NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Adam ne ya rinqa yiwa Yusuf din nasiha kan ya tausasa zuciyarsa
Haba biyaye shin a duniyarnan akwai mai wuce qaddararsane ?shin muke tsarawa kanmu rayuwa ne ko mahaliccinmu? haba Yusuf rayuwafa komai asannu mutum zai bishi matuqar kana son cin ribar rayuwar…..
Cikin sauqe ajiyar zuciya ya kalli Adam din cikin rawar murya da hardewar harshe yace Adam ya zanyi ya zanyi da burin Dan uwanmu Ahmad nafi jin makomar rayuwar Ahmad ya kamo hannushi yaci gaba da cewa shin kai baka tunanin yadda Ahmad ke son yarinyar nanne biyaye haqiqa kakanmu ya kasance mai zalumci a kan jikanshi Ahmad da yafi mu dukamu haquri da biyeyya a garesu cikin rawar murya yace Adam wlh so suke su kashe rayuwarmu da bakinciki Adam ya zanyi Plx biyaye ka tayani samawa Dan uwanmu Ahmad farin cikin Sa
Sosai jikin Adam yayi sanyi ya kalleshi cikin sanyi yace insha Allahu yau dinnan zamu samu mafita Yusuf zamuyi tunani daga yanxu xuwa dare gobe da safe sai mu isar da manufarmu a haka ya samu ya Dan lafar da fushin
A cikin gida kuwa Ahmad ne a gaban Nenne bayan ya samu Aysha ta lafa da kukan ya barta tare da Abubakar yana ci gaba da tausarta
zaune yake a gaban nenneshi ya daura kanshi kan cinyarta sai fidda wani nannauyan numfashi yakeyi cikin zuciyarsa sai tafasa takeyi da ka ganshi kaga tashin hankali
Allah sarki uwa da dan ta sai rabbi tuni Nenne ta gano yanayin da gudan jinin nata ke ciki a hankali tasa hannuta cikin sumar kanshi mai tashi da sheqi ta rinqa shafa kan nashi tana Dan shafa kumatunsa da daya hannun nata dai 2 kain kuncinshi taji damshi alamun hawaye???? da sauri ta dago kanshi ta zuba mai ido shima itan yake kallo ya Sa hannayenshi 2 y daurasu kan nata da ta tallabe mai fuska ????cikin zubda hawaye da muryar kuka bakinshi har yana rawa kamar maijin sanyi
Yace Nenne Na kingako nikuma kinga yadda rayuwa ta juyamin ya zanyi Nenne inason Aysha kuma Bappa Yaya ya hanani ita Nenne ke kadai zan gayawa naji sanyi ya kuma kamo hannuta yaci gaba da cewa wlh inasonta tana sona kuma an rabamu Nenne duk duniya bayanke da Abba ba Wanda nakeji kamarta
Itama hawayen takeyi cikin salon ni nacuceka ya kai Dana tace Ahmad ba laifinka bane ba laifin kowa bane laifi nane Nina kawo wannan irikitaccan al,amari Amman ka gafarceni D’ana da Sauri ya katseta da cewa ni baki min komai ba ni zan nemi gafararku
a haka baba bello ya shigo ya samesu suka hadu sukayi ta bashi baki da samai albarka

Da slm marsa da shigansa duk kusan a tare yayisu kuma duk batajiba har saida ya zauna gefenta daga dukkan alamu yanxu ta Idar da sallah
A Dan firgice tace kai me hakan wlh dudabe sai nakai qararka gun Aliyu Dan ka isheni ji yadda ka shigomin a fijajam bako slm cikin harzuqa yace ancemiki ni alulkitab ne da zanshiga wuri ba slm toh ai nidai banjiba
Hmm toh nidai nayi slm
bakadai yi da qarfiba kam
toh ni maroqine da Zan kama ihu a gari
oho dai tace masa ai tunda kin ga nine shikenan ga baki ga tsoro harara ta cillamai shi kuma yaci gaba da cemata dama baki ya Dan tabe ya kalleta a cukushe yace ke ni dama zuwa nayi ki…da sauri ta katseshi in baka lbrin ko toh nima bansan komai ba kan batun aurenku da akeson hadawa
Cikin qulewa yace keda Allah fadi ba,tambayaba ai duk surutn siya kin iya Amman da yake kinga INA roqonki shine kiketa wani jirgani toh ni bashixan tabbayeki ba zuwa nayi ki rakani mambila yanxu kafin manqqariba mun dawo baba bellone ya Aiken
aiko dajin haka ta miqe tana yauwa Dama inason zuwa toh mutafi Hajia a yawe
Oho dai sainaje Dan baqin ciki murmushin mugunta yayi aranshi yake cewa kedai komai fada

A hanya kaka sai bala,I take dan ganin hanyar Yola suka kama fada take ase Dama baka da mutunci INA zaka kaini ?
Sama zan kaiki ya bata amsa
fuskarsa Na kan titi yanata tsula gudu mita kam da masifa ya shashi Amman dayake mishkiline kafi mahaukashi ban haushi ko a jikinsa 5:00 pm suna cikin porlon baba Umar

By Garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????
MI,WASMITI…page2⃣1⃣to2⃣5⃣……Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????
Bayan yan gaishe gaishe da sukayi sai suka Dan tsagaita
Kakace tace kai Dudabe ka bada aike Dan dere yanayi.
toh yace mata gami da Dan kallon baba Umar cikin yanayinshi Na rashin surutu ya Dan sunkiyar da kai gami da Dan sake dagowa ya kalleshi ido cikin ido yace
Baba dama zuwa nayi kamin taimako ka Duba Al,amarinmu ni da yan uwana sai kuma ya danyi shiru Dr Umar ya Dan jinjina kai yace fada min ba komai gayamin menene matsalar
Ya Dan kalleshi gami da cewa baba Dama ni batun Auren nan ne sai kuma ya kurawa kaka ido Dan jin wani uban salati da ta dago haydar ma idon ya zuba mata ta kalleshi a yatsine tace wlh Allah ko Yusufa (a wasmitan ) zakafa yi nadama ka kama bakinka Dan gaba wlh kana dab da jin kunya zakayi nadama gabafa wlh ka iye bakinka…..
Ke da Allah wayasa bakinki cikin zancen nan me hadinki dani bafa cewa nayi kirekoni kimin gatsali a zancena ba kuma wlh ki kama bakinki ni da wadanda suka isadani nake mgn badake karere ba ya qarisa mgnar yana mai watsa mata harara da zazzaro idansa woje Dr Umar yadan murmusa Dan Sani dama haka zata iya faruwa shi mmk mayayi sosai dayaga wai Yusuf ne da kaka a mota daya kuma tafiya mai nisa gashi ba Dan rabiyar fada a tsakaninsu
Yusuf ne ya katsemai tunanin nashi yana mai fadin baba
Wlh tallahi kaji nayi rantsuwar musulmi
ko baba bana son Aysha wlh Na tsaneta ko ganin ta bana son yi Sam banjinta a raina baba wlh Auren da kukeson hadawa wlh masiface baba ni wlh Na yarda ko mahakaciya Ku samo Ku hadani da ita matuqar zan tsira ban Aure Aysha ba
Kaka kam baki ta sake tana ware ido tana fadin wataran zakaji kunya wlh sai kunya ta hanaka ganin abinda ke gaban ka ni kam baza,ayi tijarar nan daniba barima ka gani woje zanyi
Hydar da shima Sam bai farinciki da Auren da suke son hadawan ya harareta yace kifi ruwa tafiya ya koma ya kalli mahaifin nashi yace gsky baba niba banason wannan hadin naku nafison ya Ahmad ne ya auri Aysha
Goggo Aysha dake gefe najin muhawararsu ta bisu da ido tana mai cewa Yusuf ai banan ya kamaceka kazo ka furta qiyeyyar da kake yiwa Aysha ba gun Umminka zakaje ka fada
ido ya Dan zaro yace wlh tace duk randa Na kuma furta mata wani zance akai zata tsinemin cikin kaduwa Dr Umar yace
Subahanallahi
Meyayi zafi haka insha Allahu bazata tsinema ba
Cikin yanayin lallashi ya dafa kafadarsa yace
Yusuf kayi haquri
Qaddara ta rigayi
Fata
Bani da wani zabi bayan Na Bappa Yaya
Yusuf nima cikin qarqashin ikonsa nake
Kayi haquri ka ruggumi qaddara
Kayi biyeyya ga iyayenka zakaga sakayya mai kyau
Wlh bani da ikon watsa Auren ka da Aysha da ina da iko da tuni Na watsashi
Ya kuma dafa kafadanshi yace abinda baka saniba Yusuf ya rigada an Dade da daura aurenku kai da Aysha
Tun Aysha nada shekara 8 aka daura aurenku
Cikin firgici da mmk tsosai haydar kam dake zaune kan hannu kujera bai san lkcin da ya zameba Yusuf kuwa baki ya bude kawai yana binshi da kallo a rensa yake cewa wadannanfa sun Dade da kamu da cutar haukannan bamu kula da wuriba
muryar hydar ce
Ta kuma bashi wani sabon tsoro
Hamma Yusuf toh ai Abu yazo da sauqi yoh ba sai ka saketa ba kawai
Cikin kaduwa ya kalli hydar cikin murmushin takaici yace yoh in banda abinka
Hydar ai Auren da ya halatta ayishi shi ake iya sakarsa toh kai ka yadda Auren ya daurune?
Kai ya jinji yace haka nefa Hamma Yusuf
Dr Umar ne ya kallesu cikin Solon yaro mankaza
Ya kalli hydar yace haba Aliyu ase kaima kna da baqin tinani wannan wacce iriyar shawara kabaiwa Dan uwanka Ali ban sanka da haka ba ya kuma maida dubansa kan Yusuf yace wlh Yusuf ina jiyemaka tsoro fushin iyayenka kaji tsoron Allah kayiwa iyayenka biyeyya shin kai bazaka yi koyi da Ahmad ba ka ganifa shi aka gwara Amman ba Wanda zaice ga qorafin ko furuci mara dadi dayayi kayi koyi da Dan uwanka
Haka dai yaita musu nasiha

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button