Ni da Dr. SadeeqNOVELS

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 35-36

🅿️35&36

……. murmushi ammi tayi tace”.tamun abinda bazan iya mantawa da itaba arayuwa ta sadeeq”nina sanarwa hindatu karta sanar dakai komai…..tashiga sanar masa irin kulawar da Aysha ta dinga bata”

ta d'ora da fad'in jiya da yau bata kamun rubutunba"wlh bakaji yadda nakejin bbu dad'i ba"Aysha yarinyace me ilmi sosai da sosai.....ajiyar zuciya yasaki"yana kallon ammi cike da mamaki "dukda yab'oye mamakin yace".banyi mamakiba sbd nasan tanada ilimin addini sosai"kuma karki manta ammi wannan mijin naki shine yanuna beson amiki maganin gargajiya"kika nuna kema bakyaso"dukda nima banaso"ashe anan sauk'in yake da izinin Allah"sbd haka bbu damuwa zanyiwa habib mgn"muje gun mlm muhammad"acigaba da miki rubutun kawai"magungunan da addu'oin zandinga miki da kaina kawai"

meyasa bazaka bari Aysha ta cigaba ba?”d’auke kansa yayi yace”.tunda nasani nima inason samun ladar ammi”sannan ni yanzun bbu ruwana da ita.

D’an murmushi ammi tayi tace”.meye tamaka?”yakamata kadena wannan zafin zuciyar naka sadeeq”Aysha yarinyace k’arama agunka”yaka mata kamata uzuri”ita kanta na lura tanada damuwa sosai”hakane ammi”amma ni bbu ruwana da ita”yaya kodai hardani nayi sanadiyar shi….kinsan Allah hindatu kika koma abinda kikayi d’azun”zan baki mamaki bbu ruwana da anmiki aure”belt zansamiki jikinki yagaya miki”yana fad’in hakan yatashi tsaye yabar parlourn”bebi takan hindatu dake bashi hak’uri ba”tana cewa yazo yayi lunch”

dariya ammi keyi sbd ta fassara dr sadeeq”tana kuma fatan Allah yasa abinda take zargi yatabbata”

parlourn sa dr sadeeq ya wuce”sosai yaji zuciyarsa tayi sanyi”sbd miskilanci irin nasa ko a fuska be nuna yaji dad’i ga abinda Aysha tayiwa ammin ba”amma aransa gaba d’aya kewarta yakeyi”yanajin Aysha tagama yimasa duk wata kyautatawa data kula da lafiyar mahaifiyarsa”dayafi so aduniya”

shiyasa akace mutum daraja gareshi”karka wulak’antashi”kowane nada tashi irin baiwar”yatabbatar Aysha Inda watace d’azun da gori zata masa akan ta kula da mahaifiyarsa”amma ko sau d’aya bata tab’a masa zancen ba”

duk jikinsa yyi sanyi”idan yatuna kalamanta na cewa har abada itada asibitin”da kuma baffanta zai daketa idan bata kawo masa kud’i ba”sai yaji fad’uwar gaba da tausayin ta”

sarai yasan Aysha nada tsoron duka"koshi idan yace".zai daketa tadinga bashi hak'uri kenan"gashi shi yanzun idan yaje gidansu da sunan gunta yazo ai saita rainashi"

damuwar da dr sadeeq yad’auka kad’an sai gashi tayi masa girma”ko lunch beyiba ayinin ranar”

Daya koma asibiti da marece ji yadingayi kamar zuwa zatayi office nashi”dayaji motsi sai yyi sauri yaduba yaga ko sholy ce…

da dare kuwa  coffee kawai yasha ya kwanta"gaba d'aya juyi dr sadeeq keyi asaman royar bed nasa"yana tuna ko d'azun dayashiga bed room d'in ammin yasamu mayafin Aysha hannun hindatu suna firan Aysha d'in da ammi"

gaba d’aya mamakin kansa yakeyi na nuna damuwa da yayi da ita”saiya alakanta abun da tausayine da kuma yaji dad’i data kula da amminsa.

Da wannan tunanin yyi bacci da nufin da safe yatura driver da hindatu su kirawo Aysha acewar ammi ta turo atafi da ita….

washe gari da safe dr sadeeq ko Shirin zuwa office beyiba"da jallabiya milk colour ajikinsa yayi gwanin ban sha'awa"

bejima da dawowa dg masjeed ba yashigo cikin gidan”kai tsaye kitchen ya wuce yasamu hindatu acan”

yaya ina kwana?”lafiya qlau”dan Allah kadena fushi dani kaji?”haba my sweet daddy nah”babban wa uba fa yaya sadeeq”kaine yanzun fa amatsayin daddy nah”

kin b’atamun rai baby ajiya”kuma itama sholy tak’aramun da wani nata”dg yanzun idan khaleefa yakoma miki zancenta kice masa kinsanar mata cewa yana sonta”ita kuma tace”.bata sonsa”kina jina?”

Dato hindatu ta amsa tana wani zato aranta”yanzun ki ajiye wannan aikin ki shirya” kuje da driver gidansu sholy”kinuna mata ammi ta turo ki kizo da ita anan ina jiranku”

Amma yay….banason musu kinsani?”30 minit nabaki”kibar masu aiki su Ida had’a break fast d’in mana”

Dato ta amsa”atare sukabar kitchen d’in”shi yakoma part nasa”yyinda hindatu taje ta shirya”

kasancewar dama mijinta ya amince taje duk Inda yadace”fitowa tayi ko ammi bata sanarmawa ba”tasami ilu driver suka wuce anguwar su Aysha……

      **********

Ab’angaren Aysha kuwa”sosai ranta yab’aci da abinda dr sadeeq yamata.tasha kuka bana wasa ba”ga zulumin takoma gidan su bbu kud’in da baffa yace”.tasa momishi”

Cike da tsoro da fargaba ta hau adaidai ta wuce gida”

K’in komawa gidan tayi ta shiga gidansu yaya abdul”kasancewar fatima k’anwarsa kawartace”acanma taci abincin rana”sai gab da magrib tashigo gidansu”sbd tasan baffa be kwana gida.

Suleman ne kawai agidan”fiddausi ,da goggo sa’a basu nan”

wanka tayi ta canza kaya tayi zamanta”saidai gaba d’aya zuciyarta bbu dad’i”acikin 2 days d’in nan, d’an shirin dasukeyi da dr sadeeq sai taji ta shak’u dashi”bataji dad’in abinda yahad’asu ba”amma yadda taji zafin abin”tana ganin ita dashi har abada”

 sai dare mutan gidan suka dawo"atime d'in Aysha tamayi bacci"

Tun 6:am kafin kowa yatashi Aysha tayi wanka”ta shirya cikin milk d’in material d’inkin bubu”tasaka hijab d’an katsina milk colour”tasaka plate shoes “ta d’auki hand bag nata “taje ta bud’e gidan gurin 6:30 am”sbd tasan gurin 7:am baffa yake dawowa…..

Koda ta fito tunani takeyi inama zataje?”gashi islamiya yau saida 4 zataje”skul kuma bata zuwa sbd rashin kud’i”ko yanzun500 kad’ai ta mallaka aduniya”

wata zuciyar nasanar mata taje gidan ammi kawai….to kuma idan taje ai har yanzun dai tana tare da dr sadeeq”

kuka tafashe dashi”in bacin tasan 500 bata isarta zuwa batsari ta tatafi kawai”tagaji da irin wannan rayuwar k’uncin datakeyi”karma aganta awaje irin wannan time d’in Ayi zaton koba gida ta kwana ba.

soron gidansu yaya Abdul tashiga ta zauna tana latsa wayarta”sbd rashin mafita”kusan zaman 40 minit tayi wayarta tayi ringing”

Atime d’in kuma 7:25 am”kamar karta d’aga sbd ganin hindatu ce”

D’agawa tayi “Ahankali tayi sallama”hindatu ta amsa da cewa”sholy kintashi lafiya?gabanta yafad’i sbd ta tuna dr sadeeq kawai ke kiranta da sunan”lafiya qlau anty hindatu”gamunan alayinku ammi ta aikoni agunki”

gaban Aysha taji yafad’i tayi shiru batace komaiba”kina jina sholy?”uhmm”kawai tafad’a”kizo gamunan zamuyi parking”

to yaya ammin tace”.anty?”murmushi hindatu tayi tace”.jiya bakizo ba duk mundamu”shine mukazo mu d’auke ki”

shikenan bara na fito nasameku”amma dai yaya sadeeq baya nan ko?”meyasa kika tambaya?”turo baki tayi tace”.ai ni bbu ruwana dashi”

Hindatu na dariya tace”.karki damu yatafi office ai”dato ta amsa tana kashe wayar” ta mik’e tsaye dg zaunan datake kan takalmi”

tana k’ok’arin fita dg soron yaya abdul kuma yafito dg cikin k’ofar dazata sadaka da tsakar gidan su”

Aysha!cak ta tsaya”juyowa tayi suka had’a ido”k’asa tayi da kanta tace”.ina kwana?”lafiya qlau ina zakije?”

gun aiki”wai idan kinfita da safe ina kike zuwa??”inaso namiki wasu tambayoyi Aysha”amma banaso kimusu wata fahimta daban”

Ana jirana waje pls”idan munsake had’uwa kamun “insha Allah idan na sani zan baka amsa”bata jira cewar saba ta fice dg soron”

Tunda ta fito ta hango ilu driver agaban motar”hakan yasa ta nufi motar”hindatu ta bud’e back sit Inda take zaune”Aysha ta tsaya dg waje”meyasa bazaki shigo cikin gidanmu ba?”bbu komai sholy”nibana son wannan sunan?”tayi y’ar dariya tace”.meyasa to?”ba yayanki yasamun ba”kuma ni bbu ruwana dashi”

Kice fad’a kukayi dashi kenan?”shiru tayi tak’i mgn”yanzun kizo muje ko?”amma bazan jimaba”kuma dan Allah karki sanar masa nazo”

Karki damu shigo muje”batace komaiba ta shiga motar”suna fira sama sama har suka iso gidan”

Atare suka fito dg cikin motar suka wuce ciki”

Dr sadeeq daya kasa zaune da tsaye tun bayan tafiyar hindatu” yana jin horn d’in mota”yabud’e window”yana ganin sune yasaki ajiyar zuciya yafito dg shashen sa da sauri….

sbd ko shiryawa beyiba”jallabiyar d’azun ce ajikinsa”kasancewar sauri yyi”tak’in mace dana namiji ba d’aya ba”

daidai bakin k’ofar shiga main parlour dr sadeeq yatsaya”suna turo k’ofar hindatu taganshi tsaye”kasancewar itace agaba”

murmushi kawai tayi…..Aysha najin k’amshin turarensa tayi baya da sauri”kawai taganshi agabanta”
da sauri ta juya zata koma”yyi saurin rik’e gefen hijab nata yana kallonta.

Hindatu tayi dariya ta wuce ciki”juyowa Aysha tayi afusace tasaka hannunta da nufin ta k’wace hijab nata daya rik’e”takuma k’i mgn balle ta kallesa”sai jan hijab nata takeyi”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button