MATAR UBA COMPLETE

MATAR UBA 35

Cikin kuka tace “Mummy why? Me muka Miki? Laifin me muka Miki a duniyar Nan laifin mu shine kawaii don mun fito a ‘ya ‘yan ki?”

Asiyah tace “Safiyya Kar ki saurare ta ki fasa”

Safiyya banda kuka Babu abinda take yi, Asiyah ta Kuma cewa “Safiyya ki tuna wahalar da Kika Sha tun muna yara har Rana Mai Kama ta yau,ki tuna cewar itace ta kashe Mana Daddy Wanda hakan yasa muka Zama marayu, Safiyya ki fasa kwaryar Nan in yaso duk mu mutu ko ba komai an rage mugun iri”

Dariya Baraka tayi Tace “ai kunyi kuskuren taho dashi nan da tun Lokacin da Kika gani Kika fasa da yanzu wata Labari ake ba wannan ba”

Nana Tace “Baraka Dan Allah ki bari a kawo karshen wannan abun ki tuba ki koma ga Allah”

A tsawace Tace “Yimin Shiru munafuka ai da had’in bakin ki ake so a ci Amana ta a munafurce ni Wallahi sai kinyi Dana sanin sani na a Rayuwa”

Asiyah ganin duk hankalin su na Kan Baraka cikin saurin ta buge hannun Safiyya, Baraka da gudu ta Karasa gun, tuntub’e tayi ta Fad’i  kasa dake gun interlock ne kwalban na tab’a kasa ya fashe, wani irin Kara ne ya fito daga cikin kwalban had’e da wani wari da iska Mai sanyi sosai, Baraka tayi iya bakin kokarin ta ta Mike ta kasa da alama ta karya kafantane, cikin sauri Safiyya ta d’auki kwaryar Shima ta makashi da kasa, wanted irin dariya ne ya fito daga cikin kwaryar Mai firgitar da Mai sauraro.

Kara Baraka ta saka Mai kara,toshe kunnuwan ta tayi tana ihu daga bisani ta yanke jiki ta Fad’i sumammiya.

????????????????????????????????

Milhat ce

Yar Terawa

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button