NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Abubakar meyasa Sa kake abinda ke bamu tsoro”?

Shiko dry ya danyi tare da dafa Adam yace

” kallesu fa ya Adam duk sun wani firgice yoh me a ciki Ku dama kunada masu muku Addu,a ko kun mace nifa ban dashi”

Yusuf da yanzu ya fito d’akin Ummi yace

“kaima kana dashi”
Ahmad yace “sosaima Dan gasu Yusuf k’arami da k’anneshi masu zuwa daga baya duk nakane Sai ka zaba”

Sosai yai dryar Farin ciki
yace toh daga yau nine Abbinsu da sun fara mgn Ku koya musu sunana Abbi kuma su rink’a min Addu,a Allah ya kareni”

Insha Allah sukaci gaba dayansu dan jin dad’in ya sake

Shiko Yusuf A d’akin ya sameta zaune fuska a kumbure ido yayi jazir,
tana ganinshi ta mik’e da sauri zata fad’a jikinsa ya dakatar da ita cikin hada fuska yace.

“Dakata yanzu lkcin Rashida ne Dan zan kirata inji lfyarta”

Kamar wasa aiko taji Yusuf ya dage Sai hira yake da wacce yake kira Rashida dan Sai wani lumshe ido
yake.

Lkci d’aya taji wani irin malolon bak’in ciki ya tokari zuciyar ta cikin rufewar ido ta fice kai tsaye d’akin Ummi ta wuce.

Gaban Ummi da ya Abubakar ta zauna cikin zubda qollah
cikin mmk ganin yadda fuskarta ta yi jazir
Ummi tace.

“Auta lfy? me ya same ki?

Kukan da take dannewa ya kufce mata cikin rawan
baki tace

” Ummi wai Hamma Yusuf zai k’ara Aure
Ummi har kiranta fa yakeyi a gaba na”

Dry sosai ta kama Ummi da Abubakar Amman Sai suka danne cikin hada fuska
Ummin tace

“Ehh Auta”

Cikin zare ido da dafe k’irji tace

“Ummi ehh fa kikace toh sabo da me Aure fa Ummi yanzu kishiya Hamma Yusuf zai min”

Saiko ta k’ara sakin kuka.

Cikin Dan murmushi
Abubakar
yace

“Sabi da haihuwa yake so ke kuma bakya son haihuwar”

Cikin sauri ta juya gun ya Abubakar d’in nata jiki Na rawa
Tace.

“Wlh in so kuma zan Haifa mar ko 12 ne in zai ya bar batun Auren wlh zan haihu in Allah ya yarda”

Gaba d’aya Ummi da Abubakar sun cika da Farin ciki Dan ganin
K’aunar Yusuf d’in da kishinsa a k’wayar idanuta da jikinta.
Shiyasa cikin sanyi Abubakar yace
ke da mijinki ai ke zaki lallab’ashi Autan Ummi ni dai in an samu Na miji
Amin mai suna”

Baki ta d’an tura tace

“wlh bazai yarda ba ya Abubakar ka tayani bashi hak’uri”

Dry yayi sannan ya mik’e
ya ja jakarsa
Sannan yace

“Toh ba matsala
Muje parlon kinga lkci Na k’ure min”

Toh tace gami da bin bayanshi
Ummi ma bayanshi tabi suka fito.

A parlon gaba d’aya zuriyar suna cike.
Abubakar ya k’arisa Gaban baba bello
Cikin duk’awa
yace

“Ba yau zan tafi Ku gafar ceni hak’ik’a zan tafi cikin kewarku”

Kanshi ya dafa cikin sanya mai albarka
Sannan ya wuce gun Nenne itama sanya mai albarka,
Yana tashi yaje
Gaban
Umminsu da Abbansu
Hannu su ya kamo duka
ya d’aura a kanshi
Cikin sanyi ya manna kanshi jikin Ummi tare da sauk’e ajiyar hrt
Sannan ya maida kanshi jikin Abban.

Murya na rawa
yace

“Ummi Abba Ku gafar ceni
Ku yafe min duk wani laifi da na muku a rayuwata
Ummi ki gafarceni wahal dake da nayi tun ina cikinki”

Ummi kam tuni jikinta ya saki
Ba abinda take Sai cewa take.

“Baka min komai ba Allah ya ma albarka ya keutata rayuwarka Allah ya sanya sanyi a rayuwarka”

Amin suka amsa gaba d’aya parlon.

Cikin sanyi
Abba yace

“Abubakar ina alfahari da kai kuma ina mai ma fatan alkhairi a rayuwar ka
Allah ya ma albarka”

Amin ya amsa cikin sanyi ya saki Hanna yensu ya mik’e ya ruggume k’annesa su Usman
sannan ya dawo gunsu Ahmad hada Ahmad da Adam yayi ya ruggume su cikin
Sanyi yace “zan tafi da kewarku”
Suma ruggume meshi sukayi suna muma zamuyi kewarku d’an uwa.

yana sakin su ya kamo hannun Aysha
yace
“kinyi alk’awari ko? zaki min tokwara”?

A hankali tace ehh,
Dry ya danyi sannan yace

“Da kyau”

Hannun Yusuf ya damk’o ya jashi suka fito harabar gidan sauran ma suka biyosu a baya cikin tsokona a hankali
yace

“Hamma Yucut kaji ko Auta tamin alk’awarin mai suna,
Kuma ni har ga Allah Na yarda naku gamsu da Nadamarta,
Plss Hamma Yusuf a rink’a nunawa yaran pictures d’ina Dan su sanni”

Kai ya gyada mai cikin sanyi yace

“Insha Allah
Babiker ai dama dole zasu sanka
Abbinsu guda fa”

Juyawa yayi cikin Happy ya ruggume d’an uwansan.

Ciki sauk’e ajiyar hrt yace
“Ina sonka Hamma Yusuf ina sonka ina sonka”
har baki 3

Shi ko Yusuf ido ya tsura mai ya bude baki zai mgn kema.

Yai sauri ya shige mota
Fuska na zubda qollah
yace Na sani kaima kana sona d’an uwana
ya juya gun sauran
Cikin share
K’ollah yace
“Kuma na San kuna sona nima ina sonku
Amman Sai wota rana”.

Yana kaiwa nan yaja mota ya fice yana d’aga musu hannu.

Gaba d’ayansu binshi da ido sukayi jiki a mace,
har zuwa d’an wani lkci sannan suka koma cikin gida.

Shiko Yusuf d’akin shi ya koma haka kawai yaji jikinshi Na rawa
Sai dai ya zauna kusan awa 2 sannan ya mik’e cikin kasala
yaje Gaban mirror ya cire agogon hannushi zai ajiye kenan
idanshi ya k’ellah kan agogon Babiker d’inshi.

Ki ranshi yayi a woya yana d’agawa yace

“Ya akayi ne Hamma Yusuf”?
cikin sanyi yace

“ka manta agogon kafa”

Cikin dry yace
“Na baka”
Da mmk yace “Na Daimon d’innanne fa da kake so sosai”

“Ehh Na sani toh inada Wanda zan bawa ne da ya wuceka”

Dry yayi yace “toh ngd k’anina”

Cikin dry suka sallami juna,

Shiko ya fada toilet yayi wonka
zuwa lkcin
An kira azabar ya wuce massalaci
Bayan an idar ya
ya bi bayan su Ahmad suka shiga cikin gida.

Su Ahmad d’in sun isa tsakiyar parlon
Shiko yana bakin k’ofan parlon yaji kira ya shiga woyarsa
Sai da ya shiga cikin parlon sannan ya amsa kiran ganin Abubakar ne da mmk
“yace har ka isa ko”?
Yana mgnan yana hararan Aysha dake
Tsaye a k’ofar kitchen.

Gaba d’aya ido suka zuba mai jin ya saki woyarshi da k’arfi,ta tarwatse a kan tais d’in

Ahmad ne yace lfy cikin mik’ewa ya nufi gunshi
Ina kafin ya k’arisa gunshi
Sai haggoshi sukayi yayi
Luuu cikin sakin wani irin numfashi ya zube k’asa a………….

By garkuwan Fulani
[4/18, 10:14 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: ????????????????????????????????????
NAYI NADAMA
????????????????????????
MI,WASMITI page 1⃣1⃣6⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????????

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L.W

Cinkin firgici da rud’ani da bugawar zuciya Ahmad,
ya tallabo shi
ya d’aura shi kan cinyarsa,
jikinshi na rawa ya tallabo fuskarsa
cikin kasa mgn ya rink’a girgiza kai kawai,
zufa Na keto mai tako ina bugun zuciyar sa???????? Na harbawa da k’arfi.

Aysha ko cikin tsoro da zare ido da bugawar hrt da jin wani irin suka a k’akon zuciyarta ???????? ta iso garesu
Murya Na rawa ta
tallabo fuskarsa
tana juyawa
cikin d’imuwa ta rink’a
ki ranshi da d’an k’arfi tana.

“Hamma Yusuf, ka bud’e idonka menene ya sameka? me aka gaya ma”?

K’ara shigewa jikinshi tayi cikin tsonanin tsorita,
tace,

“Wayyo Allah Na wayyo Hamma Yusuf na ka tashi ka gaya min meke faruwa? me ya sameka”?

Juyawa tayi cikin kid’ina ta kamo hannun
Ummu wace
ta ke kamar an dasata ne Sai sanyi da ya rufe mata jikinta sanyin har cikin hanjinta a fili kuma Sai zufa ke keto mata.

Jijjiga Ummin tayi cikin kuka tace.

“Wayyo Ummi Hamma Yusuf dina
Ummi in ya mutu nima nasan bazan rayuba, wayyo Allah na Ummi kiga baya numfashi baya motsi”.

Adam ne ya Dan juyo gareta cikin k’arfin hali yace,

” Aysha ki nitsu kibar kukannan”.

Suna cikin haka phone d’in Ahmad
ya d’au suwa kamar bazai duba ba sai kuma ya d’aga ganin
Sunan Babiker ne a fuskar woyar
Jiki Na rawa ya d’aga ya d’an kara a kunne.

Lkci d’aya kuma ya saki woyar a k’asa cikin kid’ima ya rink’a juya kanshi
Sai yanzu ya samu bajinshi ya bud’e
kai ya rink’a juyawa yana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button