwa kaga sunyi fad’a to kishin Hashim ne sila akwai wani Course mate d’in badiyya Mai suna Amma Khan, ba indiye ne Yana matukar kaunar Badiyya,Amma ganin yanda take son Hashim yasa ya hakura da ita idan kaga ya Mata magana to magana ce da ta shafi karatu, uwa uba Yana bala’in tsoron Hashim bazai tab’a manta dukan da Hashim ya Masa ba har sai da ya kwana a sume a school clinic.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button