NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Jiki a sanyaye ta miqe tana fita tana qunquni
Mugu kawai azzalumi danma kaga INA jin tausayin ka ne shiyasa ka
mutuma in kaga dama
Da sauri yace ke me kikace ?
Baki ta Dan turo tace a ni cewa nayi
Allah ya baka lfy

OK insa zaton ai
Qunquni kikeyi min
A haka ta fita
Ta tafi

Da rana
Bashir ya qara dawowa ya dubashi gami da bashi
Magunguna

Shi kuwa Yusuf tun daga wannan ranar
Ya kamu da ciwon kai
Dare nayi
Bacci zai qaura cemai ciwon kai mai tsananin zai rufe shi
Da zazzabi haka zai ta fama ga tsananin tunanin Dan uwan shi

        A 

Nigeria kuwa
Tun randa Aysha ta kira baba bello ta shei da mai halin da Yusuf ke ciki .
Gari Na wayewa
Ya karbi
Passport din Nenne
Da Na Sadiya
Dana Usman ya hada da nashi
Yayi ta musu shirin tafiya a cikin satin komai
Ya kammala

Ran da zasu tafi
Nenne ta maida maryama gun Ummi Dan kula da ita
Gashi tana fama da laulayin ciki
Allah sarki duniya
Randa Ahmad zai rasu a ranan rabbi ya albarka cesu da samun Cikin
Maryam kam takanyi kuka sosai gaba daya ta jeme Sai Dan fari da hancinta da ya qara fitowa

      Su Nenne sun 

Insa lfy
Randa suka iso murna a gun Aysha kam ba,a mgn
Dan basu gaya musu sun tasoba
Kawai
Da yamma tana zaune
A parlo
Yayinda Yusuf ke Cikin daki
Yana konce ne Amman hankali shi baya jikin shi
Konce yake yayi rigingine idanshi a lumshe
Hawayen ne ke ta bin gefen fuskarsa
Ba abinda yake tunawa Sai rayuwarsu ta baya
Kamar mafarki ya rinqa maimaita shi kenan yanxu
Ahmad ba kai a doron qasa yanxu bazan kuma ganin kaba
Bazan Kuma jinka ba
Yanxu dagani Sai Adam
A take ya rinqa jin daci Na tokareshi a maqoshi
Yana Cikin wannan
Halin yaji
Ihun Aysha dake parlo
Tsalle takeyi kamar qaramar yarinyar tana maqale da Sadiya
Jin tana ya Usman ase Dana kaima zaka zo
Ayyah inasu ya Rabi,u

Da Dan mmk
A fuskarsa ya fito jiki a sanyaye
Yana
Shiga parlon yaga baba bello a zaune kan 1 str Nenne da Sadiya suna kan 3 str Aysha Kuma Na maqale dasu a tsakiyansu
Usman Kuma Na shigo da kayansu
Da sauri yaje gaban
Baba Cikin Dan jin dadin gani su
Ya zauna a gefenshi Cikin sanyi murya yace baba
Dama yau zakuzo
Ni ban saniba.

Ehh ya CE gamida daura
Hannusha a kanshi
Cikin qashinshi ya tura yatsunshi
Daya hannushi Kuma fuskar shi ya shafa gamida shafa har kan sajenshi
Ido
Ya zuba mai Cikin kulawa
Yace
Haba Yusuf
Wannan wacce iriyar rayuwa kakeyi
Ne Yusuf kaga yadda ka maida kanka
Fa
Kanshi ya kontar kan cinyarsa
Gami da rumtse idanshi
Murya Na rawa
Yace
Baba ya zanyi
Ya zanyi ne
Baba bazan iya manta Ahmad ba
Baba mutuwar Ahmad bazata wuce A rainaba
Nenne dake gefen tuni ita ma ta fara zubda qollah????
Aysha CE ta fada kan cinyarta gamida sakin wani
Irin kuka mai cin rai
Sadiya CE ta dagota
Cikin zuba mata ido
Tace Aysha
Kuka zai dawo da Ahmad ne
A a tace Cikin kuka
Toh kukan zai mana mgnin zafin rashin shi da muke cikine a a tace Cikin share qollah????
Murmushi tayi mai zafi tace toh mu daina yiwa Ahmad kuka muyi mishi addu,a
Ba gata ko so da zamu nuna mishi Sai addu,a
Usman dake gefen Yusuf yace wannan gsky ne Anuty a man kinga fa yadda
Hamma Yusuf ya maida kanshi
Baba bello ne ya miqe gamida cewa
Yusuf maza tashi mu tafi muje a gyara maka gashin kankan nan da fuskar nan taka
Jiki ba qarfi ya kalli baba yace baba Bari a yi muku
Othern abinci
Sadiyace tai maza tace
A a Aysha zata tashi zamu shiga kitchen zamuyi duk abin da ya kamata
Toh shike nan ma kajiko

Suna fita basu tsaya ko inaba Sai wurin gyaran kai
Shi kam Yusuf ido kawai ya wore yana kallon yadda ake ta gyara mai kai badon yana soba
Dan shi komi yafi son yayiwa kanshi
Gyaran akayi mai sosai
Gashin nan Sai sheqi yakeyi dama gashi da yawa da sulbi tamkar valarabe
Sajennan yayi luv a sufkarsa
Gashin girarsa da suke kusan a hadewa
Suma sunyi ras sun qara qawata fuskar tashi
Lkci daya yayi rasa haibarsa ta fito gonin Sha ,awa
Daga nan suka wuce masallacin

Aysha kam yau tana Cikin gata
Girkinma
Usman ne da a Sadiya sukayi
Itako tana jikin Nennen ta

Sai faman cin inabi takeyi tana ta zuba surutun ta da rakadinta
daya bayan daya take ta tabbatar kowa

Bayan sun gama girkinne
Sadiya ta shigo itama suka zauna sukaci gaba da hirarsu

Usman Kuma ya dage Wai zai hada musu kunnun aya
Yanata kiciniyar tace marka den ayar ne
Su
Yusuf suka shigo
Bayan sunyi sallan insha
Cikin mmk Yusuf ya kalleshi a gyetsine yace toh Usman abin naka Kuma har ka kai nanne
Kana namiji ka wani zage Wai girji kakeyi
Dry ya danyi yace kai hamm Yusuf nifa ba girki nakeyi ba kunun aya nake hada mana

Kai da Allah tafi can kai dai dabi,ar mata duk ka iya ya fada tare da zama kusa da Baba belloN

Sadiya CE tace yoh to ba dole muyi girkiba tunda matar gidan bata
Ma San ta yadda zatayi wani abinba
Dan gani NAYI gas dinkun nan ko sau daya tema ba ayi Amfani da shiba

Baki ya tabe Cikin gyatsina fuska yace
Wannan me taiya in banda kuka da ihu
Dan tsabar iskanci
Girkinma Wai bazata yiba sai dai zakiya ke aiko mata
Baki ta Dan tura Cikin fakaice idansu ta watsa mai hara da murguda mai baki????

Ido ya Dan zaro mata Cikin tsawa yace
ke waye kikeyiwa harara????
Oho tace mai ai ni ba da kai nakeba ehe????
Ya gane sarai yasan shi tayiwa hakan
Shiyasa Cikin
Dabara ya miqe
Gamida juyowa ya kalleta
Yace zo ki dauko
Madara ki kawo wa baba
baki ta tura
Cikin shigoba tace
Toh
Ba ga Yaya Usman ba ya dauko mana ..

Tab lallaima yarinya kin rainani toh Dan nazo gidanku Sai aka cemiki ni Dan aikenku ne
Cewar Usman kema ya fada yana gyara koncinyarsa kan 2 str
Nenne CE tace ke Aysha ai wannan aikin kine mu kam baqin ne ai
Tashi ki dauko

Toh tace gamida miqewa ta nufi kitchen
Tana tafiya tana leqa fuskar Yusuf din
Dan tasan dai tayi mai abin da ya tsana shiyasa da sauri sauri ta dauko madarar
Tana uhm gwara nayi sauri
( ta Lamido kallube do wara tawa am hado)
Kar sarki mugayen Nana yazo ya sameni anan

juyowa tayi da sauqi Dan fita kitchen fin
Gim taji ta fada jikin mutum har saida robar ta fadi
Da sauri ta daqo
Ido ta zaro Cikin tsoro murya Na Dan rawa tace ….

By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????
NAYI NADAMA
????????????????????????
MI,WASMITI.page
8⃣4⃣to8⃣5⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????
Idanshi ya qara budewa
A take yaji yarrr gaba daya gashin jikinsa Na tashi
Kanshi ya kawar da sauri

Ita Kuma tsayuwa tayi jingine da qofar

Phone dinshi ya jawo
Yana Dan daddan nawa Amman Sam hankalisa baya jikin shi
Tsawon wani lkci bai Kuma kallontaba bai Kuma yi mata mgn ba
Itako tana tsaye a haka har bacci ya fara fizgarta
Sai tayi
Yuu kamar zata fadi Sai ta Kuma miqewa
Shiko
Yusuf bai qaunar ya sake daqo idanshi ya qara ganin abinda
Zai zame mai fitina ya hanashi bacci
Kai ya mayar jikin
Kujerar gami da lumshe idanshi
Tsaki yaja
Tare da miqewa ya nufi daki
Koncita
Yake sonyi.
Amman ya kasa samun nitsuwa
Tuni ya Dan
Fara tsotsan
Lips dinshi
Yana Dan tsurawa garu ido

Itako Aysha yana tashi ta dawo kan.3 str tai konci yarta

A haka tai baccin ta
Cikin konciyar hankali

Shi kam Yusuf acewarsa yayi baqin gani garin gane ganensa ya tado da azabebbiyar Sha,awarsa gashi
Tbs dinshi sun qare
Haka ya kwana Cikin
Matsi

Tun daga ranar Aysha a parlon shi take shi kuma yana cikin dakinshi
In gari ya waye ko zasu Dan zauna a parlon Aysha ayi ta Dan hira duk da ma shi Sai ido kawai yake binsu dashi ita kuwa harara ke
Hada su
A haka har sukayi
Kwana 8

Yau jumma
Dabi,ar Yusuf tun da safe ya shirya Dan tafi masallacin da wuri
Yasa Usman ma ya shirya
Dan shi kam baba tun da yaje sallan asuba bai dawo ba yana can

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button