
Juyawa yayi yaci gaba da aikin shi.
Ita kuwa kuka ta fara a hankali da ta lura bai kulata ba yasa ta saki kukan da qarfi
Don ta cika shi da takaici
Kallonta yayi Cikin harara ya mige tare da tattara phone dinshi da laptop dinshi ya ja kujerar
Ya fita yana juyawa
Phone dinshi ya dauki suwa alamar ana buqatar mgn dashi
Dagawa yayi Cikin nitsuwa da biyeyya yake gaida baba bello
Cikin farin ciki
Baba bellon ke sheida mai.
maryam ta aihu ta sami da namiji
Farin ciki ne sosai ya ziyarci rayuwar Yusuf
Ba abin da yake fadi Sai Alhamdulillah
(en yetti tak domen)
Mun godewa ma haliccinmi.
Ita dai sai ido take binshi dasu
A can Kuma baba bellon ne yace INA Aysha?
Gata nan baba ya bashi amsa
Toh bata woyar
Toh yace Cikin miqa mata
Phone din karba tayi ta kara akunne
Bayan sun gaisane
Yake cemata Aysha Maryam ta aihu.
Daga jin Maryam ta aihu kawai Cikin Salle ta
!qaradi da tsantsar farin ciki ta cilla woyar gefe
Ta tsaki qara mai qarfi gamida tsalle kamar yarinya
Ta rinqa juyi a tsakiyar parlon
Tana rawa Sai faman juya ququnta takeyi
Tana Alhamdulillah
(Amman hade do mi seyi)
Amman yau dinnan nayi farin ciki
(Mi yetti Allah mi hotai leddi am dayirdi am)
Na godewa Allah zan koma qasa ta ta aihuwa
Juyi takeyi sosai
Gaba daya jikinta Sai rausayawa takeyi
Duk ta gama kashe Yusuf kam a tsaye
Bai taba zaton yarinyar nan ta cika hakaba Sam bai taba tsura mata ido irin na yau ba gaba daya ya wore idanshi kan mazauneta da suketa juyawa tana ta faman happy
Ko idanshi ya kasa qiftawa
A hankali ya zaro harshensa ya Dan lashi lips dinshi da suka fara motsawa
Ita kam juyawa takeyi sosai har jiri ya fara diban ta
So take ta tsaya Amman ta kasa
Da qarfi ta rinqa yin baya-baya
Zata fadi
Cikin zafin nama da tsinkewar zuciya
Yusuf ya tallabo ta fada qirjinshi
A tsorace ta rinqa fadin
Hamma Yusuf zan fadi rami a gabana
Wayyo ka tai make ni wlh zan fada Cikin rami
Sosai take surutai
Hannu yasa ya dago kanta Cikin tsurawa pick lips dinta ido
Yace ke bude adanki
Ba dai bakya jiba
Ke haka kikaga ya dace ki nuna farin Cikin ki
Ba godewa Allah zakiyi ba sai rawa da ihu
Ita kam Sam idanta a rufe yake ganin hakane yasa ya qara kontar da kanta kan kafadarshi ya rinqa shafa kanta zuwa bayan ta
Har zuwa tsawon wani lkci
Sannan ta samu abin ya saketa
Tureshi tayi da Dan qarfin tayi cikin bedroom dinta
Shi kam Yusuf ya gama macewa a tsaye dagyer ya samu ya koma kan 3 str ya zauna yana maida numfashi da qarfi-qarfi
Jim kadan ta fito
Cikin doguwar Riga baqa wacce tasha aiki da pick din zare
Kanta ta yane da siririn mayafi shima pick
Tayi tarha dashi fuskarta ta fito rasa a ciki
Ga wani Dan ma daidaicin jaka rataye a kafadarta hannuta
Daya Kuma janye da trolley mai Dan girma
Cikin fara,arta da nishadi tace
Hamma Yusuf ni kam fa na gama shirin,
sannan kai Kuma kana zaune.
Ido ya zuba mata cikin mmk
Trolley ya kalla Cikin
Jan tsaki yace lallai baki da kai bakima San abinda kikayi
Ba
Yana kai nan ya tafi part
Inshi,
Aiko da sauri ta bishi a baya gamida riqo hannushi
Cikin karya suya da Neman alfarma tace Dan Allah Hamma Yusuf kar kamin mugunta ka hanani zuwa wlh Na gaji da garin nan ni nafi son in koma can qasa ta
Baki ya Dan tabe gamida daga kafada da Dan ware hannu alamar bai shafeni ba,
Aiko ta rinqa nacemai duk inda yayi tana biye dashi a baya
Ita dai su tafi
Can dai ya juyo ya kalleta Cikin murmushin mugunta yace
In kinaso zakije mana.
Ehh in a so ta bashi amsa da sauri.
Ko ?
Ehh takuma cewa.
Kai ya kada gami da cewa
Toh Amman fa da shara din zakibi dokana shike nan in kin qi kuwa bake ba zuwa
Ehh na yarda tace dashi Cikin zumudi tace
toh gayamin menene shara din naka?
Kai ya jinjina yace daga yau ke zakina…..
By garkuwan Fulani
[4/9, 2:25 PM] +234 909 785 3276: ????????????????????????????????????
NAYI NADAMA
????????????????????????
Mi,WASMITI. Page9⃣4⃣,Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????????
Fuska a murtu qe yace
Daga yau ki raba kanki da koke-koken
Da kikeyin nan sannan
Ki daina takuramin kin iya, girki bawai baki iyaba ki shiga kitchen kiyi girkin ki
Ni ban damuba bance kiyi daniba Dan ni ba zanci kwabenki ba
Sannan karki matsamin da batun tafiyar in kinqi kuwa,
Kina gani zan tafi Na nabar ki.
Cikin zumudi tace
Na yarda zanyi
Girkin
Kuma nama bar kukan
Ta fada tana mai goge fuskarta
Tabe baki yayi Cikin cewa da kin kyau tawa kanki…
Tun daga ran Kuma Aysha ta bar koke-koken Dan dama tanayi ne da gaya Dan ta cikashi Kuma tai tamai dry a fakaice in taga ya zage yana ta fifita mata tea
Ta rinqa cewa mugu tunda dai kabar cin zalina da sauqi.
Tun ran da ya gaya mata sharudansa
Kullum da safe zata tashi tayi wonka da sauri sauri
Dan ta shiga kitchen tayi musu breakfast Amman Sai tasamu ta makara shi har ya shirya ya fita
Sai dai taci sauran abin da ya bari ta Kuma nadewa kan 3str tai ta woya da mutanen
Gida pictures din baby Maryam Kuma tamkar dansu aka buga woyar ta
Duk wani shirin ta ta gama Sai jiran Comandan nata take kullum tanason ta tabba yeshi Kuma tana jin tsoro kar allaura ta to no mata garma. Shiyasa dole takeyin shiru.
Yau Alhamis wanda yayi dai dai
Da kwana 5 da aihuwan Maryam
Da yamma
Liris
Yusuf ya shigo
Parlon Aysha
Kai tsaye kan carpet ya zauna a tsakiyar parlon laptop yasa a gaba yana ta aikin latse-latse
Ido ta zuba mai Cikin yanayin son mgn Kuma tana jin tsoro shiyasa Sai ta kalleshi Sai ta Kuma kauda kai can dai ta gaji
Ta sauqo daga kan kujeran ta matso kusa dashi Cikin hikima
Ta fara mgn
A hankali
Tace Hamma Yusuf.
Bai amsa bai Kuma dagoba
Hakan tasa ta qara matsoshi Cikin
Qarfin hali tace
Hamma Yusuf
Kaga pic din boy dina
Ko ?
kalleshi ka gani kekkewa dashi mai
Kama da ya Ahmad
Kai ya daqo Cikin tsura mata ido
Yace boy dinki
Kuma
Yaushe kikayi cikinsa?
Har kika aifeshi?
duk ban saniba?
Baki ta tura Cikin jin takaici tace d’anane mana ai in munjema Zan roqi
Maryam ta ban shi.
Hmmm yace gamida harararta yace waya CE miki zakije?
Da sauri ta daqo kai tace Dan Allah Hamma Yusuf kayi
Haquri
Wlh in banjeba zan mutu
Kai ya jinjina yace toh ai naga ko sau daya baki aikata shara dinaba sannan Dan abinda Na ajiye in Na dawo zanci Sai ki tattareshi ki cinye.
Haka mukayi
Dake?
Da sauri ta gyeda kai tana a,a
Dan Allah kayi haquri wlh gobe kam zanyi na tuba
Ta fada tana qoqarin zubda qollah????
Da sauri ya daga mata hannu cikin murtuqe fuska yace ki hadiye hawayen ki
Allah kika yarda kika zubda qollah???? bazaki jeba.
A zahiri har Cikin zuciyarshi Yusuf bai san meyasa ba Sam baison ganin fuskarta Nata tsiya yar da hawayen da zaran ya ganta tana kuka jikinshi ke macewa burunshi ya ruggumota a ranshi zai ke ji kamar ya lashi hawayen Dan tausayi ta da yakeji.
a nashi ganin fa wai tausayi ne shiyasa ya dakatar da ita
Ita
kuma sai ta fara rau rau da ido Dan maida qollar
Miqewa yayi.
Ya fice daga gidan bai dawoba Sai dare.kafin ya dawoma tuni tayi bacci
A parlon ta ganin haka yasa shima ya konta a parlon shi gamida bude qofar da daga labulen ta yadda zai ke hanqo ta.
A haka ya kwana badan yaji dadiba Dan gaba daya yanxu ya saba da kwana da ita a girjinshi baccin dai yayi badan dadi ba.
Kashe gari Jumma,a kam tun 5:00 Am
Ta tashi tai wonka tana fita tayi sallah ta dauko wasu Riga da wondo black color Sai Dan rats in fari kadan
Wondo. Dan gajere iya karsa guy warta rigar Kuma ta Dan rufe mata cibi yar ta kadan
Amman daga baya bayan ta ya Dan bayyana ta kasan mazau nanta
Sai gashin ta da ta kitse ta saki jelar ta gefen kafadarta
Kai tsaye kitchen ta nufa
Tana zuwa ta fara kici niyar fere doya
Tana gamawa ta kunna gas ta daura shi daya gefen Kuma ta daura ruwan tea
Lkci daya sukayi dai-dai yadda take buqatar
Ta sauqe tea din ta daura a filas
Sannan ta daura kaskon tuyan
Ta fasa qoi da samai kayan qamshi sannan ta matso da niyar fara tuyan.
ta debo zata zuba Cikin kaskon kenan
Sai taji kamar motsin mutum
Gaba daya jikinta ya bata ana kallonta