
Kakace ta d’an rik’o hannuta cikin sanyi tace
“Kar kije mai da kuka”
Kai ta gyada cikin share k’ollah
A hankali ta haura saman
cikin sanyi ta bud’e k’ofar d’akin Abba ta shiga kanta a sunku ye
Shiko jin motsin bud’e k’ofar ya juyo a firgice.
ganin Aysha ya sashi tsura mata ido cikin son ganin fuskarta
Itako jin jirin yasa ta zame gabanshi
ta rik’o hannushi.
Ido ya zaro cikin rawan lips d’inshi
ganin hawaye a idon ta
cikin tsoro
Hamma Yusuf ya fad’a jikinta
kanshi ya manna a tsakiyar k’irjinta ya Sa hannushi ya ruk’k’ume ta cikin tsoro ya rink’a juya kanshi yana murzawa a k’irjinta kamar yaro cikin alamar kar ta gaya mai baya sonji
K’ara tura kanshi yake a k’irjinta
Itama Sa hannu tayi cikin kuka ta manna shi da jikinta ta k’ara matsoshi shi kuma k’ara narkewa yayi a jikinta…..
WANNAN NOVEL D'IN NA SADAUKAR DASHI GA Y'AN UWANA YAYUNA YA ABUBAKAR DA AHMAD ALLAH YA GAFAR TA MUKU Y'AN UWANA RABBI YA SANYAYA MUKU MAKON CINKU Yasa Aljannace makomarku".
By garkuwan Fulani
[4/18, 10:14 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: ????????????????????????????????????
NAYI NADAMA
????????????????????????
MI,WASMITI page 1⃣1⃣7⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????????
Pure moment of life writer’s
P.m.l.w
www.aishaaligarkuwa.blogspot.com
Lkci d’aya jikinshi ya rink’a bari yana tsuma hatta jijiyoyin kanshi saida suka taso sama fuskarsa tai jazir sai k’am-k’ameta yake,
ita kuwa kuka ta saki cikin dashewar murya ta sa hannuta ta tallabo fuskarsa ta rink’a juya mai kanta alamar yayi shiru,
Shiko bai ma san halin da yake cikiba gaba d’aya ya resa me ke mai dad’i a duniya.
A parlon kuwa Abba ne da Baba bello suka shigo Dan gaisawa da su innayi da suka iso bada jimawa ba
har sun juya zasu fita, Baba bello ya kalli Ahmad dake zaune gefen kaka cikin sanyi yace.
“Ahmad har yanzu Yusuf bai tashi bane “?
Kai ya d’an jingina a hankali yace.
” a a ya tashi”.
yana fad’a mai haka Sai suka fasa fitan suka juya suka haura gun Yusuf d’in.
Cikin d’akin kuwa Yusuf duk ya rikice Aysha sai kuka take shima cikin azabar zuciya ya samu kukan ya kufce mai da samun kukan sai ya daina rawan jiki sai zamewa yayi kan cinyarta ya kife kanshi ya rink’a wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro kukan da ka jishi kasan akwai k’una mai tsananin yawa a zuciyar mai yinshi.
Itama Aysha kukan take tana k’ok’arin tallabo shi.
Dai dai lkcin su Abba da Ummi da Baba bello da Ahmad suka shigo,
Su Na shiga
Kukan Yusuf da Aysha da yedda suka ruk’ume juna suna kukan.
ya tona musu zuciya lkci d’aya Ummi ta zame gefen su Cikin kauda kai
Baba bello ne yayi k’arfin halin mgn
Bayan duk sun zauna sun sasu a gaba
Cikin dauri yace.
“Haba Yusuf wannan kuka ya isa haka meyasa bazamu d’au dangana ba shin ase ina yebonka ase kai d’in kafi kowa sakewar zuciya ji yedda kasa matarka a gaba kana kuka yanzu kasan tsawon wani lkci da Aysha ta d’auka tana kuka kalli fuskarta fa ka tausaya mata mana itafa abu 2 ne ya had’e mata kukan rashin d’an uwanta da kukan tausaya wa halin da kai mijinta zaka shiga na tabbata da ta ga ka daure da matsalarta zata regu
kuyi haquri Yusuf am”.
Kai ya d’an d’ago Cikin kallon iyayen nashi lkci d’aya kuma ya fad’a jikin Abban su ya saki wani irin sautin kuka yana.
” Abba shi ke nan Babiker Na ya tafi bazai dawoba ya tafi har abada”
Allah sarki Abba shima kukan d’an nashi sai ya sashi kuka cikin kukan yace.
“Yusuf Abubakar baiyi gaggawa ba kuma muma bamu makara ba hanyace wace dole ko wanne mai rai sai ya bita Yusuf ba Abubakar zamu yiwa kuka ba kanmu mukewa kuka, sabo mukewa kuka duk yedda muke sonshi Allahn da ya bamu shi ya fimu sonshi ka dena yiwa d’an uwana kuka,
insha Allah muna zata masa Rahama ka tunafa kashesa akayi”.
Kuka ya k’ara saki Cikin k’uncin zuciya yace.
” Wlh ba dan Babiker da bakinshi yace min ko ya mutu shi ya yafewa Adamu kuma yace min koya mutu kar muyiwa Adamu komai,
badan hakaba wlh da Adamu Sai yaga k’ask’anci da sai ya d’an d’ani hukunci Amman Babiker yace kar amai komai”.
Jin haka yasa Ummi ma sakin kuka.
Aysha ce cikin kuka tace.
“Hamma Yusuf ka gani fa kasa Abba da Ummi kuka Hamma Yusuf kayi haquri ka bar kukannan”.
Ahmad ne ya matsoshi Cikin sanyi yace.
“Biyaye Abubakar yafi buk’atar Addu,armu da kukannan dan Allah ka daure ko iyayenmu Sa samu sauk’in abin”.
kai ya rink’a jinji nawa Cikin sanyi Ahmad d’in ya rink’a goge mai k’ollan.
A hakan suka samu ya d’an dawo hayya cinsa sannan suka jashi suka fita wurin amsar gaisuwa.
Suna fita gefen kakansu suka zauna shi da k’anneshi dasu Adam Allah sarki bappa Yaya Sai hawaye ke wonke mai fuska ganin yau Allah ya zare mai d’aya daga cikin jikokin nashi.
Cikin zubda k’ollah ya rink’a yi musu nasiha.
Da deddere Abba da kanshi ya kira Yusuf Yace yazo d’akin shi su kwana tare su Adam kuwa baba bello Yace su d’auki matansu su koma gida jensu da safe Sa kuma zuwa kafin ai safakar uku.
Shi ko Yusuf tun da suka shiga shi da Abba ba abinda yake Sai bawa Abba lbrin irin hirarrakin da Babiker d’in shi ya rink’a yima mai da yazo.
da k’er Abba ya lallabashi jin kukan da yake har numfashin Sa Na fita,
shiko
Kasa baccin yayi Sai tashi yayi ya d’auro Alwala ya rink’a karatun k’ur,ani mai girma karatun yake da Farin Yana kuka daga baya kuma Sai kushi,i ya halarto mai Amman haka ya kwana ba bacci kam Sai rawan sanyi da yake.
Itama Aysha a d’akin Ummi kukan da tasha ya k’ara ingiza zazzabi jikinta ga rashin cin abincin da takeyi lkci d’aya jiri ya sark’a feta ga amai da take Na wahala tayi kakari har ta banu amman ba abinda za harar kafin zuwa safiya duk ta galabaita.
Kashe gari da sake ta kama ranarce za,ayi sadakan uku Dan da wuni akayi lissafin.
Tun asuba su Abba da baba bello da su Ahmad da Yusuf dasu Hydar gaba d’aya dai zuciyar tasu suka hallara a masallaci gidan nasu da maqota da abokan arzik’i .
Akayi Sada kan uku ana watsewa su Ahmad kuma da k’annesu suka suka d’auki k’ura,anai suka rink’a karatu da Addu,a da nemawa mamacin gafara.har zuwa Tara da rabi sannan suka koma Cikin gida, a safiyar Dr Umar ardo da Goggo Aysha ma suka koma Yola Cikin jimamin rashin da sukayi, Hydar kam Yace bazai komaba tukun,
su Bappa Yaya ma sun koma
Anuty Sadiya ma Abba ya sata tfya dole tana kuka.
11 da kadan Na safe su gaba d’aya suna zaune a parlon Ummi harda Nenne duk Dan su d’ebewa juna kewa.
Ummi dake ta zirga zirga ta fito jiki a mace ta kalli kaka a hankali tace.
“Kaka jikin Ayshan Na fa yak’i duk ta gala baita gashi ko ruwa tasha Sai ta harar ni Na tsorita da abin” .
Hydar ne Cikin sauri yace.
“Toh Ummi mu tafi asibiti mana”
Kakan ma Asibitin tace suje,
Shiko Yusuf ido ya zuba musu cikin rashin abin cewa,
Sai Nenne ce tace
“toh Ummi ta fito mu tsfin yafi ai ko”?.
Kai ta jinjina cikin sanyi tace.
” ko tsayuwa fa bata iyawa jiri da rawan sanyi, Amman dai bari Na tallabota”.
Ummi Na shiga ta sameta ta fito wonkan da ta tayata ta shiga da Dan matsa ruwan kuma Sai ta d’an ji k’arfi kadan duk da tana jin jirin,
mai ta d’an shafa mata sannan ta taimaka mata ta zura doguwar riga sai d’an gyelenshi ta yafa, sannan ta Dan kamata suka fitoh parlon sunan
isa,
parlon sai jirin da wani irin duhu ya rufe nata ido,
Cikin sanyi da rashin k’arfin tace
“Wayyo Ummi zan fad’i duhu nake gani”.