
Shima k’ara rik’eta yayi
Sai ta kuma sakin nishi mai k’arf aiko sai ga,
Yaro k’ato fari tas ya fad’o cikin tafin hannun Hamma Yusuf d’in.
Wayyo dad,I Hamma Yusuf
Ruk’k’umesu yayi da baby da maman babyn yana hawayen farin ciki da hamdala ga Allah.
shiko yaro sai kuka yake tsalawa alamar lafiya yake.
Kai Yusuf ya sunkuyar Dan lek’a fuskar Amritanshi
Cikin tsoro da firgita da kad’uwa ya zazzaro ido ganin halin da Ayshan ke ciki duk ta k’ak’and’are ta matseshi shi da yaron cikin azaba ta ……
By Garkuwan Fulani
[4/18, 10:14 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: ????????????????????????????????????
NAYI NADAMA
????????????????????????
MI,WASMITI page 1⃣1⃣9⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
????????????????????????????????????
Pure moment of life writer’s
P.m.l.w
www.aishaaligarkuwa.blogspot.com
Ta kuma yunk’uri da nishi mai k’arfi sai ga yarinya ta sumb’ulo,
tana cillah kuka, Yusuf kam gaba d’aya ya cika da farin ciki sai hamdalah yake yana ruk’k’ume da family d’inshi,
Ita kuwa Aysha komawa jikinshi tai ta lafe tana mai maida numfashi da sauk’e ajiyar hrt tana mai hamdala.
Lkci d’aya Hamma Yusuf ya kimtsa yaranshi da matarshi shi da kanshi ya musu komai ita ya fara tallafawa tayi wonka tare da Dan gasa jikinta sannan ya fito da ita ya taima ka mata ta kimtsa tsap abinsu yara kuwa, goge su yayi tsap ya murjesu da mayuka sannan ya shiryasu tsap ya nad’esu cikin blanket nasu masu laushi da taushi farare tas.
Har zuwa 5 ya kammala komai shima yai wonka ya fito ya nufi masallaci bayan sun idar da sallah ne Ahmad da Adam suka tsareshi a gaba suna mmk Wai yaushe ya dawo shine bai fad’a masu ba,
Shi kuwa dariya kawai yake yana ruk’k’ume su,
Cikin kewar juna da k’aunar juna, ya kallesu cikin farin ciki yace.
“Na dawo jiya da dare dama nace sai kawai Ku gani da safe”.
Ahmad yace.
“Aysha ta murd’a kabbunta ko”?
Dariya yayi tare da cewa.
“A a baby’s sun kira Abbansu dai”.
Ido Adam da Ahmad d’in suka zuba mai cikin mmk da son gane zancensa.
Kai ya jinjina musu alamar
“ehh hakane”
Adam yace.
“Me kake nufi”?
Gyara tsayuwa yayi tare da Dan sunku yawa yace.
” ina nufin Aysha ta Haihu ta haihu jiya da dare bayan Na dawo ta haifa mana tagwaye”.
Lkci d’aya zuk’atan su suka cika da farin ciki
Cikin zumud’in suka wuce gidan Yusuf d’in.
A gidan kuwa Kaka na idar da sallah ta d’an fito parlon,
ido ta tsurawa corridor d’in d’akin su shiru ba motsinsu cikin d’an tunani ta komai d’akinta tana shiga kuma taji muryar Ahmad na kiranta da sauri ta fito
a parlon ta samesu ido ta tsura musu cikin tsoro
sai kuma tayi ajiyar zuciya ganin fuskokin su cike da annuri.
Adam ne ya kalleta da kyau yana.
“Kaka sai kawai muka samu yan tagwaye kai Alhamdulillah”.
“Harara tasaki musu cikin tab’e fuska tace
“ai koda bansan wahalar haihuwa ba haihuwar ba shan ruwa bane”.
Dariya Ahmad yayi cikin sanyinshi yace.
” toh ni dai nasan biyaye na ba mak’aryaci bane kuma Na yard a da zancensa”.
Shiko Yusuf kawai d’akin ya wuce yana shiga ya samu Aysha na rik’e da woya daga duk kan alama da Ummi take mgn dariya take tana.
“Wlh Ummi da gske Na Haihu kizo ki gani mana”.
Karb’e woyar yayi yana dariya yace.
“Ummi ke dai kizo kigani”
Cikin gsky da gsky tace.
“Ni banson shirme fa”
shima cikin gskyar yace.
“Allah Ummi kizo ki gani”
Toh kawai tace.
A parlon kuwa tare suka fito shi yana rik’e da macen ita kuma tana rik’e da Na mijin.
Kaka kam tana ganin Aysha ba ciki sai yara a hannu ta bushe a tsaye tana zare ido da tafa hannu,
suko su Ahmad karb’ar yaran sukayi suna ta ruk’k’umarsu da sanya musu albarka,
Ita kuma Aysha jikin kaka ta rab’a cikin tsokana tace.
“Kinga Hamma Yusuf d’ina ko yazo ya takalo nak’uda ya kuma karb’i haihuwar bamu ma baki tsoroba”.
D’an tureta tayi tana.
“Can tafi daga nan Ku dai wlh Allah ya shiryeku”.
Shiko Hamma Yusuf dariya yayi ya tallabo matarsa cikin so da k’auna yana.
” kin biyani ban mancewa da ranaku biyar masu haske a rayuwata”.
Ahmad da Adam da kaka kam farin ciki kamar su had’iye hak’oransu.
Kafin ace kobo gida ya cika da yan uwa yadda matansu Usman dasu Rabi,u
Su Ummi harda kukan farin ciki Hydar ma yana ji ya kawo Goggo Aysha da matarsa Nafeesat Aysha kam tana shan gata da kula
Yusuf ko duk nacin kaka da Goggo Aysha dole suke hak’ura da Yusuf da ya nace shifa tare zaike kwana da matarsa da yaransa dole suka yarda dan in sun hana ma a gunsu yake tarewa
Ummi zatayi fad’a yace.
ai yasan abinda yake shima kawai zai kula dasune.
Ran suna yara sunga gata da so gun kakannisu da iyayensu
Ahmad da Adam sun taka rawar gani inda suka hana Yusuf kashe ko sisi
Yaron
Yaci sunan Abubakar Abbanshi yace a kirashi da Abubakar d’inshi shi kuwa Babiker yake kiranshi ita kuwa mace sunan Ummi Aysha tace asa mata ana kiranta Mami,
Anyi suna lfy an waste lfy
Yara sun samun kula da gata tako wanna bank’aren.
Yusuf kuwa duk lkcinsa Na matarsa ce da yaransa ba ruwanshi ko gaban kaka lallatsata yake yana shi fa wlh ya gaji ai jego kam ya k’are.
Kaka ko tace jeki ya d’irka miki wani cikin tun yanzu shi ko a jikinsa.shi kuma sai yaita dry kawai.
Yau asabar ta kama kuma yau satinsu 4 da haihuwa,
Tara dai dai Na dare suka waste hiran da suke a parlon,
Yusuf ya d’auki Mami dake bacci,
Cikin murmushi ya manna mata kiss a goshi sannan ya kalli Kaka yana dan dry yace.
“Kaka kalli yadda yarannan suke ta k’iba gashi basa rikici sai suita bacci abinsu shi babiker yamafi Mami Na girmi”.
Cikin tuna baya tace.
Aishi Abubakar komai Na mai sunan shi ya d’auko in mutun ya ganshi zaice d’an shine Na cikinsa”.
Lkci d’aya fuskar Yusuf ta sauya, ya Sa hannu ya karbi yaron daga hannu Aysha ya had’a da Mamin ya ruk’k’ume su,
A take kuma ya juya ya tsurawa TV ido cikin bugawar zuciya
Tashan
MBC Bollywood ne suka sako tallan film d’in
Kal ho laa Ho
wak’ar ya rink’a ratsashi yana tuna mai d’an uwanshi yana tuna yadda babiker ke son film d’in
Lkci d’aya jikinshi ya fara tsuma cikin sanyi ya mik’e rik’e da yaran ya wuce d’akinshi,
kan gado ya dire yaran yaje yai alwalah yazo yai ta nafilfili yana mai yiwa d’an uwanshi addu,a.
Ita kuwa Aysha a parlon jikin Kaka ta rab’e cikin sanyi tace.
“Kaka yau kuma Hamma Yusuf ba zaiyi bacci ba
Kaka me zan mishi in sama mai nitsuwa Na tabbata yau kwana kuka zaiyi”.
Cikin share k’ollah Kaka tace.
“Aysha nima bansan ya akayi nayi mgnar Abubakar ba da nayi shiru”.
Cikin sanyi tace.
“Kaka ko bakiyi mgnan ba TV ya tuna mai ya Abubakar”
A hankali tace.
“Aysha tashi kije ki taushi zuciyarsa”
Haka ta mik’e cikin sanyi taje gareshi
tana shiga ta zauna gefen yaran ta zuba mai ido yana karatu k’ur,ani yana zubda k’ollah.
Lkci d’aya shima yaro ya fara kuka,
Itama Aysha sai ta tsurawa Hamma Yusuf d’in ido tana zunda hawaye.
Jin kukan yaron yasa ya rufe karatun yazo ya d’auki yaron ya mik’a mata ganin tana kuka yasa ya had’a su da babiker din ya ruk’k’ume.
Cikin sanyi yace.
“Na bari kema kibar kukan
Nasan ganin halin da nake ciki ya saki kuka toh Na bari Amrita bazan sake ba”.
Cikin kukan tace
” kayi alk’awari”?
A hankali yace.
“Zanyi alk’awari bazan sake kukaba sai dai nai ta mai Addu,a,
Amman kuma kema yau ki tausaya ki motso gareni Dan begenki ya kusan karni”.
Cikin sanyi tace.
“Hamma Yusuf ban gama workewa bafa”
Dariya ya d’an yi sannan ya d’age yaron daga cinyarta dan ya koma bacci ya kontar da yaron cikin sanyi yace.