NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaune take kan kujera ta duqunqune ta tura kanta cikin cinyarta tana sana ar tata a hankali Amira ta dafa kafadarta ta zauna gefenta
Cikin sanyin murya tace Ayyah Aysha ki tausayawa kanki ki tausayawa umminki mana baki ga duk damuwarki ta kama zuciyarta ba ta danyi shiru ganin Ummin a gefensu cikin damuwa hannuta dauke da cup en nono ta zauna gefenta cikin rarrashi tace Aysha karbi ko da nononne ki Sha kinji ko
Kanta ta dago ta zuba musu jajayen idanunta cikin takaicin rayuwa tace Ummi ni banjin yunwa Na qoshi
Haba Aysha yaufa kwana 5. Bakici abinciba so kike kijawa kanki cuta ne
Kanta ta manna jikin Ummi ta fashe da kuka cikin kukan tace Ummi wai da gskne mgnar aurena da Hamma yusuf Ummi kuma da gaske bani ba ya Ahmad
Ta dan zuba mata ido tace Ummi Amman bakya sona ko girgiza mata kai tayi cikin sanyi tace Aysha ina kika taba ganin uwa taqi yarta nima wannan abin ba a son raina za ayishiba Amman bari in gaya miki gskyan Al,amarin ……………???????????? duk ta zuba mata ido dakunne danjin meye gskyar abin

By garkuwan Fulani 76
[4/9, 2:24 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????
MI,WASMITI…page 1⃣2⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????
Cikin lallashi taci gaba da cewa Aysha nima kaina wannan abin yafi qarfi nane shiyasa banda iko ko damar hanawa shiyasa wlh da ina da iko da Na hana ko dan farin cikin Ahmad inajin quna a raina sabida halin da Ahmad ya kasance a ciki ina jin tausayin mahaifiyarshi da Abbanku dan duk duniya sune Na forkon shiga matsala in damuwa ta dameshi
Ta daura hannuta a kanta tana shafa gashin ta cikin taushin lfzi tace Aysha kiyi hqri da gddarar ubangiji ki daure kiyiwa iyayenki biyeyya kibi umurninsu
Kuka sosai ta saki cikin jin zafi tace Ummi shikenan ni kam bani da wani sauran farin ciki ko ?
Kina dashi Aysha am me zai hanaki ai rayuwa juyawa take wata ran sai lbr rayuwa zata kawo miki farin ciki zuciyarki ta Koma tamkar bata taba riskar takaiciba
Haka dai taita bata baki Amman duk da hakan taqi cin abinci sai kuka da ta sake suna zaune a haka har bacci yaci qarfinta tai baccin
Gudun kar a tadda ita taci gaba daga Inda ta tsaya dole Amira ta dawo parlon suka kwana tare
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Yau
10 days kekan da jin wannan sabon salon rayuwar da suke ciki damuwa da kuka su suka zama abincin Aysha yayinda Ahmad da yusuf sukayi wuyar ganuwa
Adam dai yakan dan chigo kadan kadan

Misalin qarfe 9 Na dare Abba da ummi ke zaune a parlon Abban suna dan tattauna wa cikin damuwa Abba
Ya dan kalli Ummi yana mai cewa Ahmad fa kwana 3 kenan ni ban ganshiba kuma yawanci a kwanakin zai kirani da safe muna gaisawa zai katse kiran kuma ko Na sake kiranshi sam layukan nashi basa shiga abinfa Na damuna sosai ya qarisa mgnar cikin damuwa
Ummi ta danyi ajiyar zuciya cikin sanyi tace wlh ni kam ma yau kwana goma kenan
Ban ganshi da idona ba sai dai kullum zai kirani mu gaisa kam
Haka kuma shima yusuf bai shiga kuma dukkansu ko abinci yadda aka kai musu haka za,a dauko
Kanshi ya jinjina gami da zaro wayarsa number Usman ya kira yana dagawa ko gaisuwarsa bai amsaba yace (hey Usman ya ‘youni nam ya Ahmad Mon) kai Usman je ka kiramin ya Ahmad enku
Toh ya amsa da sauri gamida katse kiran
Ya kalli Nenne da suke parlonta suna ta dan hira yace Nenne ya Ahmad fa ?
Abba ke nemansa kai ta dan kada tace wata qil yana dakinshi
A dakin ya sameshi kan sallahya yana kwance yayi rigigine hannushi ruggume da Al,QURA,ANI mai girma Amman kuma idonsa a lumshe yana ta rera karatun cikin narkekkiyar sauti baki 2 yana mai mgn bai jiba saida ya qarisa gun ya zare AL,QURA,ANIN
Da sauri ya bude idonsa
Shima din shi ya zubawa ido cikin yanayin tuhuma dan ganin yadda ya koma tam kar ma jinyaci yace ya Ahmad (dume hebima) meya sameka
Kai ya dan gyada mai cikin qarfin hali ya dan murmusa yace kai ba komai lfy ta lau ya fada a lkcin da ya miqe tsaye
Ba dan ya yardaba yace toh masha Allah tunda lfy kaje Abba Na kiranka
Da sauri ya kallishi yace yana ina
Yana parlonshi ya bashi amsa lkcin da ya juya ya fita
⭐⭐⭐⭐
A hankali cikin nitsuwa yayi slm Abba ya amsa mai
Shigo ya cemai
Ya shigo cikin girmamawa ya zauna inda Abba ya nuna mai kusa dashi a kan carpet yayinda Abban kuma ke kan kujera
Cikin mmk suka zuba mai ido
Ummi ce ta fara mgn cikin kaduwa tace Ahmad baka da lfy ne ?
a,a.
Ya bata amsa a taqaice
Cikin damu tace doctor kallifa yadda yaronnan ya zama cikin dimuwar Abba ya xuba mai ido ya dafa kanshi
Yace Ahmad meyasa baka cin abinci gafa yadda yunwa da damuwa da tunani suka galabaitar da kai
Ya dago kanshi ya kalli shi cikin qarfin hali da murmushi a fuskarsa yace Abba inafa cin abinci
Kanshi ya dan kawar ya kalli Ummi yace Fatima kawo min abincina
Toh tace ta juya da sauri ta nupi kan dining dan dauko abincin
Kanshi a gefe ya kirashi cikin taushi yace Ahmad tsoronmu kakeji ko? shiyasa kke buya kar mu sake zaluntarka
Da sauri ya daura kanshi kan cinyar Abban ya dafeshi da hannu Bibibbiyu yace cikin rawar murya
A,a. Abbana baku zalunceni ba bare naji tsoron kar Ku kuma
Mun zalunce ka mana Ahmad am banda yadda zanyine shiyasa Ahmad qaddara ta rigayi fata ka gafarcemu hqqa mun zama masu tauye haqqi a gareka dana
Ummi ya kalla a lkcinda ta dire tiren abincin a gabansu gamida dan sunkuyar da kanshi yace ummi ki tunawa Abbana matsayinsu a guna mana in yana fadar haka zafi nakeji sai inga kamar ganisuke basu isa daniba
Ummi kam sai hawaye cikin muyar kuka tace ga abincin ta dan zuba mishi ta miqa mai Abbane ya karbi pilet en ya zame qasa kusa dashi
Tuqeqqen tuwon shinkafane da miyar taushe sai qamshin man shanu yake
Sa hannu kaci kaji ko Ahmad ba musu ya danci abincin badon yanajin dadinshi ba
Sai dan ya faran tawa Qanin mahaifinshi
Bayan ya dan mishi nasiha da qarfafa mai guiwa da sanya mai albarka
Sukayi sai da safe har bakin part ensu Abban ya rakashi

A bin mmk a palonsu ya samu ……….

By garkuwan Fulani
[4/9, 2:24 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????
MI,WASMITI…page 1⃣3⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????
Yusuf Ne zaune yana riqe da cup din black tea yana dan Sha gefenshi yaje ya zauna cikin yanayin happy ya dan murmusa ya kalleshi yana kai biyaye yaufa kusan kwana 5 ban gankaba
Klonshi yayi cikin harara ya miqa mai cup en yana gashi karbi kasha karba yayi ba musu yana Sha ya dan tsaya zaiyi mgn da sauri ya dan daga mai hannu yace gama shan tukun sai kayi farfa gandan naka kar kayi ka qware
Ajiye cup din yayi ya kalleshi da kyau yace biyaye farfaganda kuma ni din
Yes ya bashi amsa kai din dai ba waniba ya dan girgiza kanshi da dan gyada kan cikin yanayin muryar da tafi kama da zaka qwaremu yace
Biyaye bazan iya fushi da kaiba bazan iya rayuwa cikin happy bayan kai taka rayuwar ta cabe ba
Hannushi ya dan daura kan qirjinshi yace kana son soya zuqa tanmu da biyeyyarka mara amfani a wannan karon cikin jin takaici yace nifa banda matsala dan banma ji zancen tsohonan ba bare Na wani yarda da tsarinsa Na gaibu ni kwannan zan barmusu qasar
Amman damuwata nasan zasu yimaka daurin kazar kuku
Dry ya danyi yace tab guduwa zakayi kenan ? ehh ya bashi amsa tunda ban da mafita iyayena sun Sa baki kan zancen zauceccen tsohonga ai dole Na bar qasan
Zan fadawa Abba murmushin takaici yayi yace Na tabbata bazaka iyaba shiyasa Na fadama
Haka suka danyi ta tattaunawa har zuwa qarfe 11 sukayi shirin kwanciya
Dama shi yusuf tunda suka dawa da yake bai son kayan takaici injishi da fada sai yakan wuni gidan kaka Zubaida sarkin surutu sui fada su shirya
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Yau kusan 2 weeks kenan da dawowarsu mambila amman har yau Aysha batasa ya Ahmad dinta a qwoyar idantaba
Duk da fama da take da azabebben ciwon girji Sam bata iya cin abici sosai qirjinta ke suqa kuma dai dai kan dukiyar fulaninta har taji tamkar zasu tsage

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button