
kuka ta kama sosai tana
“a,a
ya Adam”
Cikin cije lips d’inshi
yace
“Haka ne mana Aysha
Kuma tunda hakane
Ni Na kira
Babanmu Na gaya mai abinda kikayi
Na kuma fad’awa Hydar yanxu haka sun taso daga Yola
So Sai ki tanadi abinda zaki gaya musu
dan Na lura mu duk kin raina mu”
Zuwa yanxu kukan take sosai
a hankali ta matsoshi cikin kuka ta d’aura kanta
kan guiwarsa
Murya na rawa
Tace
“Ayyah ya Adam dan Allah kuyi haquri
wlh bazan k’ara ba
Ka kira baba kace mai wlh bazan sakeba kuyi haquri dan Allah”
Ture kanta yayi cikin had’a fuska
Ya mik’e tare da cewa
“gafarar Allah da mijinki ya kamata ki nema ba ni ba
Wlh ki gyara ala qarki da Yusuf in ba hakaba wlh ba ruwana da ke”
Yana kaiwa nan ya fice abinsa.
A parlon
ya samesu Suna
zaune Ummi ta kawo musu breakfast
ya zauna gefen Abubakar
Ummi dake ajiye musu pilet tana
“a Adam dama kana cikine?
“cikin girmamawa yace Ehh Ummi ai tare muke da Ahmad”
Aiko naji dad’i yau yarana duk a guna zasuyi kari”
Abubakar
“Yace gsky kam Ummi yau kin hada yaranki”
Dry tayi cikin nufan d’akin tana bari Aysha tazo
Ta hada muku tea.
Ita kuwa Aysha a d’akin tasha kukanta ita bama abin da yafi cinta kamar Fushun Hamma Yusuf d’in nata
Gaba d’aya ta resa sukuni
Kukan tayi mai isarta sannan ta kifa kanta kan kujerar
A hakan Ummi ta sameta
Cikin kula tace
“Autan Ummi tashi kije ki hadawa yayunkin tea
Ko bacci kikeyi”?
cikin kauda kai ta goge fuska tace a,a Ummi bari inje
Cikin boye fuska ta fita
Dan kar Ummin taga halin da take ciki.
A parlon
Cikin sanyi ta zauna gefen Hamma Yusuf din ta jawo
Cups d’in
da pilets d’in
Abubakar ta fara sawa ta Dan tura mai gabanshi cikin sanyi tace
” ya Abubakar ina kwana”
Fuska a d’an sake yace lfy ya jikin dai?
“da sauk’i”
tace cikin Sada kai k’asa
Sannan ta hadawa Ahmad da Adam ta mik’a
Musu ba tare da kallonta ba suka d’an fara cin abincin,
A hankali taja d’aya cup d’in
da pilet din ta hada mai tea d’in
ta zuba mai cibs
da d’an k’oi
Ta d’an sunkuyo ta gefenshi cikin jin wani irin tsoro ne ko kunyace ko Nadama ce ta kasa ganewa
A hankali tace
“Hamma Yusuf
Ur breakfast is ready”
kanshi a k’asa tamkar bai jita ba
Jiki a mace ta Dan juya gareshi
cikin sanyi tace
“Hamma Yusuf
zaiyi sanyifa”
Bai kulata ba sai phone dinshi da ya d’auka ya fara latsawa
Ganin haka yasa
ta d’an tura hannuta ta k’asan
darning d’in ta d’aura hannuta kan cinyarsa cikin
sanyi ta rink’a
murza cinyar tashi
tare da d’an kauda kanta tana
“Hamma Yusuf ko wani Abu kakeso in defema”
kai ya d’ago cikin
Murtuqe fuska ya d’ago ya watsa mata harara
Har saida taji ta kware da yawun bakinta da sauri ta janye hannuta daga jikinshi
Shiko mik’ewa yayi cikin
Jan tsaki
da k’ara mata wani irin kallo
Itako cikin sauri tayi k’asa da kanta.
Kan kujera yaje ya zauna yana
B’iyaye
“Lkci Na tfy fa Abba Na jiranka”
Adam ne ya mik’e cikin
d’an sakin fuska yace
“Yusuf Ko zamuje kaci
girkin
Miraa?
baki ya d’an tabe cikin sanyi yace,
“Azumi nakeyi fa”
Ido Ahmad ya tsura mai Dan yasan abin da ya sashi cikin halinga
Lkci d’aya ya k’ara jin haushin Aysha
A haka shima ya mik’e tare da cewa
B’iyaye bari in wuce gun abban.
A haka sukayi part dinshi shi da Abubakar da Adam
A haka suka d’anyi ta hira
Har zuwa
2 dai suka fito
Bayan sunyi sallah
A farfajiyar gidan suka samu baba Umar da Hydar sun iso tare da Abba
Suna ganin su sukaje suka tarbesu cikin jin dadin ganin juna
Parlon baba bello suka wuce.
Bayan sun gaggaisa
Baba Umar ya kalli Yusuf dake gefenshi cikin
Sanyi da ta kaici
yace
“Yusuf kayi haquri insha Allah ubangiji Na bayanka
Kuma bazaka tabeba insha Allah zan d’auki mata ki kan
Wannan mugun abin da Aysha ta aikata ma”
Baba bello ne yayi gyaran murya cikin
Kallon Dr Umar
yace
” mu bazamu iya gyarawa ba kenan Umar?
Kana nufin mu Aysha tafi k’arfinmu ne?
kai ya d’aga cikin sauri
yace
‘A a wlh ba haka bane Yaya bello
Wlh rai nane ya b’aci matuk’ gaya
Amman ni ban tunanin kun kasa a kanta
Amman a gsky gatar tayi yawa har ta fara sata kauce hanya Dan ganin ba mai tsananta mata”
Ajiyar hrt baba bello ya sauqe cikin sanyi yace toh ko in haka ne ka barni da ita.
zamu d’auki mataki
kar kayi mata mgn Dan yanzu bata worwore sosaima tukun”
Adam ne
ya hada fuska tare da cewa
Wlh baba ni da zaku barni da nasan yedda zanyi da ita”
Hydar kuma cewa yayi ni wlh
banyi zaton haka daga gareta ba
Naji zafin abin a raina
yarinya ai ba hakane a kantaba”
Shi dai Yusuf
Ido kawai yake binsu dashi
A ranshi kuwa cewa yake
Koma dai me akayi ai ta rigada ta cutar dani ta gama kuntata min cikin kuma ba dawowa zaiyi ba gwara a barta kar a k’ara min zafi 2.
Baba bello kuma dole ya hana baba Umar mgn
Koda aka kirata tazo su gaisa zasu juya Yola yau din.
Gaba d’aya cikinta ya d’uri ruwa
tana shiga ta zauna gefen ya Hydar din nata
Tana
“ya Hydar barka da zuwa”
Ko kallonta baiyi ba
Baba Umar d’inma
da gyer yamsa gaisuwarta
Ya bud’i baki zai fad’a kenan
Baba bello yace
“A a bamuyi haka da kaiba
Ke Aysha tashi ki tafi
aiko cikin murna ta fita Dan ta tsorita
gashi duk kunyar kowa takeji.
A haka suma suka juya suka tafi.
Biyar dai dai Na yamma
Yusuf ya shiga kitchen din Ummi yana
Kiranta cikin
yanayinshi Na rashin wolwola
yana
” Ummee
Ummi dake tare da Aysha a kitchen d’in
ta amsa mai tare da cewa mene Na kiran nan”?
K’ara hada fuska yayi ganin Ayshan Na gun
cikin juyawa yace
“Ummi dama abin buda baki nake son ki had’a min Dan naga lkci kar ya k’ure’
Toh tace tare da
“cewa Aysha tashi
ki fara hada mai Dan INA da aiki da yawa ki daura mai kunun nono nasan yana so gashi dama Hydar ya kawo mana sabon nono
Maza mik’e”
Cikin sanyi ta mik’e
Shiko da sauri
ya CE
“Ban so a bari zanje gidan Anuty Sadiya ni wlh Ummi kin sani banson jogolgole da kwabe”
Yana fadin haka ya juya
Ita kuwa ido ta tsurawa k’eyarsa da gashin kanshi yayi luf a kwance
Ummi ko cewa tayi
Kiyi Aysha ki kaimai in yaga dama ya zubar,
Ita a nata tsarin
In ba haduwa sukeba bazamu dai dai taba
ta kuma ga alama Yusuf fushi mai tsanani yake,
Haka kuwa akayi ta hada mai komai
Ana fara kiran sallah
ta hada ta kaimai
d’akin ba kowa shiru
cikin kewar d’akin da mai d’akin ta
har renta take jin kewar Hamma Yusuf d’in nata
Tayi kewar komai nashi.
ajiyewa tayi can gefe sannan
ta tsurawa d’akin ido
Komai nan tsaf Sai
Kan mirror da ya hargitse da kolaben turaruka
Ganin haka yasa ta tattara ta goge ta jerasu sannan ta canxa mai bedsheet da blanket ta shinfid’eshi ta share d’akin
ta koma cikin gida ta dauko d’an kasko ta samai turaren wuta mai d’an Karen k’amshi da sanyi
Ta sassake labulayen sannan ta kunna A.C
Ta kashe wuta ta kunna Na jikin wani fulawa
Wutan read Sai ya haska kalan komai Na d’akin
Sannan ta juya ta tafi
A cikin gida ta dama mai fura da nono mai sanyi ta Sa mai k’ank’ara a ciki.
Sannan ta zauna ta d’an gyara gashinta
Ummi dai Sai binta da ido takeyi
Tana gamawa wonka ta shiga ta shirya cikin
Rigar baccinta yar k’arama mai laushi da sulbi
ta fesa turaruka sannan ta konta
tare da cewa Ummi
“saida safe”
Itako Ummi dry tayi cikin gano logonta tace
“Allah bamu Alkhairi”
Ta fita
Shiko Yusuf gidan Anuty Sadiya yaje
Sukayi ta hira da Baban Yumin bayan sunyi buda bakin.
8 dai dai ya biya gidan kaka
Dan dama ya kirata ta dama mai tura
Yana karba a gora ya juya ya fita gidan ya nufa
Da sauri d’an hadarin daya taso
Sai iskar dake kad’awa
Yana isa ya rink’a sauk’e numfashi da shak’ar k’amshin dakin sosai yaji Dan sanyi a ranshi
Wonka yayi cikin jin iska Na ratsashi ya shirya ya kwanta
duk bai lura da gyaran da akayi maiba bare yaga kulas din abincin
Gajiyar azumi tasa lkci d’aya bacci ya d’ebeshi
Gashi albarka cin azumin ya samu raunin abinda ke hanashi bacci.