Mustapha Naburaska Ya ýanta Fursunoni 33 Tarar Da Ake Binsu
An sako fursunonin su 33 ne daga Gidan Yarin Gwauron Dutse da ke Kano bayan Naburaska ya biya tarar da ta sa aka tsare su gidan yarin, saboda sun kasa biya bayan kotu ta same su da laifukan da aka gurfanar da su a kai.
Fursunonin da yanzu aka sako domin su yi azumi tare da iyalansu sun hada da mata biyu da maza 31.
Da yake magana a madadin sauran fursunonin da aka sako, Mado Bala, ya yaba wa Naburaska, tare da da yin alkari cewa zai kasance mutum nagari, domin ya koyi babban darasi a tsare shin da aka yi a gidan yari.
Mustapha Naburaska wanda a kwanakin bayan Gwamnan Jihar Kano ya nada a matsayin mashawarcinsa ya ce ya yi hakan ne domin ya kara kwarin gwiwa ga wadanda ke da hali wajen faranta ran masu karamin karfi, musamman ganin cewa watan azumin Ramadan ya matso AminiyaAminiya ta rawaito.
“Gaskiya ba karamin tashin hankali ba ne a ce mutum zai yi azumi a gidan yari, shi ya sa na ga dacewar a biya musu tarar da kotu ta yi musu da dan abin da zan iya,” inji shi.
Dan wasan barkwancin ya yi kira ga mawadata da kungiyoyi da kamfanonin da su rika taimakawa wajen ceto rayuwar mutanen da ke cikin mawuyacin hali a gidajen yari, saboda sun kasa biyan bashi ko tarar da kotu ta yi musu kan wasu kananan laifuka.
[ad_2]