NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yoh raini kuma Na nawa tunda ta ga gadon baccinsa ta kuma yiwa mararsa kallon tsaf ai raini ya qare anan cewar lamido
Kenan
Adam yace bar Dan iska shima zai worene wannan wuri in kasan dadin da ya qunsa ai bakayi taurin kaiba dry sosai lamido yayi
Shi kuma cikin ta kaici yace wallah tallahi kunji Na muku rantsuwar musulmi ko toh wlh ni kam har a bad a bani ba Aysha kam kodako mata sun qare a duniya koda zan rasa rai nane
Adam ya kalleshi cikin mmk yace ni kuma Na tabbatar kana tare da wahala wotarana
Dai2 lkcin suka zazzauna kan kujera cikin jin kunya Amira ta kawo musu dirings masu sanyi ta gaidasu ganin yadda hamma Yusuf din ya murtuqe fuska yasa ta wuce kitchen dinta taci gaba da aikinta
Basu dade ba Yusuf ya miqe yace su tafi gidan Ahmad

A baking gate sukayi qaro dashi yana kokarin shiga mota cikin tsoro da firgici da tsananin kaduwa suka isa gun shi
da sauri Yusuf ya kamo hannushi…….

FAHIMTARWA
Da yawa suna min qorafin basa fahimtar me sunan littafinnan yake nufi sabida ganin sunan da yaren fullancine ana yawan cemin menene ma,anar MI,WASMITI toh
Manar mi wasmiti dai yana nufin
NAYI NADAMA
Fatan masu karatu kun gane sunan novel din nayi Nadama
Kuma insha Allahu zanci gaba da hada sunan da hausan
Ina godiya da kulawarku

KINA RAINA UMMI Garkuwa marubuciyar Jennifer fatan alkhairi a gareni

Gaisuwa ga dukkan marubutanmu inai mana fatan alkhairi

By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????????

NAYI NADANA
MI,WASMITI page 4⃣1⃣to4⃣3⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????????
Hannunsa Ya riqe cikin mmk da kdma da tsabar firgici cikin kaduwa yace
Biyaye meke damunka ?
Baka da lfy ko?
Shiyasa yau kwana 2 bakaje gidaba ko ?

Shiru dai baiyi mgn ba
Cikin damuwa yace
Haba Ahmad ya ina mgn kayi shiru
Ji yadda gaba daya ka rame
Ase dama shiyasa kake yawan Sa manyan kaya
Dan ka boye yadda ka sauyane ?

Cikin yanayin shi Na sanyin hali da kawaici da haquri yayi murmushi Garfin hali da qoqarin boye halin da yake ciki
Yace
Ni wlh matsala ta da kai kenan saurin
rudewa jifa yadda ka wani gigice kana ta jeromin
Tabbayoyi
Toh wacce tabbaya daya nasan
Zan amsa maka
Adam ne yace ka gaya mana gsky ya fada cikin son gane me Ahmad din ke son boyewa musu
Dry yayi cikin qarfin hali yace
Bani da wata matsala ni kam

Cikin kura masa ido Yusuf yace ka tabbata?
Yes bani da matsala ya fada yana kamo hannun lamido
Yace on top mu isa kunzo kun tsaidashi a woje
Yusuf ne ya kirashe biyaye
Na,am ya amsa masa
Yace juyo ka kalleni
Cikin dryar tausayawa Kansu da Kansu yace anqi juyo wan
Da sauri Yusuf ya Sha gaban shi yace nace ka kalli qoyar idana ka cemin baka da matsala
Cikin sauri yayi gasa da kanshi
Dan yasan muddin ya bar idon Yusuf cikin nasa toh zai gano halin da yake ciki
Dan su tun suna yara sukan laqanci halin da Dan uwansu yake ta cikin qwayar idan juna koda ko ya boye a fuskarsa

Part dinshi ya nufa riqe da hannun lamido

Cikin karaya da yanayin cushewar tunani Yusuf ya kalli Adam cikin rawar murya yace biyaye inajin tsoro
Wlh tsoro nakeji
Adam kalli yadda Ahmad ya dawo
Adam kasani Na Sani iyayenmu sun Sani su Kansu su Bappa Yaya
Sun San cewa Ahmad Aysha yakeso
Itace burin ranshi
Sun kuwa San zai iya zaucewa in aka hanashi ita
Adam meyasa
Suke son
Sabautamin rayur Dan uwana
Kanshi yake ta jijjigawa da juya idan shi yasa lips enshi Na qasa a baki ya ciza da qarfi
Hawayen da suka cuko a idonsa yakeson su kwaranyo ko zai dainajin nauyin da ya danni qirjinshi
Amman ina abin yaqi
Da qarfi ya riqe hannu Adam yace
Biyaye ni
Banajin kaina banajin Aysha
Dan uwana nakeji
Adam ni
Yanxu Na gama tsara komai Na komawa cshool
Ba Wanda zan gayawa sai kai da Ahmad
Dan banson su Abba su San zan tafi nafiso sai naje Na kirasu Na gaya musu
Amman Adam kaga halin da Ahmad yake ciki
Adam ko dai Na fasa tafiyar Nanne
Adam in natafi Na bar biyaye da kai kadai zaka iya kula dashi
Cikin rawan murya Adam
Yace kaje insha Allahu ba komai yadda zaka barmu lfy haka zaka dawo ka samemu lfy
Duk kulan da kake tunanin zaka bawa Ahmad zan hada da nawa
Cikin murmushi takaici yace
Ya ja hannushi suka bi bayan su a parlo suka yada zaggo suna ta Dan taba hira
Har aka kira sallan LA asar Adam ne ya fara shiga yaje yayi alwala sai lamido yana fita yace
Yusuf kuyi saurifa kunsan innah tanan ca tana jirana kuga dare yanayi

Tare suka miqe Ahmad dinne ya fara shiga yayi alwalan sai Yusuf din ya shiga sauri sauri yayi ya fito
Har yazo baking qofar fita
Sai kuma ya dawo da sauri ganin abin mmk
Da sauri ya fito parlon ya kira Ahmad din hannushi ya jawo har gaban gado ya kalleshi cikin
Tuhuma yace
Biyaye jinin menene wannan a kan shimfidarka har kan pillows dinka ?
Shiru yayi
Cikin kaduwa yace Ahmad tabbayarka fa nakeyi

Cikin inda inda ya kama cewa A.a
Ai dama
Damafa
Biyaye ka Dane inda inda ka gayamin gsky
Lamido ne ya katseshi da cewa wlh kai dai bakaji
Dadiba Yusuf
Ka fiye bincike da qididdigar mutane
Kazo gidan sabbin amare Dan kaga jini a makwancinsu ka tsaya dogon bincike kai Amman dai anyi surkin banxa
Cikin jin dadin zance Ahmad yace qyaleshi dai duk suka fita suna dry Amman banda Yusuf Dan shi ya zargu da jinnan da ya gani
Har zasu fita Adam yace bamufa ga qauwar tamuba

Ras Ahmad yaji gabansa ya fadi har sai da ya fafe qirjinshi danshi har ga Allah mantawa yakeyi da wata a cikin gidan
Lkci daya kuma yaji kunya ta rufeshi ko ba komai Maryam bata cenceci haka daga gareshiba Dan ba laifinta bane

Muryar tane ta katseshi da tunanin da yakeyi

Cikin Dan sakin fuska tace laa ya Adam Hamma Yusuf ya lamido sannuku da zuwa
Da sauri ta nufi kitchen tana bari Na kawo muku abinci Yaya
Ta fada tana kallon fuskarAhmad din shi kuwa da sauri ya kauda ganinshi daga gareta Dan kunyarta yaji sosa
Yusuf ne yace a a Alhamdulillah mun gaisheku wucewa masallaci zamuyi

Cikin Dan tsoro tace
Ayyah Hamma Yusuf da sauri haka
Ko ruwan Baku shaba
Toh mubar sallan kenan ya fada fuska a daure ????
A ranshi kuma yace ba gashi ba har sun fara tsare mutane da raini

Cikin sanyin murya tace A,a
Toh Ku gaida su Ummi
Harara ya kuma watsa mata yace suwayen yan Aiken naki mu zaki aika
Kai ta girgiza gudun kar ta kuma mgn ya zama laifi
A ranta tace shi kenan Aysha am ke kam kin kade zama da wannan masifeffen
Tare suka fita
Ahmad Na bayan su
Har yazo baking qofar sai ya kuma komawa yazo dab da ita ya Sa hannushi ya tallabo fuskarta cikin rauni da
sanyin murya yace
Maryama kiyi haquri ki gafarceni
Rau rau tayi da ido alamar kuka da sauri ya zaunar da ita kan kujera yace ki yafemin ba nufina kenan Na cuxguna miki ba kimin afuwa yake yar uwata
Cikin sanyin murya tace
Ni baka min komaiba ya Ahmad kuma ko ka minima Na yafe

Cikin farin ciki ya subbaci goshinta ya
fita yana cewa rabbi ya miki albarka
Amin tace cikin jin dadin addu,arshi gareta

3:30 pm su inna sukayi sallama da su Ummi suka kama hanyar Yola sun tafi suna kewan juna

Yau saura kwana 2 Yusuf ya bar Nigeria

Da yamma su Abba da baba bello Na zaune a harabar gidan nasu Yusuf ne yashi cikin nitsuwa ya isa gunsu
Cikin biyeyya yace sannuku da hutawa baba
Abba yanxu naje hospital baka can anata nemenka kawai suna ganina suka tsareni
Baba bello yace a to kace yau ka Sha aiki kenan
ehh wlh baba har C,S nayiwa wata mata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button