
Ya juya yayi gaba a hankali tabi bayan shi
A parlo ya ajiye mata nata ya karbi tasa ya juya yabi Cikin Dan koridon da zai Sa dashi da parlon shi
Yana shiga ya fada kan 3 str Cikin
Yanayin shi da yafi kama da maraya
Ido ya lumshe ba tare da yayi bacci ba zafi yakeji sasoi a rayuwarsa
A hankali ya daqo phone dinshi Nenne ya kira
Tana dagawa tace Yusuf kun isako ? ehh yace mata
Gamida cewa ki gaida baba Sai da safe
Toh Allah ya bamu alkhairi tace dashi gamida katse woyar
Shi kuwa a nashi gefen kashe phone din nashi yayi gaba daya
Ita kuwa Aysha da qyer taja jikinta ta tafi bedroom dinta
Kan gado ta fada Cikin kuka a haka a ranan ta kwana kuka
Shi kuwa Yusuf kukan ya nema ya rasa shiya sa ya tashi Cikin rawan jiki yaje yayi alwala yazo ya rinqa nafilfili
Idan yayi sujjada ba abin da yakeyi Sai nemawa Dan uwan shi gafara
Washe gari da safe
Abokan Yusuf laraba suka rinqa zuwa mai taziya da dama daga cikinsa sun San Ahmad
Wasu sunsu Kuma insun zo kuka sukayi kamar zasu suma
Akwai wasu abo kansu su 2 Sulaiman da Bashir Wanda tare sukayi karatu a inda
Kuma suma yanxu suna Jami,atul madinan ne suna kara ilimi
Bashir Dan Katsina ne Kuma tare da matarsa sukazo
Mai suna Zakiya
Tunda sukazo
Sulaiman yake kuka kamar mace dan shi ya shaqu da Ahmad sosai kusan halin su iri daya
Bashirne ya rinqa Dan bashi baki yayinda dashi ma yake ta sharar qollah????
Shi kam Yusuf Sai cije lebe da yakeyi
Cikin daburcewar murya yace Zakiya ki isa gun qaunar Ahmad tana ciki
Ku gaisa
Toh tace mai gami da miqewa
Tayi candin
A hankali tayi SLM Cikin parlon ba kowa
Ido ta Dan bude Cikin zubar hawaye tana kallon parlon a shirya yake tsafta ba datti ko kadan komai Na parlon farine da jaa gashi labulayen suna sasake shiyasa Sai parlon yayi dubu kamar dare
SLM ta kumayi gamida zuwa jikin gini ta kunna wutan tsakiyar parlon
Ba kowa har ta juya zata fita Sai kuma taji sautin kukan a cin bedroom din
Juyawa tayi ta shiga dakin
Kan gado ta hangota tayi rufa da ciki Sai kuka takeyi tana
Ayyah ya Ahmad yanxu mun rabu kenan bazan Kuma ganin ka ba
Zuwa tayi ta zauna gefen ta Cikin sanyin murya
Da qoqarin danne nata kukan tace
Kiyi haquri Aysha ki daina bin Dan uwanka da kuka kiyi ta masa addu ,a shi yafi buqata a gareku ba hawayen ki ba
Dagowa tayi tana kallonta Cikin rashin Sani
Fahimtar hakan da Zakiya tayi shiyasa ta kamo hannuta
Tace
Ni suna Zakiya ni matar abokin Yusuf ne sunan mijinta Bashir
Muma muna qasar nan Kuma tare muke da mijina yana can gun Yusuf dinne .
Allah sarki Aysha rashin Dan uwa shiyasa a take taji zaki tamkar Maryam da Amira
Cikin hawayen tace kinsan ya Ahmad dinako ?
Eh Na sanshi Aysha
!
Ayyah to shinefa ya rasu.
ehh Na Sani Aysha
Kibar kukan Dan Allah
Wlh nima zaki Sani kuka
Kai ta jinji na gami da share hawayen ta tace
Ni ma banson yi mishi kukan kasawa nake in banyi kukan ba ji nake kamar zan mutu
Cikin tausa yawa tace ki rinqa addu,a kinji ko Aysha
Toh tace Cikin goge qollah????
Haka dai Zakiya tayi ta lallashinta
Har ta samu ta jawota suka shiga kitchen
Suka danti girki mai Dan sauki
Dan dama ba abin da babu a cikin kitchen din
Ita ta dauka ta kaiwa su Yusuf
T juya zata tafi Bashir yace in kin gama kizo mu tafi
Toh tace Cikin sanyi Dan tanajin tausayin yadda Yusuf da Aysha zasu kasance su kadai
A
Parlon ta zuba abinci ta matso ayshi cin lallashi tace
Ayyah Aysha ki matso kici abinci kinji ko
Kai ta girgiza tace bazan iyaba bakina daci nakeji
Ta Dan sunkuyar d kai tace Aysha bakya son nazo gobe ko ?
Da sauri tace a a wlh inaso
To kici abinci
Ayyah Zakiya nima ina son ci bazan iya bane shi yasa
Miqewa tayi gamida yin Cikin kitchen din furts ta dauko ta kawo mata
tace gashi ki daure kici koda inabinnan da Dan dabino ga Apple
Karba tayi ta danci
Sannan sukayi sallan insha
A parlon Yusuf Kuma shi da sulamai sun kasa cinnkomai shima Bashir sai dan tea ya Dan Sha
Bashir dinne ya miqe gami da kallon Yusuf
Cikin sanyi yace
Yusuf zamu tafi Sai gobe in Allah ya kaimu insha Allah zamuzo
Amman dan Allah Yusuf ka rinqa Sa dauriya a ranka Yusuf ka rege tunani Dan Allah kar ya maka illa
Kasan kana da matsalan zuciya
Kai ya sunkuyar Cikin ceje lips dinshi da gaba daya yanxu sun kubbura sunyi jazur sabida rashin kukan da bai samu yayinba
Sai yayi ta cizon lips din nashi
Haka dai Bashir ya rinqa bashi baki
Sannan suka wuce parlon Aysha
Sulaiman kam yana ganin ta Sai hawaye Dan shi yasan irin son da Ahmad yake mata
Kuma itama tasan Sulaimanu
Durqusawa tayi a gabanshi tana zubda qollah???? Cikin rawan murya yace
Sannu Aysha sannu da rashi Allah ya jiqanshi da Rahama
Amin ya rabbi ta fada Cikin kuka shima Bashir ya gaida ta sannan suka fita suka tafi
Shi kam Yusuf parlon shi ya koma Cikin kuncin zuciya
Yadda ya kwana jiya hakama ya kwana yau
Washe gari da safe Bashir da Sulaiman sukazo Zakiya kuwa sai da ta tsaya tayi musu girki sannan ta taho
Daga ranan haka sukayi tayi Sai randa suka cika kwana 7 da dawowa sannan suka daina zuwa
Su wuni Sai dai duk da haka kullum zakiya ke musu girki ta bawa Bashir ya kawo musu duk da baci sukayi ba yadda Bashir ke kawo shi haka yake zuwa ya
dau keshi
Sannu a hankali yau watansu daya da dawowa
Rayuwa ta juya ta canxa
Yusuf Dan qolisan nan gaba daya ya zama abin tausayi banda wonka ba abinda yakeyi ko mai bai shafawa
A hankali Dan sirinrin sajenshi Na ya rinqa qaruwa yana yawa yana bajewa ga wani irin rama da yayi duk ya canxa sai dai kyau kam kamar qara mai akeyi
kullum da safe yana dawowa masallaci Sai ya leqa gun Aysha a cewarsa amanarsa CE ita
Duk da ita kam bata ganin shi
Wata ranar jummah da daddare misalin qarfe 2
Na dare Aysha dake parlo Wanda a yanxu parlon ya zama dakin kwananta Dan
Da zaran tayi bacci a bedroom sai mafarkin ya Ahmad dinta ke bibiyarta
Shiyasa ta dawo parlon
Inda zata kwana kuka yayinda zata kwana jin sautin karatun Yusuf Kuma a parlon shi
Sai dai abin tsoro da firgici jin a yau ba sautin karatun Yusuf din take jiba Cikin firgita ta tashi da sauri ta nufi parlon bashi….. Tsoron ta ya qaru ganin abinda Yusuf din keyi
ta kidime ta rude ta kidime da sauri tayi kanshi……….
I love you all my frns????????????
Allah ya barmu tare
By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] +234 909 785 3276: ????????????????????????????????
NAYI NADAMA
????????????????????????
MI,WASMITI page 7⃣6⃣to7⃣7⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????
Kina raina Asma,u Adam admin din zauren guzurin gobe alqiyama????????
I love you all my frns????????
Kuka yakeyi cikin fitar hankali kuka mai ban tausayi gaba daya ya fita hayyacinsa
Jikinsa kab zuface ke tsatsafo mai tako ina
Ya zaune kan sallayah runqqume da qur,ani mai girma a jikinsa ga qaton photo su su 4 Shi da Ahmad din da Adam da Abubakar
Hannushi yasa ya dafe kanshi da hannu bibbiyu
Cikin kuka
Da ya samu rabbi ya sauqo mai dashi a yau
Cikin dashewar murya yaketa nanata wayyo Allah Na
Wayyo Allah
Ya rabbi ka bani ikon cin jarra bawar da ka jarab ceni da ita ya ubangiji kayiwa bawan ka Ahmad Rahama rabbi ka haskaka mai qabarinshi
Kanshi ya dafe da hannushi daya gaba daya jijiyoyin kan nashi sunyi rudu rudu
Hannushi daya Kuma qirjinshi ya dafe da qarfi
Gaba daya jikin shi rawa yakeyi
Sai zamewa yakeyi a kan carpet din
Cikin wahala ya rinqa kiran Ahmad shi kenan mun rabu
Ayyah biyayena
Bani da wani masoyi kamar ka bani da mai gayamin gsky kamar ka bani da Wanda nakeji a jikina kamar ka Kaine maisani farin ciki