Hausa Novels

Lu’u Lu’u 21

*21*

 

 

 

Mai gadin dama yana d’akinshi, dan haka suka lallab’a inda Umad ya bud’e k’ofar suka fita a gidan, wani kyakyawan babur suka tarar a k’ofar, cikin salo da k’warewa Umad ya hau tare da saka hular kwano sannan ya mik’o mata ita ma, karb’a tayi ta saka kafin ta hau suka d’auki hanya.

 

A k’alla tafiyar minti talatin suka samu inda Umad kuma ya dakata a wata garage dake rufe, tana tsaye tana kallo ya bud’e k’ofar ya fito da mota k’irar benz bak’a wulik, saida ya koma ya rufe garage d’in sannan ta shiga suka kuma d’aukar hanya, awa d’aya suka share a motar nan suka isa wani k’arami kuma k’ayataccen gidan da ba zaka tab’a tsammanin wani daya tara kud’i sama da pan ko euro ko kuma dolar milyan biyar ba, dan k’arami ne sosai daidai da k’aramin ma’aikacin da buk’atar gida ba zata gaza samunsa ba.

 

Saidai a cikin gidan tsofaffi biyun ke rayuwa ko d’an aike babu, tsofaffi biyun sukan ware lokaci zuwa lokaci dan su keb’e kansu su samu lokacin farin ciki a tsakaninsu da kuma walwala ba tare da d’awainiyar al’umma ba, dan sarautar k’asar Egypt ba k’aramar sarauta ba ce kamar kowace, hatta da tsarin tafiyar da mulkin daban yake da na kowace masarauta kamar yanda tsarin shigarsu da yarensu yake daban.

 

Sau d’aya Umad ya buga k’ofar suka gane waye a k’ofa, tsohon ne ya k’araso cike da dattako da haiba ya bud’e, murmushi ne ya bayyana a fuskarshi sanda suka had’a ido da Umad, kaucewa yayi a hanyar alamar ya wuce sai ya rufe k’ofa, da fara’a Umad da kuma girmamawa yace “Barka.”

 

Kamar dai kowane sarki ko jinin sarauta shi ma da ido ya amsa mi shi tare da d’an murmushin gefen labb’a, kallon fuskarshi Umad ya sake yi yace “Ba ni kad’ai bane, na zo muku da wata kyauta ne ta musamman.”

 

Idonshi kawai ya d’aga zuwa bayan Umad d’in dan ganin menene, a hankali Umad ya rab’a gefe dan ya bashi damar ganin wacce ke bayanshi.

 

Suna had’a ido wani yanayi na musamman ya ziyarcesu a tare, sanyayye kuma k’akk’arfan fad’uwar gaba suka samu a tare, sai dai kuma wata irin alak’a mai k’arfin gaske da suka ji ta k’ullu a tsakaninsu lokaci d’aya.

 

Ayam kasa d’auke idonta tayi ta saki baki tana kallon tsohon kamar zatayi magana, sai take jin kamar fuskarshi ta mata kama da fuskar matar da take gani a mafarkinta, dan a duk sanda tayi mafarkin matar tana tashi ta kan kasa hasasho yanayin fuskarta, amma yanzu tana ganin tsohon saita ji kamar fuskar ce.

 

Daga can k’asar zuciyarta take jin wata narkakkiyar k’aunar tsohon da bata tab’a jin tana ma wani mahaluki a duniya ba, hakan yasa ta alak’anta ko ma menene a tsakaninsu to tabbas alak’ar mai k’arfi ce wacce ta isa ta sa su gauraya su zama dunk’ulallen abu.

 

A hankali ta tako ta shigo d’akin idonta akan na tsohon nan, yanda shi ma yake kallonta zai tabbatar maka abu iri d’aya suke ji a jikinsu da zuk’atansu, wasu k’walla ta gani a idon tsohon sun taru suna neman zubowa, cikin wata irin muryar kuka mai tattare da shauk’i tsohon nan ya bud’i bakinshi yace “Idan har abinda nake ji a yanzu gaskiya ne, hakan na nufin yau ni ne a gaban jikanyata? ‘yar da’ yata ta haifa?”

 

Ayam kam tuni k’walla suka zubo mata suka shiga wanke mata fuska wanda ita kanta bata san dalili ba tace “Ban san asalin me nake ji ba sanda na gan ka, amma dai ina jin daban a kan ka, waye kai ? Me ye alak’ata da gidan nan? Me yasa nake jin haka dana ganka?”

 

Wani lafiyayyan murmushi ya saki ya kamo hannayenta duka biyun zuwa ciki, bin shi ta dinga yi har saida suka shiga tsakiyar falon, dan yanayin ginin gidan sak irin zubin k’irar yan Turkey aka mi shi, tsohuwar data samu zaune a kan kujera ta kwanta baya sosai jikinta lullub’e da tattausan bargo ne ya nemi haukatata.

 

Sak fuskarta take gani a tsohuwar, abu kawai daya banbanta su shi ne ita yarinya ce ita kuma tsohuwa, ita ma mik’ewa tayi da sauri tana sake k’urawa fuskarta ido, irin dai abunda suka ji a farko haka yanzu ma suka ji, da sauri ta k’araso tana kallon mai gidan na ta tace “Habibi, kamar akwai wani abu tsakaninmu da wannan ko?”

 

Jinjina mata kai yayi sannan ya juya ya kalli Umad dake bayansu a tsaye, a hankali tsohuwar ta kai hannunta wuyan Ayam ta kama sark’ar nan tana kallo, fashewa tayi da kuka ba tare data saki sark’ar ba tace” Wannan sark’ar ba zan manta ranar da waccen azzulumin ya sakawa ‘yarmu ita a wuya ba bayan ya mana barazana da rayukanmu.”

 

Da k’arfi ta jawo Ayam suka rumgume juna tsam, Ayam da bata gama fahimtar me ke faruwa ba ita ma kukanta shiga rerawa, Umad kam wuri ya samu ya zauna k’afa d’aya kan d’aya yana kallonsu, sai tsohon ne ya rabasu ya ce su zauna, zaune tsohuwar tayi daf da Ayam ta rik’e hannunta gam kamar za’a rabasu, shi tsohon gefenta ya zauna suka sakata tsakiya.

 

Kallonsu tayi dukansu tana ziraro wasu hawaye tace” Alamu sai k’ara nuna min suke Habbee da Utais ba iyayena bane na gaskiya, sai dai kuma bana so abinda ak fad’a akan mahaifina na gaskiyar ya tabbata, da haka ya faru zan so na yi ta zama a cikin rayuwar nan mai kama da mafarki.”

 

A tare tsofaffin suka d’ora hannunsu a kan ta da niyyar shafawa, amma da suka ji a tare suka d’ora sai tsohon ya janye na shi ya bar na tsohuwar, cike da kulawa da k’auna tace” Ayam hak’uri zakiyi, haka shi ne jarabawarki kin ji.”

 

Kallonta tayi tace” Ku su waye?”

 

Ajiyar zuciya tsohuwar ta sauke ta nuna kan ta tace” Ni sunana *Bilkis* sarauniyar Egypt, wannan kuma *Abdallah* sarkin k’asar Egypt, mu iyaye ne ga mahaifiyarki wacce tayi nak’udarki wato Juman, gimbiyar Egypt sarauniya kuma a Khazira.”

 

Juyawa tayi ta kalli tsohon ta rik’o hannunshi tana kuka tace” Da gaske ku d’in ku kuka haifi mahaifiyata? Da gaske ne sarauniyar Khazira ta haifeni kuma ta bayar dani ga jakdiyarta?”

 

Jinjina kai yayi yace” Tabbas gaskiya ne, duk da bamu had’u da mahaifiyarki mukayi magana baki da baki ba, amma dai abinda aka fad’a miki gaskiya, mahaifiyarki tayi hakane dan kub’utar da ke.”

 

Cikin matsancin kuka tace” To amma ce wa suke harda mahaifina ma cikin masu son kasheni, taya haka zai yiwu?”

 

Sarauniya Bilkis ce tace” Zai yiwu, musamman ga mutum irin Musail mai son kansa da zuciyarsa, babu abinda ba zai iya aikatawa ba dan ganin mulkinsa ya ci gaba da wanzuwa a doron k’asa.”

 

Kallon tsohuwar tayi tace” Kenan gaskiya ne yana son kasheni? Idan har shi ya haifeni da cikinsae yasa zai nemi kasheni?”

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button