NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Yau kusan satinsu 3 kenan da zuwa mambila amma Yusuf bai kuma zuwa ba kuma duk weekend sai sun je yau jumma,a bayan sunyi sallan la.asar duk suna hallare a babban palonsu suna ta hira bb bello ya dan gyaran muraya yace toh Yusuf kunsan gobe Saturday ko dan haka duk Ku shiyarya da wuri dan tfyar sassafe nake son muyi..
Ya dan tura hularsa qeya kadan yace hmm baba nifa ina da taya goben Ummi ta dan kalleshi cikin jin haushi tace wai kai kam wanne iron mutum ne kai Sam bakason shiga yan uwanka kowa mararin zuwa yake Amman banda Kai su kullumu basu da mgn sai taku Amman a fili kake nunawa Baka damu da suba Duk baqin haline hakan da mugun mishkilanci wlh bakaji dadin rayuwarka ba..ta qarishe mgnar cikin fada
Nenne ta dan kalleshi tace ina zakaje ne Yusuf ?.
Ya dan yamutsa fuska yace Yola zamuje dan tunda nazo bamu jeba gashi har klcin komawata ya fara matsowa Goggo jiyama saida ta kirani tana ta fada bamu jeba
Adam ya kalleshi da kyau yace wai kai ban ganeba fa kanata xakuje bakujeba kai dasuwa kenan zaku ? Ya dan harareshi ta wutsiyar ido yace toh da dasuwa nake zuwa ? Atoh nikam bazaniba ban saniba wataqil Ahmad zaije
Ya kalleshi a yatsine yace wlh sai kaje dole kaje mutum baison jiharsa ta aihuwa ko kadan
Ahmad ya danyi murmushi yace toh Abba mu dai gobe Yola zamu Abba da su Nenne su kace toh Allah ya kaimu lfy

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Haka kuwa akayi Adam badon yaso ba suka tfy Adamawa
bayan sallah azahar kada suka isa A hankali Ahmad yayi parking a harabar gidan hydar da Maryam dake qoqarin fitowa da sauri suka qarasa gunsu cikin jin dadin ganinsu hydar ya karbi briefcase en Yusuf da miqamar hannu suka gaisa Maryam ko da sauri ta fada jikin Adam tana welcome ya Adam sai yau kuka zo ya dan subbaci goshinta yace ya zafin garinku tai dry dai dai lkcin da ta fada jikin Ahmad ta dan dago kanta ta kalli shi tace kajifa ya Ahmad wai garinmu wato shikam bandashi murmushi kawai ya iyayi yana dan tureta daga jikinshi dan wani mugun Abu yaji yana yawo a jinshi abinda bai tabajiba dan ya runqumi su Amira ga kuma Yusuf dake ta watsa musu harara
A hankali ta nufi jikin Yusuf tana Hamma Yusuf yaus…..
Da sauri ya katseta ta hanyar daga mata hannu da murtuqe fuskarsa tamkar sojan dake filin daga Atake tasha jinin jikinta


Bayan sun gaggaisa gogga ta cika musu abinci a gabansu suna ci suna dan hira ba laifi yau yadan sake Amman dai baici Abinciba har baba Umar ya dawo ya jasu palonshi sukai ta hira yana musu da nasiha ya kallesu da kyau cikin qaunar yaran nasu yace Ahmad kunci abinci kuwa ? Alhamdulillah baba munci mukam Amman biyaye baiciba ya fada yana nuna shi OK yace ya kwallawa Maryam kira yace ta kawo mishi abinci ..
da kanshi ya zuba mishi ya bashi yana maza cinye banason dabi,arkannan ta zama da yunwa da gyar ya danci kadan ya kalli Goggo yace Goggo nonofa mai dan sanyi tana dry ta dauko mar mai sanyin gsky toh nanne ya danci
Haka sukai ta hira kashe gari suka dan zaga dangin babansu Adam
Da a zahar suka kama hanya sai jaligo

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Aysha kam tunda tasan yana dan zaman palon ta daina fita da zaran tasan yana gun bata fita duk da bawai mgnarsa take jiba qamshin turarensa ke fadamata yana palon
Dan gudun bala,inshi da duka

Yau tunda safe suke ta dan girke girken dan yau babban soja xai diro daga Abuja ya Abubakar kenan sosai take farincikin zuwansa dan yana gwada mata kauna ta haqiqa
Qarfe 2 dai dai ya dira a babban palonsu tana tsaye gefen dining area tana ta shirya mai abinci Sam bata lura tare suka shigoba da qarfi tasa dan qara ta fada jikinshi yako tallabota yana dan juyawa da ita a tsakiyar palon sai dry take sosai tana miss U ya Abubakar juyi yake da ita sosai tana maqale a jikinshi Ahmad dake gefensu farinci yake sosai a ransa ganin ayshansa Na cikin happy aduniya duk abinda zai sata farinciki to shima zai sashi farin cikin

Muje zuwa masu karatu aiki Na gaba Na Gode da kulawarku da qaunarku gareni Nina kuna raina ????????

By garkuwan fulani
[4/9, 1:48 PM] ‪+234 909 785 3276‬: ????????????????????????????????MI,WASMITI…..Page 6⃣ Na Aysha Ali Garkuwa????????????????????????????????

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Da garfi ta saki qara gami da fizge hannunta dan azabar da ya ratsata jini kuma a take ya rinqa tsirtowa abinka da farar fata gata da laushi kamar auduga kuka take sosai tana yarfa hannun tana bubbuga qafafunta a qasa Ahmad kam tuni ya kamo ta ya riqo hannu yana matse kan dan yatsar da niyar tsaida jinin amman abin yaqi Adam ya jawo handkerchief en Yusuf dake kan cinyarsa da sauri ya yagi gefen handk en ya kamo hannu ya daure kan dan yatsar Amman ina jinin zuba yake Abubakar kam da Ahmad tamkar a jikinsu jinin ke zuba kuka take sosai jin kukan yasa Ummi da Nenne suka shigo a tare da sauri sukayi gunta tana lafe jikin Ahmad cikin mmki Nenne tace kai Ahmad meya yankata haka shiru yayi yana girgiza kai yana damqe da hannun ba abinda yake furtawa sai sorry Aysha cikin jin takaici da tausayinta a hatsele Ummi ta buga musu tsawa kai ana muku mgn duk kunyi shiru ke Aysha waya miki muguntarnan dan ita tuni tasan mai aikata aikin dan duk suna zagaye da ita suna ta tausarta shiko oga ko a jikinshi ko inda suke bai kai idonsaba kamar baya gun kanshi a sunkuye yana ta danne danne a phone enshi ga cup en coffee a gabanshi yana dan Sha Ummi ta sake daka musu tsawa tace wai kuna jinmu kunyi shiru Rabi,u ya dan kalleshi yaga a sunkuye yake ya maida dubanshi gun su Ummi gamida gyaran murya ya dan dunqule hannushi ya miqar da dan babban yatsarshi ya nuna Yusuf in gamida dan musu alama shine yana gedawa Ummi kai da dan furta haaa Nenne tace toh Koma waye yanzu dai kai Yusuf zoka San yadda zakayi ka tsaida jinin kanshi a qasa yace Nenne ni kuma ? Ummi ta jinjina kai tace a a ba kaiba wani mugun da ban da ya yanketa wlh ka kiyayeni ka fita harka yarinyar nan dan banga me ta tsare maka ba tunda kai zuciyar dutse Allah ya maka baka da qaunar yar uwarka bare tausayi kullum sai mugunta fada sosai takeyi
Shiru yayi zuciyarshi najin zafin yarinyar da tsananta a ranshi shi kullum a kanta sai ranshi ya baci cikin jin takaici ya shiga dakin innayi ya fito rike da kwalbar turare da qarfi ya fizqo hannu ya matse ya danna bakin kwalbar fesss ya fesa cikin yankan
Da qarfi ta saki qara dan jin yadda azabar zafin ke ratsa jikinta har cikin zuciyarta sosai ta qanqame ya Abubakar tana wayyo Ummi ya qasheni ya Ahmad zafi nakeji gaba daya hannu sai bari yake Ahmad ya zagaya ya kamo hannun yana huramata iskar bakinshi mai sanyi yana dan shafa kanta Abubakar kuma yana dan buga bayanta a haka dai jinnin kam ya tsaya sai ajiyar zuciya take
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Gaba daya porlon sunyi shiru suna sauraron Bappa Yaya A hankali yayi gyaran murya ya dan jinjina kanshi irin Na manyan mutane ya kalli yayan nashi daya bayan daya cikin muryar gsky da gsky ya kalli baba bello yace bello mgnarmu akan yarannan lokaci yayi da ya kamata ace duk mai shirin aure ai masa Sam banji dadin ganinsu a haka kun xuba musu ido suna abinda sukaga dama ya dan yi shiru sannan ya kalli Aliyu yace Aliyu inason mako mai zuwa Umar yazo da qanwarku Aysha dan insha Allah zamu San matakin da zamu dauka akan abin cikin girmamawa yace to Bappa insha Allah zan kirashi
Juyawa yayi gunsu Ahmad cikin yanayin tabbaya yace kai Adamu kai ka fidda matar aureko ? Ehh ya bashi amsa yana mai nuna Amira yana ko dai baza ka ban ita bane a a Na isa nine mai badasu oho nasani ko zaka gwada ikonka..
Dudabe ya kira Yusuf ya dago cikin jin haushi yace meye kuma ? Ehh akwai batun aure fatan ka shirya dan bazaka bar qasannanba saida matar aurenka uhum kawai yace dan yasan tsohonnan da iya kalen fitina shi kuma Bappa Yaya cewa yake wlh kunji kunya kune manya kan Abubakar Amman gashi dayin aurensa shekata 2 kenan da da saurin rabo da har an samu qaruwa
Ahmad ya danyi murmushi yace toh ai shikenan muma zamuyi yanzu kam cikin kallon Ahmad din yace shiyasa Na yarda da kai Ahmad kai mutum ne sosai Na tabbata bazamu samu matsala da kaiba shisa matarka ta musammance Adam ya dan kalleshi yace mukuma ba mutane bane ko eh ai Ku kam gwara ma kai akan sarkin fadannan kam ya nuna Yusuf haka dai yaitawa zuriyarsa addu,a da fatan Allah ya maidasu lfy har bakin gate ya rekasu
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button