NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da safe bayan ya gama shirinsa ya shigo ya ya rinqa binsu innayi ko wace har dakinta yana basu kudi da yi musu slm yana ce musu Allah ya sadamu da alkhairi
Duk sai yaji ba dadi

A farfajiyar gidan yaga Sadiq ya bude but din motarshi yana zuba kaya
Ga Aysha kuma a bayan Bappa Yaya tana kuka
Cikin tsoro take cewa wlh zai dakeni ni bazan tafi da shiba
Cikin mmk da take baki yace ke da Allah can ki rufe mana baki nima motata ba ta daukar mahaukata bane
Kai Sadiq
Rufemin mota Wanda ya kawoki yazo ya maidake ai ni ba bawan kubane
Cikin isa Bappa Yaya yace toh ai bani nace Ku tafi taraba ubankune ya fada kuma tunda kace kai kafi qarfi bari Na gaya mishi
Miqawa Sadiq woyar yayi yana maza kamomin bello
karba yayi ya kirashi bugu daya ya daga ko slmarsa bai amsaba yace toh bello ga isheshshen Dan naku yace bazai taho da itaba
Dry ya danyi Dan yasan anacan ana shan rgima tsakaninmu Yusuf da mutanen gidan baki daya.
katse kiran yayi ya kira Yusuf din
Bugu daya ya daga cikin takaici Dan yasan mgnar da zai mai
Toh kawai yace
Ya fito cikin motar woyar Na kunneshi daga dukkan alamu mgn yake mishi har yanxu
Da garfi ya fizgo hannuta da ita da jakar tata gaba daya ya cillasu a gaban motar gamida maida marfin gib ya rufe cikin fushi ya shiga ma zaunin direba ya figi motar da qarfin duk abinnan da yake baba bello Na jadda da mai Yusuf karfa kasa yarinyar nan kuka

cikin takaicin ansashi daukar ta a dole yace
Ni ba ruwan Na da itafa baba,,,,,,,, cikin mota ko a zuciye ya dago,,,,,,,,

Ina gaida dukkan ma karanta novel dinnan inai mana fatan alkhairi

By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????????
NAYI NADAMA
MI,WASMITI page 4⃣6⃣to4⃣8⃣Na
Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????????
Jakarta ya danna mata kan cinyarta cikin mugunta
Daga nan bai sake kallon ko gefen da taken ba
Titi ya zubawa ido
Yanata sharara gudu
Kafin 9:11 Am
Sun isa

Kashe gari
Tun da safe
Aysha ke kuka wuy wuy da hawaye da suka kasa tsayuwa
Saka makon bayanin da Abba ya mata Na tafiyarta tare da Hamma Yusuf din
Kuka take sosai tana pita parlorn Abban nata kitchen ta nufa
Ummi dake qoqarin hada musu breakfast ta fito da sauri gami da kama hannuta cikin tausaya mata da cikar takaici
Dan Sam Ummi bata son abin da zai taba mata autar tannan
Daki ta wuce da ita kan gado ta zauna gamida jawota
Cikin kuka ita kuma ta zame ta zuba guiwowinta a kasa ta kifa kanta kan cinyar umminta cikin tsananin kuka tace
Shi kenan Ummi nikam Na shiga ukuna Ummina
cikin Neman alfarma tacigaba da cewa Dan Allah Ummi Ku gafarceni Na tuba kumin afuwa dan son Annabinmu Dan Allah kar kubari ace tare zamu tafi da Hamma Yusuf wlh tsoronshi nakeji Ummi zai kashe miki nifa
Haka tai ta kuka tana surutai
Ummi ta dago fuskarta tace kalleni nan Aysha
Na miki alqawari
Indai Na isa
Da Hamma ku
To insha Allah bazai cutar da keba
Kisa ido kigani ni nasan iya koki da dokokin da zan bashi a kanki
Haka dai tai ta bata baki da kontar matada hankali
Dama tuni an qarisa mata shirinta

Ahmad kuma da Adam tun da sukayi sallan asuba suka taho gida Dan yiwa biyayensu rakiya zuwa airport
Suna tare a farfajiyar yar gidan bayan an gama dura jakukkunansu a but

Cikin nitsuwa
Yusuf yaje gaban baba bello ya Dan duqa gamida cire hular kansa cikin sanyin murya

yace toh baba zan tafi fatan Allah ya qaddara saduwarmu kan alkhairi ya Dan yi shiru kadan ya Dan kuma dago kanshi cikin rawan murya yace Ku gafarceni baba in akwai abin da Na muku cikin rashin Sani

A hankali baba bello ya dafa kanshi cikin son Dan Dan uwanbnashi yace baka mana komai ba Yusuf Allah ya maka albarka Yusuf mu iyayenku
xuqatanmu baza su iya yin fushi da kuba duk da kaso ka boye min tafiyar Amman ya zama dole nasan duk woni motsinaka shiyasa tun jiya Na sanar da kai munSan da batun tafiyar taka Dan kar da safe ka shirya ka tafi ba tare da ka nemi afuwar iyayenka da sanya albarkan suba
Allah yayima albarka
Hannun shi ya Sara kan hannu baba bello da ke cikin sumar kanshi yace
Amin ya rabbi

A hankali ya taka yaje
Gaba mahaifinshi
Cikin biyeyya ya duqa gaban shi ya dago ya kalli ma haifin nashi yace
Abba ka gafarceni ka San yamin albarka ko zan samu sauqi cikin rayuwata
Ya kuma Dan duqar da kanshi Yagi gaba da cewa yau zan tafi ina mana fatan saduwa cikin alkhairi

Kai Abban ya jinjina yace ba komai Yusuf Allah ya muku albarka baki dayanku da kai da yan uwanka INA maka fatan alkhairi cikin karatun ka
Amin yace cikin jin dadi
Haka yaje gaban Nenne ita ta samai albarka
A gaban Ummi ya tsaya cikin mmk ganin tana riqe da hannun Aysha ita kuma sai kuka take fuskarnan duk tayi jazur da ita
Ba tare da ya qara kallon inda Ayshan takeba yace toh Ummi ni kam zan tafi sai kuma Allah ya gaddara saduwarmu
Toh Allah ya kaiku lfy ya kuma dawo daku lfy
Amin yace cikin rashin gane me zancen Ummi yake nufi Allah ya kaimu lfy to shi da waye kenan
Cikin ransa kuma yace toh me ruwanka kai da zaka bar musu qasar
Cikin Dan sassarfa ya qarisa gun Adam rungume juna sukayi cikin qaunar juna
Adam ya Dan kai bakinshi dai2 kunneshi cikin sanyin jiki yace
Zamuyi missing dinka biyaye
A hankali yace insha Allah kamar yau zan dawo muci gaba da rayuwar mu mu 3 dinmu
Har yanxu suna ruqqume da juna cikin jadda dawa Yusuf ya Dan bubbugi bayan Adam yace
Adam nabar amanar Ahmad dinmu a hannuka Dan Allah ka kukan mana dashi ka Samar mai farinciki insha Allah nima inna isa zan aiwatar da aikin ummra zan roqi mahaliccinmu da ya cikawa Dan uwanmu farin cikinsa
Cikin qarfin hali Adam yace Na karbi wannan amanar
A haka ya sakeshi tare suka nufi gun da Ahmad din yake tsaye yana jingine da jikin mota Anuty Sadiya Na gefebshi wanda yanxu kenan isowarta

Ya
Isa gaban shi kenan Abba ya iso riqe da hannu Aysha cikin muryar umurni ya kamo hannu Yusuf din ya damqa mai annum Aysha cikin nasa ya hada ya rumtsesu
Cikin mmk ya dago ya zubawa Abba Ido cikin Ido sukayi
Cikin kaduwa ya bude baki zaiyi mgn
Da sauri Abba ya dakatar dashi dacewa
Bana son jin komai daga gareka Yusuf a yanxu haka umurni nake baka kai tsaye ka kama hannun matarka tare zaku tafi wannan umurnine kuma kab mun gama yanke wannan hukuncin

Cikin razani da kidima ya maida dubanshi kan baba bello da alamun tabbaya
Kai ya jinjina mai cikin alamun yes umurnine
Ummi ya kuma kallah cikin daure fuska tamai nuni da amanace

Cikin tsananin bugawar qirji ya maida dubanshi ga Ahmad dake gaban shi da ya zama tamkar an dasashi
Girjinshi ke duka 3 3 a take zufa ta fara keti mai tabbas yasan da tfyar Yusuf Amman baiyi tunanin za a hadashi da Aysha ba
Cikin sauri ya dawo kanshi ya kalli fuskar Aysha Ido cikin Ido sukayi cikin wata iriyar narkekkiyar murya ta saki kuka mai tsuma xuciyar mai sauraro
Kuka take tana wayyo ya Ahmad dina shike nan kun rabani da ya Ahmad dina
Cikin azama ta fizge hannuta daga cikin hannu Yusuf din da ya zama tamkar ruwan ya cinyeshi
Da qarfin ta fada qirjin Ahmad din ta Sa hannuta ta qaqumishi ta mannashi da qirjinta tamkar zasu chige cikin juna
Gaba daya shiki kam ya zama tamkar takarda jinshi yake a tsakiya shi ba sama ba shi ba qasaba tabbas badan a jingine yake da jikin motoba da tuni sun kai qasa
Bugun zuciyarsa kuwa tamkar zata balla girjinsa ta fito woje qoqol warsa ko gaba daya ta cushe mai ji yake kamar zai zauce
Allah sarki Ahmad damo sarkin haquri
A hakan yayi murmushin qarfin hali yasa hannushi ya dagota cikin ciccijewar voice yace Aysha ai tafi ya ba mutuwa bace koba Dade ko banjima zaki damo ki samemu
Kuma muma zamuna kawo muku ziyara
Ita dai kuka take harkamar zata shide
Hannuta ya kamo ya miqawa Yusuf cikin qarfin hali da juriya yayi Dan murmushi yace
Biyaye ko zaka iya riqe wannan amanar da zan baka cikin takun jarumta ya matso gareshi yace
Yusuf bazan taba gane kana so naba sai ka tayani son abinda nakeso fiye da kaina
Dry ya danyi kuma cikin dacin rayuwa yace INA nufin Aysha kuma INA nufin so Na Dan uwanta ka
Cikin mmk Yusuf ya zuba mai I do shi tunda suke da Ahmad bai taba kiran shi da woni sunan da ya wuce biyayeba Amman yau ya kirashi da yusuf kenan yana nufin amanar dai yake bashi da gsk

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button