NAYI NADAMANOVELS

NAYI NADAMA COMPLETE

NAYI NADAMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kai kai kai Sai kuma ya ruk’k’ume Yusuf a jikinshi da k’arfi ya saki wani irin kuka mai cin zuciyar mai sauraro.
Kuka yake yana rawan sanyi yana k’ara k’amk’ame Yusuf d’in.
Adam ne
cikin tsoro da firgici
Yace
“Innalillahiwainnailaihi raji un
yace haba Ahmad ka sanar damu meke faruwa”?

Nenne da ta shigo yanxu jin kukan Ahmad yasa ta k’aroso da sauri
Jiki na rawa tace.

” meya faru me ya samemu a zuciyar nan? me ubangiji ya hukunta a kammu?
Ahmad
Ka gaya mana”?

Ummi kam hannu tasa duka biyu ta tallabe cikinta da k’irjinta
tare da cewa
Wayyo Allah Na cikina sanyi kamar hanjina zasu tsinke”

Da sauri Nenne ta k’arisa gunta cikin cewa
“meke faruwa damu ne”?

Aysha ce ta kamo hannun Ahmad cikin sakin wani irin kuka mai siririn sauri tace

“ya Ahmad meya faru”?

Cikin kukan da kifa kai jikin Yusuf a hankali
Yace,

“Aysha Babiker”
Sai kuma kife kanshi.

Ita ko Aysha cikin tsoro ta juya ta zubawa Ummi ido
Sai ta kuma sakin kuka.

Cikin rawan murya Ummi tace
“Aysha me woyar ta kamo min? yau kuma gaya min ya zanyi da mu k’addari”

cikin kuka da carkewar mgn tace
“Ummi ya ..
Ummi ya..
Ummi ya Abubakar”

Allahu Akbar uwa da d’a Sai Allah Sai mutuwa,
Ummi da fari murmushi tayi tana
Kullum nafsin za,ikatil maut.
Allah sarki
Abubakar Na ase ban kwana kamin da gsk
Ya Allah Na ka jik’an wanna bawa naka Abubakar”.

Ina Sai kuma zuciyar ta ta d’an yace
Cikin sanyin sauti
ta saki wani irin kuka tare da rik’e cikinta tana
Wayyo cikina
Allah Na Na godema da wannan jarrabawa rabbi ka fini son Abubakar Allah kasa can yafi mai nan Abubakar Na yafema duniya da lahira”.

Nenne kam itama kukan take sosai. tana Abubakar d’in ?”

Adam ko Komawa yayi ya zauna dirsham ayyah Usman
Dasu Abba da baba bello yanzu suka shigo gidan.

Suna shiga cikin tsoro baba bello Yace
“meya faru”?

Ba Wanda ya samu da mar mgn Sai kuka
Cikin firgici da hatsala yace,

“Ku gaya min meya faru? kunyi shiru”

Adam ne cikin kuka da wani irin voice Yace
“Baba Abubakar Abubakar ne ya”.

Sai kuma ya kasa k’arisawa.

Allahu Akbar cikin mutuwar jiki da tsoro Abba da Baba ballo suka zame kan kujera
Usman ko da Rabi,u da Abdul,
Hade kai sukayi wurin d’aya suna wani irin kuka mai sanyin sauti.

Cikin k’arfin hali baba bello ya rink’a musu fad’a shi dinma kamar a gigice yake
yana.

” Haba Ahmad yanzu wannan shine matan da zakuyi wa d’an uwanku
Adam har kai dinma kuka shine abinda zaku aikawa Abubakar
Usman ase ba Addu,a zakiyi mai ba”?

Ina shi ma Abba kanshi ya jingina jikin kujera yana ta nanata Addu,a Amman INA hawaye Sai zuba suke
Ganin kukan Abba yasa Aysha sakin wani irin kuka sosai ta rink’a jin tausayi Abban.

Cikin yin Hamdala Ummi tace

“Ahmad accident ne
Abubakar yayi”?

Kai ya jinjina alamun a,a”
Cikin mmk tace

” toh me ya sameshi”?

Murya Na rawa yace

“Ummi kashe Abubakar akayi”!

Gaba d’aya parlon suka juyo gareshi cikin rud’u da alamun tabbaya
Abba ne yace waya kashe min Abubakar “?.

Cikin sanyi yace

“wani yaronsa ne Adamu “

Baki Na rawa har suna had’a baki sukace Adamu,
Adamu Dan y’iware nan”?
Cikin gyada kai Yace shi ne.

Adamu wani Yaron Abubakar ne shike wakiltan sojojin kan hanya Na yankin Taraba zuwa binuye state kuma yaron ya dad’e da farautan rayuwar Abubakar Dan yana hank’k’o kanshi a matsa yin Abubakar kuma yana jin takaicin yedda Abubakar ke ta kai mai birki kan halinshi Na zalumci.

Toh da suka taso
suna tfy har suka isa cek point na kan hanyar Y’iwaren
ya samesu a lkcin azabar tayi sai
ya tsaya sunyi sallah da driver shi
cikin sanyi yace.

“Sani muyi salla anan gunsu Adamu Sai mu wuce ko”?

cikin tab’e fuska Sani Yace ‘ni wlh oga ban son Adamunnan mugune”

Dry ya danyi cikin sanyi yace

“kake kyautatawa dan Adam zato kaji ko Sani? ba abin da zai faru face da sanin Allah”

Shi dai Sani ba Don ya soba
suka tsaya sauran sojojin suna ta murna da ganin ogansu
Gashi da halin kyauta
Sunyi sallansu
Sani ya fito musu da Abinci da Ummi ta had’a musu sukaci tare da sud’in.

Sun gama komai zasu tafi
Wani daga cikin su yabi bayan Abubakar cikin sanyi yace

“oga Dan Allah kake kula da kanka a Gaban oga Adamu”

Dry yayi Yace ba komai Allah Na tare dani.

Har ya shiga mota
Adumun ya bishi rik’e da sanda irin ta kiwon shanu.

Cikin dry Yace ‘kai
Oga tsaya ba kai kace Fullo bane Sanda bata cinka
bari mu gani”

Cikin dry ya d’an juyo yana
“ai fulanin da nacema bana yenxub..
Kafin ya k’arisa Sai sand’ar yaji
kauuu a k’eyarsa zai juyo ya kuma sake mai d’aya a gadon bayanshi ya yunk’ura zai taso ya k’ara mai d’aya a tsakiyar kanshi,

Ganin abin ba Na wasa bane yasa sauran suka rarumoshi suka danne.

Shiko Abubakar cikin azaba ya fad’a jikin Sani.

yana numfashi da k’er yace
“Adamu yanxu nizakayiwa haka Amman ka sani Sai Na rama”
A take Sai ko ya fara aman jini.

Ihu bayan hari ganin haka Sai
Jikin Adamu ya d’au b’ari cikin tsoro da kuka
Yace.

“Na shiga uku
Abbakar aman jinin kakeyi
Dan Allah ka gafarceni”

Cikin aman Yace

“Sai Na rama fa”

Cikin kukan Yace ka rama indai zaka yafe min Dan Allah Abubakar ka gafarceni”.

Sai ya kuma sakin kuka

Shi kuma aman yak’i tsayawa cikin galabaita Yace
Na yafema Dan Allah tunda
Allah ma da kanshi yana son masu hak’uri da yafiya”

Cikin nishi Yace

“Sani kira min
d’an uwana kira min Hamma Yusuf
d’ina”.

Shine fa a lkcin ya kira Yusuf.

Shiko yana jin muryar d’an uwanshi

Cikin fizgar numfashi yace

” SLM Hamma Yusuf
Adamu yamin dukan kisa ni nasan zan mutu Amman Na yafe mai
Hamma Yusuf ko Na mutu Ku barshi Na yafe maiii,
Sai ya d’aura da Kalmar shahada…

ganin haka yasa
Sani zare woyar cikin firgita Yace..

“Hamma Yusuf
Oga Abubakar ya rasu ya tafi ya barmu”.

Furucin kenan da ya buga zuciyar Yusuf
ya sashi sumewa.

Cikin Sauri Abba ya mik’e
tare da cewa baba bello Yaya mu tafi mu d’auko
gawarsa muyi mai su tura”.

har sun mik’e
Cikin kuka
Aysha tace
Abba ” kalli Hamma Yusuf shima a sune yake tun dazu bai numfashi “

Su gaba d’aya Sai yanzu suka Ankara kan Yusuf dake ruk’ume jikin Ahmad.

Kai Abba ya jinjina ya zo suka d’aga shi shi da Ahmad
Sama suka haura dashi har kan gadon Abban suka direshi
Abban ya duk’ufa kanshi cikin zubda qollah.
A Ranshi yake cewa Rashin d’an uwa bai da misali”.

A hankali ya samu ya farfad’o sannan Abban ya mai Alluran bacci.

Su kuma suka wuce.y’iwaren
Kafin su iska sarkin garin yasa akayi mai sutura akayi mai sallah Aka kaishi gidan shi Na gsky da yake abokin bappa yaya ne
su Abbanma Sai k’abarinshi aka kaisu suka gani washe gari da safen sukayi sammako suka dawo
Adamu kuma da kanshi ya kai kanshi hukama dasu Abba sukazo
aka kawoshi garesu
Abba kam Na ganinshi Sai hawaye
Shiko baba bello cikin kuka
Yace

“Adamu kaci amanar abota a duniya”

Haka suka dawo gida aka zauna karb’ar gaisuwa

Shi ko Yusuf tunda ya farfad’o akayi mai Allurar bacci bai tashiba Sai washe garin da safe bayan su Abba sun dawo.

A hankali ya bud’e idanshi cikin wani irin tsinkewar zuciya da tuni abinda Sani Yace mai ya mik’e jiki Na rawa
Toilet ya shiga Alwala yayi cikin firgici kar acemai gsky ne abin da yaji
Sallolinshi ya rama sannan ya fara jera nafilfili.

Yana cikin sallanne Ahmad ya shigo ganin yana sallah yasa ya juya.

Parlon Ummi yaje cikin dashewar murya yacewa Aysha

“Auta kije d’akin Abba B’iyaye ya tashi ki tafin mai da abinci”

Aysha dake kwance jikin kakarsu innayi
Fuska a kub’b’ure fuskar tayi jazir ga wani zazzabi mai zafin gske cikin jin jirin ta mik’e tana goge k’ollah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button