NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali ya daura nashi kan kan kafadarta
Yasa hannushi ya riqe nata Sai ya kuma kura mata ido
Yana jujjuya kai
A hankali tace Yusuf kayi min mgn ma ko zanji sanyi a raina dama kullum Ahmad cemin yake ko ya mutum kar Na damu gaka ga Adam da Abubakar duk abin da nake so zaku min
Kai ta juya cikin kuka tace Ummi INA Abba Ummi a wane hali Abba yake ?

Cikin duseshewar murya tace Sadiya
Abba tun a Daren jiya ya tafi Abuja shida Hydar Kuma yau dinnan zasu wuce India
A Dan tsorace tace Ummi Abba ne ba lfy ko ehh Sadiya abbanku baya Cikin hayya cin sa
Hawan jinisa ne ya tashi
Sai hawayen ke bin fuskar ta

Adam ne ya kalleta Cikin sanyi yace anty sadiya ko zakizo kije dakin Ummi ki zauna da su Maryam da Aysha da Amira suna can Sai kuka sukayi ba mai lallashin wani
Cikin sanyin jiki ta nufi dakin Ummin

Ayyah Maryam da aysha suna zaune tun jiya da Aysha ta farfado suke ta kuka abin tausayi Aysha abin ya hadu mata jiya tasan ba ummi
bace mahaifiyar ta kuma a jiya ta rasa ya Ahmad dinta Kuma a jiya tasan mahaifiyata ta rasu a lkcin aihuwarta
Ganin Sadiya yasa ta fada jikinta tai ta wani sabon kuka
Ta ruggumi meta nan sukayi ta kukansu
Da dyar dai suka samu suka tsagaita
Da kukan

Rayuwar gidan ya canja musu gidan ya koma tamkar ba kowa Sai masu zuwa gaisu da zaran bakin suntafi kuma to shike nan gidan yayi shiru
Rayuwar Yusuf ta sauya ta koma abin tausayi baya mgn da kowa komai za acemai da kai ko ido yake bada amasa duk masifar Na ta Yusuf da bala,I da mishkilanci yanxu babu su
Ya koma abin tausayi Baya iya mgn 5 lafiyeyyu
Komai ya rigada ya gama sauyawa
Aysha kam ko yaushe Sai ta shiga toilet tayi ta kukanta Sai fuska ta kumbura Maryam Kuma yanxu bata iya kukan ya rigada zuciyata ta bushe

Yau ne akayi sadakan 7 gaba daya baqi sun waste su Bappa Yaya ne kadai suka rege basu tafi ba

Yau kwana 10 da rasuwar Kuma yaune su Bappa Yaya ya zasu koma
Shiyasa da safe ya Tara zuriyar tasa
Bayan ya gama musu nasiha
Ya kalli Yusuf da Adam yace
Dudabe
Na,am ya amsa cikin
sanyi
Ido ya zuba mai cikin tausayawa yace
Yanxu me kakeyi a qasarnan ?
Kai ya sunkuyar gami da cije lips enshi yace me zanyi Kuma a qasarnan bani da abin da zanyi
Toh ka shirya kaida matarka Ku koma kaje kaci gaba da kara tunka
Aysha dake takure a jikin Nenne Cikin kuka tace Dan Allah Bappa Yaya Ku barni ni bana son komawa can
To me zaki zauna kiyi a nandin ?

Ni dai banson komawa canne
Ta bashi amsa Cikin kuka
Shi dai Yusuf shiru yayi Dan yanxu qoqolwarsa bata fiye gane me ake yiba

Haka kuwa akayi randa akayi kwana 15 da rasuwar a ranar baba bello ya kamma lawa su Yusuf shirin tafiyar su
A Kuma ranar ✈ jirginsu zai tashi

A hankali suke fitowa daga parlon suna zuwa harabar gidan
Bayan su Rabi,u sun gama Sa musu kayansu a but

Cikin sanyi Yusuf yaje ya durqusa gaban baba bello murya Na rawa yace baba zan tafi
Kanshi ya dafe Cikin qarfafa mai guiwa yace Allah ya kaiku lfy Yusuf
amin yace
Gami da miqewa yaje gaban Nenne itama ta mai addu,a
A hankali ya qarisa gaban umminshi
Ya durqusa guiwa bibbiyu yace Ummi zan tafi Amman bazan sake zuwa qasarnan da wuriba

Cikin
ajiyar hrt
Ta kamo shi ta tsaida shi
A hankali taja hannu Aysha ta samai Cikin nasa tace to ga amanar da Dan uwanka ya baka
Yana Cikin qabarinshi
mu kuwa mune masu ganin irin yadda zaka riqe amanar da ya baka a dai dai lkcin da ransa yake fita a jikin shi

Hannu yasa ya kamo Na Ayshan ya juya Cikin Rashin sanin me zaiyi
Ya jata
Suka qarisa gaban Adam ya ruggume juna sukayi musabaha
Ya kalleshi Cikin sanyi yace biyaye Allah ta sadamu kan alkhairi
Amin yace dai 2 lkcin da suka shiga mota

Usmanne da Rabi,u suka kaisu airport

3:37 pm jirginsu ya tashi

By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????

NAYI NADAMA
????????????????????????
MI,WASMITI page 7⃣4⃣to7⃣5⃣ Na Aysha s Garkuwa
????????????????????????????????

Allah sarki rayuwa mai juyawa
A
cikin jirgi
Yusuf ya zauna kan kuje rarsa ta number 24 yayinda Aysha Kuma nata number 23 ne
Nata kujerar itace kusa da window jirgin
A hankali Yusuf yake takawa har ya isa wurin zaman nasu
Jiki a sanyaye ya zauna
Gamida yin taqumi da hannushi daya ya Sada kanshi qasa
Bai tuno komai Sai ran da suka dawo India a lokcin da suka kamma la kara tunsu
A wannan jirgin suka dawo a wadannan kujerun suka zauna inda ya ke zaune anan ya zauna a wancan lkcin Na gefenshi Kuma biyayenshi ne
A hankali ya zubawa sit din ido
Zuciyarsa Na suya
Sai cije lebenshi yakeyi sabida kuka yake son yi Amman kuma ya kasa samun kukan

Yana Cikin wannan halin
Yaji abi Na diga kan wuyanshi
Hannushi yasa ya shafo wurin kamar ruwa yaji
Kai ya dago ya zubawa Aysha dake tsaye a gefenshi dafe da kan kuje ranshi
Hawaye wannan Na koran wancan
Kallonta yayi Cikin shawa,a
A ranshi yake cewa
Kinji dadi da kika samu kina kuka kina zubda qollah???? nasan koba komai zakiji sauqi a ranki

Sanarwan da akeyi Na koma ya koma gun zamansa jirgi zai tashi shine ya dawo dashi daga tunanin da yakeyi
Ido ya sake zuba mata
A hankali ya daqo
Hannushi ya kamo nata
Ya jawota
Gami da Dan Jan qafafunshi
Dan ta samu gun wucewa
Kan sit din gefenshi ya yaja hannuta ya zaunar da ita

Ita kam Aysha ido cike da qollah???? ta bi fuskar shi da kallo
Lkci guda Kuma ta tuno
Lkcin da zasu tafi wancan karon
Da ta tsaya a kanshi haka tana kuka
Cikin masifa ya rinqa surface mata bala,I harda yarfa mata mari yana mayya kawai kin wani tasa mutane a gaba kina kuka toh kanki zakici ai tunda kikayi kuskuren yadda kika biyoni toh wlh baqin jaki Sai ya fiki jin dadi
Cikin tsawa ya jawota ya tura a wancan lkcin

Tana Cikin tunanin taji jishi
Cikin wani irin voice yace
Kija bel dinnan ki saka
Kai ta sunkuyar Cikin zubar qollah????
A hankali
Jirgin ya rinqa
Qugi da Dan diri
Cikin tafiya a hankali ya rinqa Dan tashi sama
A hankali Yusuf ya maida kanshi jikin sit din ya lumshe idansa jikin jin wani irin azaba a karo Na forko da yaji yana qaunar barin qasarsa ta aihuwa
A karo Na forko da yaji ya qagu ya daina shaqar iskar qasar
A ranshi yakeji to me y rege masa a qasar nan
Babu ya fada a bayyane
Gami da bude idanshi da jin zafi a ransa
Ita kam Aysha ta window take yiwa qasar ta wani irin kallo da jirgin ya gama tashi sama
Ta kifa kanta jikin window ta saki kuka mai ban tausayi

Ido ya zuba mata gami da jinjina kai
A ranshi Kuma cewa yayi kuka ma Rahama ne bazan hanaki ba

A haka Cikin kukan bacci ya debeta
Yayinda shi Kuma Sai ajiyar hrt da yake tayi
9:00 Am agogon Nigeria
Dai2 da 11:00Am saudiya

Jirginsu ✈yayi landing Cikin birnin Madina
A hankali fasinjoji suka rinqa fita
Ido Yusuf ya rufe a sannu Kuma ya budesu
Kan fuskar amanar Ahmad dinshi
Cikin sanyin murya yace
Ke
Ke tashi mun iso
Kamar a mafarki taji muryar shi

Sai kuma taji tsoro Dan tuna wancan Zuwan nasu inda ya rinqa zuba mata mari Cikin fushi yace ko ki taso ko Na tafi Na barki
Bira alaqaqai kawai
Banza mayya..a wancan lkcin

A hankali ya katse mata tunani da takeyi
Muryar shi ta kumaji
Cikin Dan kauri yace
Ke INA mgn kinyi shiru
A hankali ta miqe
Tabi bayan shi
Har inda aka ta naji motici Dan ma tafiya wani ma aikaci Na biye dasu riqe da jakarsu
Har zuwa gun motar
Suka shiga suka tafi

A dai dai harabar wani qaton gida mai kama da ma aikata part part sun kusa 7

Abakin qofar su direban ya tsaya dai2 bakin qofar shiga
Suna fita
Yaja motarsa ya tafi
Jakar ta ya zubawa ido Cikin ranshi yasan bazata iya dagawa ba Amman kuma shima ga nashi
Sai kuma ya kalli inda take ta tsaya Sai rawan sanyi take Dan daga dukkan alamu anyi ruwan samane ya dauke Sai walqiya akeyi da iska mai sanyi da take kadawa
Hannu yasa ya dauki jakar tata yasa qafa ya tura mata nasa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button