NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin sanyi ya karbi Kalmar shahadar da maifinshi ke mai
Abba da yake ruqqume dashi kanshi a kan cinyarsa
Da qarfin ya ruqqumeshi gami da rumtse idanshi
Yana fadin innalillahi wa ibailaihi raji um
A hankali Yusuf yaji hannun Ahmad ya saki nashi
Cikin zaro ido ya kalli fuskar
Ido Cikin ido
Sukayi
Murmushi Ahmad din yayi Cikin sanyi yace
Biyaye ga amanar Aysha
Sai kuma ya daura da Kalmar Shahada
Idanshi suka koma suka kafe murmushin da yayi yana kan fuskarsa

Dr Umar ardo ne ya rinqa mai mata kullu nafsin za ikatul maut

Nenne dake gefe cikin gigita tace shike nan Ahmad kaima kabi yan uwanka Ahmad Na rabu da kai Sai kuma ta saki wani irin kuka mai ban tausayi
Gaba daya dakin ya rude
Hatta Abba kuka yake sosai ringume da gawar Ahmad din
Adam kam
Tuni ya fada kan Yusuf Cikin riqe hannushi
Yana
Shike nan Yusuf Ahmad ya tafi ya barmu Yusuf mun rasa Ahmad
Sh kenan yanxu dagani Sai kai Yusuf Ahmad ya tafi ya barmu

Maryam kam da Aysha qaqqame qawar sukayi Cikin firgici da rudani
Suke kuka kamar ransu zai fita

Baba bello ne da Dr Umar ardo sune suka samu Dan qarfin jikin miqewa baba bello kam Nenne ya kamo ya ruggume Cikin rawar murya yace haba ruqayyatu kar kibi Ahmad da kuka mana shin baki ga Rahamar da Allah ya mishi ba cikawafa yayi da kalmar shahada
Allah sarki Nenne Sai fafawa tayi jikin mijinta ta rinqa kuka mai ban tausayi

Cikin kuka Abubakar ya riqo hannu marya da Aysha da nufin ya jasu su fita
Da qarfin Maryam ta fada qirjin shi Cikin n kuka tace ya Abubakar da gaske ya Ahmad ya rasu Na rasa ya Ahmad
Kai ya rinqa juya mata yana zubda qollah????ya jata suka fita
Ummi CE ta matso Cikin kuka tasa hannu ta rufe mai idanshi
Su Usman da Rabi,u kam da abdul dama tuni suka koma parlon kuka suke kamar yara
Ummi CE ta miqe gami da kamo hannu Aysha da nufi su fita
Tana janta Sai gani tayi tayi yuu
Sai fadawa kan Yusuf tayi a sume
cikin firgita Ummi ta rinqa kiranta tana jijjiga ta Amman ina
Goggo Aysha CE tayi tunanin debo ruwan ana Dan shafa mata a fuska Amman INA ko matsi bata yiba

????????dimuwa. Da firgici da tsoro mai matuqar tsananin su suka sauqa kan rayuwar Yusuf inda ya zama tamkar mai Ciwon mantuwa
Lallai kuka ma Rahama ne
Shi kam Yusuf yau yake buqatar kuka a rayuwarsa Kuma a yau kuka ya mai tsada
Zuciyarshi ta kasa tuno komai qoqol warsa Kuma gaba daya ta tsaya bata aiki kanshi da jikin shi duk jinsu a juye suke????
Ido kawai Yusuf ke binsu dashi Sai hannushi da yasa ya damqi hannu Ahmad din
Su Ummi yake klo Cikin zare idon fuskar Aysha yabi da idonshi Cikin yanayin rashin sanin abin da akeyi

Hydar ne ya zo ya ciccibi Aysha yayi dakin Ummi da ita kamar gawa

Yusuf kam yana zaune a gun riqe da hannun gawar
Dr Umar ya ja Abba ska fita tare
Fuskar Ahmad din ya zubawa ido Sai ya juya ya kalli Adam dake durqushe a gefen shi yana ta kuka
A haka har zuwa tsawon wani lkci

       Allahu Akbar 

Lbrin rasuwar Ahmad
Ta kasance tam kar sauqan aradune a zuqatan yan uwa da abokan arziqi
Lbrin ya zama tamkar sauqan qanqarane ne a jikin mutane

Kafin wani lkci gida ya cika tab da yan uwa da maqota da abokansu

Baba Ahmadu ne da Dr Umar
Suka shigo
Daukar gawar Dan
Aje ayiwa gawar wonka ayi mata sutura a kaita makoncin ta

Cikin tsoro baba Ahmadu ya daqo yana kallon yadda dr Umar ke ta yin qoqarin cire hannu Ahmad Cikin Na Yusuf Amman …….

Allah sarki rayuwa Dan Adam Dan mutuwa nima kaina Aysha Ali Garkuwa rasuwar Ahmad ta zame min fami a zuciya ta ta famimin rasuwar yan uwana shiyasa wlh bazan iya ci gaba da typing ba har Sai zuwa gobe ????????????

By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????
NAYI NADAMA
????????????????????????
MI,WASMITI page 7⃣1⃣to7⃣3⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????

Amman gsky Baku kyautamin ba masu karatu ya kamata ace tsakaninmu Marubuta da ma karanta a ringa yiwa juna uzuri
Daga jin Ahmad ya rasu Sai wasu suka rinqa qananan maganganu wasu harda kirana a woya Wai meyasa zan kashe Ahmad ai wanna NAYI rashin imani Haba masu karatu kukam kuyi Haquri maNa Ku Biyoni A hankali ai zakuga yadda zan tsara mana abin masu bina ta prvt chart kowa da irin qorafin da yake min
Dan Allah mu rinqa yiwa juna uzuri
Wasu harda cewa ai gwara akashe Yusuf????
Ina Baku haquri wasu nace Na sasu kuka sosai karku damu zakuyi dry a gaba fiye da yadda kukayi dry a baya zaku Sha nishadi fiye da zatonku
Ku dai Ku hira Yusuf ya shigo hannu????????????????????

Jan hannu Yusuf din yakeyi yana qoqarin rabewa a na Ahmad din shiku ma Yusuf Sai damage hannu da yayi yana mai zuba musu ido
Kamar zaucecce a hankali Dr Umar ya zauna kusa dashi Cikin tausasa zuciyarshi yace
Yusuf saki hannu Ahmad
Kaji sakeshi a yanxu ba wani gata ko
Alfarma da zamuyi mishi sama da mu kaishi Cikin qabarinshi
Baiyi mgn ba bai Kuma sakiba Sai zuciyarsa da ta rinqa bugawa da qarfin qarfi

Hannu nashi ya jawo ya dawowa kan qawar yasa yatsunshi ya rinqa bude tafin hannu da Yusuf do ya damqe
Shi kam Yusuf kallon shi kawai yakeyi
So ya yake yaji shi shima a mace ko zaiji wani a bu a ranshi ji yake dama haukacewa yayi
A hankali zuciyarsa ta fara tuno mai abinda kalaman baba Umar ke nufi a take Kuma Sai jikin shi ya rinqa karkarwa
A haka suka samu suka dauke gawar
Cikin kuka Adam yabi bayansu
Shi kam Yusuf a wurin ya zauna kamar dasashi akayi

Acan Kuma akayiwa gawar duk abin da ya kamata kafin ma gari ya waye anyi komai an gama

Washe gari da safe wannan lbrin ya iski Anuty Sadiya
Duk da mijinta ta ya ji dashi akayi komai Amman ya rasa ta INA zai fara kawo mata wannan zance
Sai da safen yace ta shirya suje gida
Su gaidasu
A mota ta kalli mijinta Cikin sanyi tace Abban Yumin.
Na,am ya amsa mata Cikin sanyi
Sai kuma tayi shiru gamida dafe qirjinta
Hannushi yasa ya kamo nata yace
Kin kirani kin Kuma yi shiru
Kai ta daqo ta kalleshi Cikin rawar murya da alamar kuka zatayi
Tace Abban Yumin
Zuciyata Na tsinkewa tsoro nakeji ban San meyasa ba tun jiya nakejin faduwar gaba
A hankali ya jawota ya manna ta a jikin shi cikin fargaba yace ki rinqa addu,a ki Kuma kasance mai yarda da gaddara
Dai dai nan yayi parking a farfajiyar gidan nasu
A hankali ta zame jikinta ta fito
Cikin tsoro da firgita ta bude idanta da kyau ganin gaba daya harabar gidan a cike yake da mutane a take qafarta ta fara rawa Cikin tsoro ta juyo gareshi tana Abban Yumin me ya faru me kake boye min
Hannushi ta riqe tana jijji gawa da qarfi tana ka fada min INA Abba ban ganshi anan ba
Allah sarki
ita Sam bata kai tunanin ta kan qaninta ta rasa ba
Rabi,u dake gefe ne yayi saurin isowa gareta durqushe wa yayi a gaban ta Cikin kuka yace Anuty Sadiya ya Ahmad ya tafi ya Ahmad ya tafi ya barmu
Ido ta zaro Cikin tsoro Sai kuma tayi Cikin gida kai tsaye dakin Nenne ta nufa
Can ta hango Ummi da sauri taje gaban ta ta fada Cikin kuka tace Ummi
Me nakeji Ummi meya samu Dan uwana wayyo Allah wayyo Dan uwana wayyo Nenne Na wayyo cikina Ummi shike nan Na rasa Dan uwa
Adam ne ya kamo hannuta Cikin kuka yace Anuty Sadiya mun rasa Ahmad Anuty Sadiya Ahmad ya tafi ya barmu
Gaba daya suka ruda parlon kakace ta tashi itama Cikin kuka ta kamo hannu Sadiya
Da Adam tayi Cikin daki dasu

Suna shiga Sadiya ta hango Yusuf Wanda tun jiyan bai tashi a wurin ba sai sallan asuba da ya tashi yayi da taimakon hydar
Tana hoggo shi ga Nenne a gefenshi
Tana riqe da hannushi tana fadin
Haba Yusuf kayi mgn mana Yusuf katashi kaje qun baqin da sukazo yi maka gaisuwa
Haba Yusuf fushi kakeyi da yin ubangiji ne
Shin ase bazaka rungumi qaddara ba
Yusufa mufa musul Maine
Shi kam Yusuf ido ya zubawa Anuty Sadiya
Ita Kuma gabanshi tazo ta durqusa ta kamo hannushi ta kifa kanta kan cinyarsa ta saki wani kuka mai ban tausayi
Tana kuka tana fadin Yusuf ya zamuyi Allah shi yabamu Ahmad Kuma shi ya dauke shi
Dama kullum haka Ahmad ke gayamin ai Wanda ya Baku ni yaga fiku sona Anuty Sadiya ki dena damuwa da halin da nake ciki ase Ahmad duk maganganu da yakejin wasiyace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button