Mutanen da suka cike fam na tallafin 30,000 da aka ce na Tinubu sun fuskanci matsala.
Mutanen da suka cike fam na tallafin 30,000 da aka ce na Tinubu sun fuskanci matsala.
Daga Barista Nuraddeen Isma’eel.
“Rahoton gaggawa, da suke bayyana yadda aka fara kwashewa dubun dubatan al’umman Nijeriya waɗanda suka cike fam ɗin cewa Ɗan Takaran Shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai bada tallafin Naira “30,000” kuɗaɗensu daga asusun bakinsu musamman masu ajiyan kuɗi a bankin “GT” da Zenith.”
“Idan baku mantaba, wata takarda ɗauke da bayanai cewa Ɗan takaran Shuagaban ƙasar zai bada tallafin “30,000” yayita yawo a yanar gizo cikin makon da ya gabata, lallai ya tabbata na ƴan damfarane suka shirya, da sunan jama’a su cike kana domin su san bayanan asusun bankin mutum su kwashe masa kuɗi.”
“A halin yanzu haka, rashin jituwa ya afku a tsakanin masu tu’ammali da waɗannan bankunan guda biyu na GT da ”Zenith” duba ga yadda aketa yin masu zari ɗai-ɗai na makudan kuɗaɗen su dake cikin asusun bankinsu kai tsaye ba shamaki.”
“Bugu da ƙari waɗanda lamarin ya shafa sun koka, bisani sun tabbatar da cewa, aƙalla miliyoyin kuɗi ne ƴan damfarar nan suka kwashe daga asusun waɗanda suka cike wannan fam musamman masu amfani da “GT” da “Zanith” bisani suke cigaba da datsan asusun Mutane musamman masu cike fam suna awon gaba da kuɗin su.”
“Sun kuma ƙara fashin baƙi da cewa harta waɗanda suka cike amma da wasu bankunan can daban bana “GT” da “Zenith” ba Lallai su ma su shirya domin ba barinsu ƴan damfarar nan za su yi ba, tunda mutum ya saka bayanan bakinsa Sai abinda ya gani.”