Ni da Dr. SadeeqNOVELS

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 27-28

🅿️ 27&28

……nidai banceba yaya sadeeq”kwafa yaja yana tayar da motar”bayan sun hau titi batare daya kalletaba yace”.wane mataki kike a skul?”SS 3 fa nake”

Tab’e baki yayi yace”.nazata JS 3″sbd kinyi k’aranta da SS3″haba yaya sadeeq kallon y’ar yarinya kakemun ko?”yo meye ke inba yarinyar ba?”

Turo baki tayi batace komaiba”tanata kallon cikin motar”aranta tace”.har motarsa kamshinsa takeyi”

wayarsa dake hannunta tayi ringing”kallon fuskar wayar tayi taga
stupid girl

dariya Aysha ta dingayi tace”. stupid girl nakiranka yaya sadeeq”azatonta masifa zai mata”sai taji yace”.ki d’auka ku gaisa mana”sai kiyi dariyar sosai yadda zatajiki”amma dariyarki batada amfani tunda batajiba.

Ina ruwana da itane tunda bani takiraba”tafad’a wayar nakatsewa”tab’e baki yayi bece komaiba yana cigaba da driving d’in sa”

wani kiran yakoma shigowa”Aysha na murmushi ta d’auka”sweet heart yakake?aka fad’a dg d’ayan b’angaren cikin kashe murya”

Aysha tayi murmushi tace”. assalamu alaikum”wacece ke kuma?”ina mai wayar”Aysha tayi dariya tace”.basai kinji koni wacece ba”mai waya kuma yanajinki ,saidai baida lokacinki…ke banza y’ar iska nizaki….ashsha!gsky bakida sanin yakamata”miye abin ki zageni?”to yaya sadeeq d’in bazai d’aga kirankiba”tana fad’in hakan takashe wayar tana turo baki”

Dr sadeeq tamkar yayi dariya yadai danne bece komaiba”itama ajiye wayoyin gefensa tayi da keys d’in office nashi”

hakan yayi daidai da shigowar su cikin gidan”yana gama parking Aysha nata b’ata rai ta tura k’ofar….arufe tajita”juyowa tayi tana masa kallon tambaya”harara ya gallah mata yace”.saikin gama d’aure fuskan sai a bud’e miki”

Amma yaya sadeeq kasan halinta kace na d’aga?”gashinan tazageni tas”uhmm aiba tilas namiki akan ki d’aga ba”murgud’a baki tayi tace”.aidai nayi blocking d’in ta nakuma goge number d’in”

Tab’e baki yayi yace”.kin kyauta”to kabudemun”saurin meye kikeyi?”dan Allah nidai ka bud’emun na fita”tafad’a cikin narke murya”wacce batamasan tayiba”

Dr sadeeq kuwa tsintar kansa yyi dajin fad’uwar gaba”da yadda ta narke murya”beyi mata mgn ba, yabud’e k’ofar yafita”itama fitowa tayi”

amshi nan”juyowa tayi ta kallesa taga brief case nasa da wayoyinsane da keys d’in shashensa ahannunsa”yanata mik’o mata”

Ciki fa zan….kinsan banisan musu ko?”yafad’a fuska ad’aure”karb’a tayi har hannunsa danata yahad’u gu d’aya”

Kije ki bud’e d’akin ki ajiyemun ki had’amun ruwan wanka”dato ta amsa ta wuce”shi kuma yayi sashensu ammi”

Ammi,hindatu, khaleefa (d’an yayar ammi)duk suna zaune a main parlou”dr sadeeq yashigo da sallama Ahankali”

Duk suka amsa”hindatu na murmushi tace”.yaya sannu da zuwa”yauwa”ya gidan?”lafiya qlau”

yaya sadeeq ina wuni?”lafiya qlau khaleefa yasu hjy?”suna gaisheku”

yaya abinci najiranka”sai nayi wanka”ammi yaya jikin?”murmushi ta masa tana kallon keys nashi na office dake hannunsa”ta masa alama dasu”

Beganeba dai yana murmushinsa mai tsada”hindatu tayi dariya tace”.tanafa nufin ina baby”wai sholy?”uhmm hindatu ta fad’a tana murmushi”wato sabon suna yaya yasakawa baby? tafad’a aranta.

Tana k’ok’arin mgn Aysha tashigo parlourn da sallama…..tunda ta shigo khalifa ke binta dawani mayen kallo”hindatu na murmushi tace”.yanzun nida ammi muke tambayar yaya ke”

kamar ance sadeeq yakalli khaleefa”yaga gaba d’aya yamaida attention d’insa akan Aysha”

Aysha kuwa murmushi tayi ta zauna k’asa kan carpet tace”.ai dama nabiyosa fa”dannazo nagaisheku”

kingama aikin dana saki?”Eh nagama”kin gyara parlourn?”ah ah”ai agyare yake”cewar Aysha tana kallon ammi.nasakafa angyara yaya”cewar hindatu”

wanda akayi bemunba kije ki gyaramun”dan Allah yay….hindatu yaushe nafara fad’i in fad’a dake?”yafad’a fuska ad’aure”

Ammi dake zaune tana kallon komai da sauraren komai”tayita so su had’a ido da dr sadeeq amma yak’i yarda”

Hindatu kuwa tasha mamakin jin yafad’i sunanta”da wuya yakirata dashi sai baby”sbd shine yasaka mata baby tun tana jinjira”kayi hak’uri yaya bazan sakeba”

Sholy kina jiran nasake cewa kije ne?”d’ago kanta Aysha tayi zatayi mgn suka had’a ido da khaleefa daketa aikin kallonta”

To yaya sadeeq bara naje”tafad’a tana tashi tsaye ta kalli Khalifa tace”.ina wuni?”sbd ita saima sannan ta ankara dashi”

Lfy qlau yakke?”Alhmdllh ta fad’a tana fita”gaba d’aya dr sadeeq tsintar kansa yyi da jin haushin khaleefa”

Sis wacece wannan baby d’in?”cewar khalifa yana kallon hindatu”hindatu tasaci kallon dr sadeeq taga ita yake kallo yana wasa da keys d’in hannunsa.

K’anwarmuce!adangin daddy take”dg haka tayi shiru”dr sadeeq kuwa tashi tsaye yyi yabar parlourn”

Khaleefa yaga ammi Idonta biyu”da harshen turanci yatambayi hindatu kozata iya bashi number d’in Aysha”kuma meye sunanta awane anguwa take?”

Hindatu na dariya tace”. broth nifa bbu ruwana kayiwa yaya mgn”kuma batada waya”

Shiru yayi bece komaiba”amma gaba d’aya tunda yayi arba da Aysha yarasa nutsuwarsa”yaji sosai yarinyar ta burgeshi”

Khaleefa ba wani babba bane kusan age mate ne da hindatu”27 yrs”

ganin Aysha shiru bata dawo ba kawai yayiwa su hindatu sallama yafita”

Ita kuwa hindatu tsab tagane khaleefa son Aysha yakeyi”tabari yayanta yazo taji me zaice”

Aysha kuwa abinda yasa kawai ta koma ta gyara sbd ganin idon mahaifiyar sa”tasan dai aikin dayake tak’ama ya d’auke ta”a asibiti ne ba’a gidaba”to akan me zai sakata aiki agida?”

Da wannan tunanin ta koma sashensa ta bud’e”tak’arewa parlourn kallo taga fes yake”

zamanta tayi kan carpet tana latsa nokia d’in ta “aganinta ta zauna kan kujera ta zak’e”turo k’ofar yayi yashigo”

Okay zama kikayi kenan?”bafa haka bane yaya sadeeq”dubifa parlourn meyayi dan Allah?”

ina wayata?”suna ciki”kizauna anan akwai wanda zaizo nemana”banaso yazo ina ciki”sai kice yajirani idan yazo”dato ta amsa shikuma ya wuce ciki”

kayan jikin sa yarage yad’aura towel iya k’ugunsa”yawuce bath room”

yana fitowa yagoge jikinsa yashafa mai”jallabiya milk yasaka ya d’auki wayarsa yakira hindatu”ke Khalifa na nan koya tafi?”okay yafad’a yana kashe wayar yafita dg cikin bed room d’in.

Tana ganinsa tace”.yaya sadeeq bezoba fa”okay zan kirashi”natafi dan Allah?”dama rik’eki nayine”shiru tayi ta mik’e tsaye tabar parlourn”bata koma ciki ba”dukda yunwar datakeji”

nafef ta hau ta wuce gidansu”

Dr sadeeq azatonsa ciki ta koma”saiya kira hindatu yace”.kituromun sholy takamun lunch nawa”ai batazoba yaya”bece komaiba yakashe wayar”

Aysha kuwa koda ta iso gidan”dama ba abinci ake bataba”sallar la’asar tayi tafita taje ta siyo wake da shinkafa taci ta k’oshi”acikin y’an kud’in datake samu gun anty murja ko hindatu”

Tana nan zaune sai cikinta yadinga ciwo da mara”sbd watantane”kuma haka take fama dashi duk idan zatayi.

tana kwance tana juyi kan y’ar yololuwar tabarmarta”fiddausi ta shigo d’akin kamar anjehota”ke baba yace”.kije waje kinada bak’o”

gsky banida lafiya bana iya fita”lallai wuyanki yayi k’wari”uffan Aysha batace ba”fiddausi ta fice dg d’akin.

bbu jumawa baffa idi yashigo yanata zage zage “goggo sa’a natayasa”

Y’ar iska zaki tashi kije ku gaisa dashi ko kuwa??yo mlm bak’in ciki take mana kar muci arzik’i ko?”Inda bintu tabata umarni fita tad’i “tak’i zuwa tunda uwartace”cewar goggo sa’a”

kibarni da munafukar Allah”Aysha na kuka ta saka hijab ta fita”baffa idi yasamu Alh nura Asoro yace”.nina wuce gun aiki sai safe nida dawowa gida”yadda kukayi kasanar mun kota wayane”dato Alh nura ya amsa”shikuma yabar gidan….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button