Ni da Dr. SadeeqNOVELS

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 29-30

🅿️29&30

……washe gari Aysha ta farka idanuwanta duk sun kumbura sbd kuka”wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga bak’a ta yane kanta da mayafin ,yadda taga anayi”ta feshe jikinta da turare”powder da kwalli kawai tashafa”amma ba k’aramin kyawu tayiba”idan kaganta bazaka iya cewa dg nan gidan ta fitoba…lox”pad da wayarta tasaka cikin hand bag nata”tana k’ok’arin saka takalmi…..taji muryar baffa na k’wala mata kira”

 cikin fad'uwar gaba tasaka takalmin ta fito"dan ubanki abinda kikayiwa Alh nura kenan?"to wlh ko mutuwa zakiyi saina samu kud'i ta hanyarki"

Banida lafiya fa baffa
“shine nace masa…yimun shiru algunguma”goggo sa’a data fito ta karb’e zancen da cewa”idan baki lafiya yanzun gidan uwar wa zakije ne?”kwanakifa haka kace tabi Alh rabe”yarinyar nan haka tabamu kunya….

Aysha na kuka tace”.dan Allah baffa nidai kowane irin aikine zanyi nasamu kud’i nakamaka”amma banda sab’on Allah”

shegiya !munafuka ! y’ar bak’in ciki”muddin bakiyi sanadin nasamu kud’i ba”wlh korarki zanyi”

Ubanki be bar komai ba sbd tsiya ta masa kanta”ke kuma dole ki nemamun kud’i”kodan sbd kyawunki”amma dan kina y’ar bak’in ciki shine bakyaso ko?”

To tunda kin kori Alh nura “bansami kud’in dana saka rai agunsa ba”dole ki fita nabaki awa 5zuwa 6kiyi yadda zakiyi kikamun dubu 10”

Ah ah mlm tadai kamaka dubu sha 12 gsky”sbd nima ina buk’atar kud’in”cewar goggo sa’a tana hararar mijin nata.

yayinda Aysha kanta ak’asa batace komaiba tanata kuka”tasha alwashin yau zataje anjima gun anty mero(kawar ummanta) k’ilan tasamu number d’in umman.

Cikin fad’a baffa yace”.zaki wuce ko kuwa?ko kukan jini zakiyi sai kin samosu kona miki shegen dukan dakika kasa tashi agidan nan”

Be rufe bakiba Aysha tabar gidan da sauri”

tana share hawayenta ta tsayar da adaidaita”ko gidan ammi batajeba”kuma batayi rubutunba,tama manta gaba d’aya”

Abakin get d’in asibitin aka sauketa”bayan ta sallamesa ta wuto ciki”

gaba d’aya zuciyarta acunkushe take da k’unci da b’acin rai”murtala na zaune”bata tankashiba ta nufi office d’in dr sadeeq ta murd’a”arufe taganshi”

dawowa tayi ta zauna ta kalli murtala yaya sadeeq bezoba ne?”eh gsky bezoba”bema cika kai irin wannan time d’in ba gsky”

Amma naga ai 7 yake zuw…..maganar ta mak’ale mata sbd ganin dr sadeeq datayi “yasha wankan manya kaya”abin saidai ace masha Allah!harma yagaji dayin kyau”fuskarsa ad’aure”yyi banza da murtala dake gaishesa”wani irin haushi yaji daya sami Aysha anan zaune suna mgn”

wato shi yana can gidan ammi zaman jiran idan tazo su wuto tare”shine tazo nan tana watsewa wani banza hak’oranta”

da wannan tunanin yabud’e k’ofar yashiga office”Ahankali ta shigo “jikinta asanyaye”sbd ta lura fuskarsa ad’aure take”

yaya sadeeq ina kwana?”tafad’a bayan ta duk’a”banza yamata yaja kujera yazauna”tashi tsaye tayi dg d’ukiyar datayi”tanajin damuwarta ta k’ara yawa”ko ina bbu dad’i”

ko ina ta gyara kamar yadda ta saba”dr sadeeq be koma mata mgn ba”itama bata koma masa mgn ba”

ganin ta gama komai ,gara taje gun anty datayi ta zama haka”ta saci kallon sa”zanje waje dan Allah?

Ina ruwana?”aina zata banida matsayi agunki ko k’imar tambayata”dg yau na hanaki mgn da murtala”idan kuwa Kika koma koma dg ke harshi zanbaku mamaki….ina can ina jiran kizo mu wuto nan”ashe ke kinma zo”kina mgn da wani banza”kinbar marar aikinyi najiranki ko?”

nayi laifi yaya sadeeq kayi hak’uri dan Allah”murtala namasa mgn ne akan kazo?” yace” ah ah”shine kasamemu”

tana fad’in hakan ta fita sbd kukan dataji yataho mata”dr sadeeq kuwa har yanzun haushinta yakeji”

patient’s yacigaba da dubawa”kusan awa 1″da fitar Aysha amma bata dawo ba”

tashi tsaye yyi ya fito dg office d’in…..Aysha na zaune tayi tagumi ta zurfafa atunani ga kuka tanayi”

Ke! Lfy zakixo kina yiwa mutane kuka?”salon kuma ace namiki wani abun”kamar yadda ake cewa”

batare data kallesaba ta cire tagumin”Ahankali tace”.bbu komai” tab’e baki yayi ya wuce yana cewa idan kin gadama ki biyoni”

Anutse ta tashi tsaye ta bishi a office nashi”bayan tayi sallama ta shigo”zoki zauna anan”yafad’a yana nuna mata kujerar gefensa”

babu musu tazo ta zauna”meke damunki kiketa kuka?”k’asa tayi da kanta wasu hawayen nazuba”tanata murzar idanuwanta”

Banason kuka sholy”kiyimun shiru kisanarmun damuwarki kinjiko?”sosai tayi mamaki”sbd betaba mata mgn muryarsa ahaka ba.

Baffa ne!meya miki?”bansan wace irin shak’uwa kikayi da ammi da baby ba”duk sun damu yau basu ganki ba”jiya kuma kika gudu bbu ban kwana ko?

Bakai bane kaja natafi”nikuma sholy?”uhmm”yanzun fad’amun meyasaki kuka?”tunda dai yanzun mundena fad’a dake ko?”

baffane yaturo mun wani jiya,kuma ba mutumin kirki bane…..banfa ganeba ?kimun bayani”inaso idan bbu damuwa kisanarmun wani abu dg tarihinki sholy”meye dalilin yin aiki? kina d’aukar albashi”bayan kinada k’ananun shekaru??”

nidai sai kayita cemun yarinya ,ni bazan fad’a ba to”Amamakin ta sai taji yayi murmushi….saurin d’ago kanta tayi sbd ta tabbatar”suka had’a ido”yana kallon ta yace”.nadena cemiki yarinya”shikenan?”kinga duk kindame baby face naki da hawaye da kwalli ko?

K’asa tayi da kanta tak’i mgn”nafa dakatar da duba patients sbd naji meke damunki?”sai nacigaba da dubasu”

sosai taji zuciyarta ta mata sanyi”ko yaya ai yadamu da damuwarta”kamar yadda anty murja ke nuna damuwarta”zamanta ta gyara kanta ak’asa tashiga sanar masa tarihin rayuwarta”tun kafin rasuwar abbanta “har zuwa rasuwarsa”da abinda mijin anty murja yaso yamata,da abinda baffa idi keson d’ora ta ahanya tayi……da kuma abinda yafaru ayau da safe….

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un!kawai dr sadeeq ke maimaita wa aransa”yana share zufar data keto masa agoshi da handcheef”

wani irin tausayin Aysha yaji nabin ko ina na jikinsa”yanzun yarinya k’arama me irin wannan k’ananun shekarun ke fuskantar irin wannan k’uncin rayuwar”

wani irin mugun tsanar baffanta yaji”musammun daya fahimci Inda yadosa.yanaso ya wofin tar da rayuwarta”yaji kuma ta burgesa data kasance me tarbiyya da tsoron Allah”dukda ada yanata kallon marar tarbiyya”ashe ba haka bane.

Aysha kanta ak’asa tana kuka”kingama kuka sholy muddin kina tare dani insha Allah” kinjiko?”kinaso ki koma skul?”eh inaso yaya sadeeq”

saime kikeso?inaso nagano ummana “ko waya bamayi da ita”kinsan garin?”Eh”ai acan dangin abbanah suke”week end zamuje nakaiki kinjiko?”

Da sauri ta d’ago kanta tana murmushi cikin murna tace”.dan Allah da gske yaya sadeeq?”kansa kawai ya gyad’a mata”

kuma nidai yaya sadeeq banason zama agidan baffa idi”sai yayita turo mun maza”

Shine ai babbar matsalar”idan munje garin su umman naki zanyi magana da sauran baffan ninki”ko kuwa ni badamuwata bace nasaka hukuma ta kamashi”

dukda abinda yakeyi miki dole sai ansamu shaidu”ai duk mutan anguwar sun sani”ko gidansu yaya abdul sun….waye Abdul????”

🤣🤣 natafi yajin aiki serious saikun gyara ana comments saina dawo zangani awannan page d’in inkun gyara🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️

Mom fareesa🖊️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button