Mijin Matar nan da aka kulle a daki na tsawon watanni har ta mutu ya musanta zargin da akeyi masa
Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Yobe ta ce tana ci gaba da bincike kan wani mutum, wanda ake zargi da kulle matarsa a ɗaki na tsawon lokaci ba tare da kulawa ba.
Tuni dai matar, mai suna Sadiya Salihu, wadda ƴar asalin jihar Kano ce ta rasu a wani asibiti da ke Kano bayan ta sha fama da jinya.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem, ya shaida wa BBC cewar yanzu haka suna tsare da mijin matar, kuma suna shirin gurfanar da shi a gaban kotu.
A cewarsa “a yanzu da nake magana mun riga mun fara bincike.”
Sai dai ya ce mutumin da ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa a lokacin da ƴan sanda suke yi masa tambayoyi.
Ya kara da cewa rundunar ƴan sanda tana ci gaba da riƙe shi saboda irin bayanan da take da su.
Haka nan Mr Dungus ya ce rasuwar matar za ta iya sauya irin tuhume-tuhume da za a gabatar gaban kotu.
A cewarsa rahoton da likita zai bayar ne zai tantance yadda tuhumar za ta kasance.