NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali ta murda qofar dakin ta shiga can ta hangoshi kwance kan gadonshi yayi ruf da ciki matsowa tayi ciken sanda tasa hannuta ta zare picture enta daya kifu a kai idansa ya rumtse gamida cije lips enshi cikin Dan dakewar murya tace bude idonka budesu ka kalleni ka gayamin meye a zuciyarka shin xaka gskanta zancenka Na baya ko zaka qaryata kanka da kanka
Kai ya rinqa juyawa cikin disashewar murya yake ta maimaita a,a
Hannu tasa ta dafa kafa dunshi tace ya Ahmad wlh kashemu kake son yi kallifa yadda ka dawo da rayuwarmu
A hankali yace Aysha nine da laifi meyasa kike qara azabtar da zuciyata?
Ehh kaine da laifi Ashe dama yaudara gsky ce maza nayi sannan kai sai ka rasa wacce zaka yaudara saini qanwarka kasan dama ba aurena zakayiba meyasa ka cutar da zuciyata????
Ya Ahmad ka cucemu ta fada cikin kuka kan qirjinshi ta fada tana kuka ????
Sosai tana Dan bugaga girjinshi tana dama baka sona ashe zancenka qaryane dakace Aysha ce bugun zuciyarka ????
A hankali zaciyarsa keta cushewa zancenta ke ratsashi idanshi ya fara budewa bakinshi ya fara motsawa zafi da yakeji ya fara bunqasa cikin rauni ya kamo hannuta ya daura kan qirjinshi
Yace kinjin har Abadan bazan miki qaryaba haqiqa ke Aysha kece buguzucita???? Na gayamiki duk numfashin da zan zuqa da sonki nake zuqarsa wlh ina mai sheidamiki rayuwar Ahmad sauran kadan tunda aka tirsasawa zuyata fidda qaunarki Ayshaaa ki sani wlh duk randa Na gama cireki a raina toh tabbas a ranar zan barduniya????
Cikin sanantar kukan tace OK zaka ciren a ranka kenan ?
Eh Aysha ya zama dole naiwa iyayenmu biyeyyah da qarfi ya danna hannuta kan qahon zuciyarsa yace kiji har abada zan mutu da qaunarki hannushi 2 ya hada yace plxx Aysha( burtinam ha sudu am usenifu ta loru waru ha am)
Fitamin a dakina ina riqonki karki qara zuwa guna
Klonchi tai sosai cikin zubda qollah tace fitar numfashinka shi zai yanke nawa numfashin yayinda muka mutun zuciyar Dan uwanka dakafiso zata buga Dan rashinka ta sake kallonci tai murmushin takaici tace Allah sarki duniya su Abba zasuga tarin qawarwaki wataqil rashinka yasa Abba na barin duniya ayyah baba bello zai qunci takaici da dacin rayuwa
A hankali ta matsoshi tace yau zanyi ban kwana da kai kiss taimai kan kumatunshi yayinda shi kuma ya lumshe ido a hankali ya manna kanta kan qirjinshi can kuma ya Dan daqota ya manna mata kiss a goshinta ta kalleshi cikin yin murmushi takaici ta sake shi tafi tana suyar zuciya

By Garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????
MI,WASMITI…page 1⃣6⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????


Haka dai rayuwa taci gaba da juyawa cikin quncin rayuwa
Yau jumma,a
Bayan an sauqo daga sallan jummaa
Duk sukayi gida
Cike suke a parlon
Sai Yusuf da Ahmad da basa gun
Baba bello ne ya dan kalli Usma dasu Rabi,u ya danyi gyaran murya yace kai Abdul tashi kuje parlona ku fitomin da kayayyakin dake ciki
To suka amsa gami da miqewa sukayi part inshi din
Aysha ya kalla a dan fizge gamida dan yafi tota da hannu a hankali ta dan saki hannun ya Abbakar ta miqe taje gabanshi ta dan duqa
Wani dan leda mai sheqin gaske ya miqa mata yana gashi ki kaiwa Yusuf kuma kice ina kiranshi dum zuciyarta ta Nada wani sauti
????????????ido ta zaro cikin firgici tace baba ni kuma ?
Eh ya bata amsa gami da gyada mata kai
Cikin firgici da razana da bugun zuciyarta da ya tsananta ???? da gyar ta miqe dakin Ummi ta nufa riqe da laidar
Kaka da tazo bikonsu su duk sun daina zuwa gunta
Ta kalleta cikin wasa tace ke figi ruga yau ba mgn ne
Baki ta dan zunbura ta zauna gefen
Umminta tana rau rau da idanta tace ayyah Ummi dan Allah ki ajiye wannan in Hamma Yusuf yazo ki bashi wai inji baba
Kai ta dan girgiza mata
A a ni ban isaba ko ni ya aika dole nakai aiken ba wani nawa den ke kiwani ce sai ni zan bayar
Kaka tayi caraf ta karbe da cewa ai wannan ma rashin kunya ce
Kallonta tayi a lkcin da tamiqe tasa bayan hannunta tana goge qollah tana wlh Na Sani sai ya zageni kun sanshi sarai mugune ???? banje inda yake bama Yaya ke kaka badai burinki ke da dan uwanki ku naqasamin rayuwa ba kusani kunci da takaici
Da sauri Ummi ta dan yimata don qolo
Kaka tai dry tace
Barta Fatima ai randa zatayi alfahari da hadinmu nanan tafe
Ita dai fita tayi tana dan qunquni

Zaune yake a dakinshi a qasa kan carpet jikinshi sanye da 3 qtr sai dan riga mai hade da hula ya Daga dukkan alamu woya yake
Ita kuma a tsakiyar parlon ta dan tsaya tana tunanin ya zatayi tayi slm shiru toh ko bayananne ta tabbayi kanta sabida tayi SLM yafi a qirga shirun da taji yasa
Ta danyi tinanin shiga dakinshi ta ajiye mai kawai
Cikin nitsuwa kanta a sunkuye tayi cikin dakin ba tare da tunanin ko yana cikiba sai xuciyarta dake bugawa
Bugun zuciyar ya tsananta a lkcin da ta shiga dakin kanta a qasa tana nufin ajiye mai kan gadonshi sai ji tayi tayi tuntube da qafarsa aiko tai taga taga ta fada kan kirjinshi
Da sauri cikin mmk da jin ta kaici ya hanka data duk da bai gama gano wayeba sabida duhun dake dakin
Itako tuni hancinta ya sheida mata shine qamshin turarensa yasa ta ganoshi shiyasa cikin sauri ta miqe gami da miqa mai aiken jikinta har bari yake cikin tsoro da rawar murya ta miqa mai ledar tace (da Hamma baba on vi mi waddine ) gashi Yaya baba ne yace in kawo ma
Fuska a murtuqe ya zaro ido ya buga mata tsawa yana ( salu vurti nam hado ) wuce ki ficemin daga nan
Tsoron sawar da masifarsa yasa ta dan saki laidar
Wasu yan takardu masu kyan gani suka watse a gun har kan qafarsa
Iskar pankar dake kadawa ya rinqa watsa su
Mmk sosai ya bayyana a fuskarsu su dukka cikin al ajabi da dimuwa yasa hannu ya dauko daya yana dubawa da fargaba sosai cikin minti 2 kamanninsa suka qara sauyawa bugun zuciyarsa ya tsananta numfashinsa ya fara dabur cewa idansa ya sauya daga yan qanana farare suka koma manya jajaye hatta jijiyoyin kanshi dana hannushi suka taso sama da wani irin yanayi ya tako ya nufi inda take
Cikin tsoron da take ta Sa hannu ta toshe bakinta da hancinta???? da nufin hana kukanta fita sai hawayen daketa kwaranya a hakali ta rinqa takawa tana baya baya shi kuma yana binta har suka pito parlon
Ganin zatayi waje yayi saurin fizgota har saida ta fada jikinsa

By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????
Mi,WASMITI..page 1⃣7⃣to2⃣0⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????
Cikin takaici ya rinqa sakar mata maruka
Zuwa yanxu tsoro ko gudun dukan ya fita a ranta firgicin ganin i,v din Auren sun da suka gani yafi komai bada tsoro a gareta jikinta da zuciyarta duk sun qageshe
Zafi sosai Yusuf keji a ransa ya gama makancewa da bacin rai shiyasa baiji bai gani yaketa bugarta kallonta yake ido cikin ido a fili yake cewa badai ke kince taurin kaiba ba tsayuwa kikayi kina tsuramin shegun idanunki ???? kamar Na matsafaba toh wlh kanki zakici mayya fitinenniya ya kuma hambararta tai baya 2 ta fadi bakin qofa a dai 2 lkcin Ahmad da Adam suka shigo parlon
Da sauri Ahmad ya sunkuyo ya dagota yayinda Adam ya nufi gun Yusuf din yana fadin
Haba biyaye me hakan anya kana cikin hankalinka kuwa ko dai ka fara shaye 2 ne
A harzuqe yayi kan Adam yana zazzaro ido woje yana eh giya nasha Adam ko kana da maganin buguwarnan tawane cikin mmk Adam yake klonsa kamar dai a bigen yake kam da sauri ya dakatar dashi hannushi ya jawo ya ajiyeshi kan kujera Goran Faro mai sanyi ya ballo ya miqamai karban Goran yayi ya cillata kan Aysha da sauri Ahmad yasa hannushi zai tare Goran cikin qeqashewar zuciya ta ture hannun ta kalleshi ido a bushe cikin yana yin dacin rayuwa tace barshi barshi ya Ahmad wlh ni a yanxu nafi buqatar azabar Hamma Yusuf ina dai sau daya ake mutuwa toh kubarshi ya kasheni ko duk ma huta wlh nafi buqatar zalumcin Hamma Yusuf din Don gwara nashi ai Ku naku boyeyyen zalumci kukemin wanda zai iya fasa zuciyata ta qareshi mgnar tana mai zubda qollah????
Cikin sanyin jiki Ahmad ya kamota ya rugumota ya mannata a girjinshi yana Dan shafa kanta yana bubbuga bayan ta
A hankali ta rinqa sheshsheqan kuka mai tsuma rai
Yusuf da yake ta numfashi kamar zaki Dan zabar bala,i da zuciya cikin daga murya yace wlh kar nazo Na sameki a nan Dan wlh sai na lahira ya fiki jikin dadi
Da jin haka Ahmad ya jata sukayi cikin gida

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button