UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 71 to 80

NURU dake tsayi tajisa tsayuwarsa a bayanta ta ta rufe idanuwa mararta na sake murdawa ta bude idanuwanta batareda ta juyowa taji takunsa ya tsaya gefenta tareda kallonta kafin ya juya ya kalli afia data sake Shiga rudu da firgici ta matso qafafunta na rawa ta bude Baki zatai magana ya dakatar da ita da idanuwansa dasuka sake gigita kowa agurin suka sake sauke kawuna suna tsuma.

Inda lailah ke tsaye Bai kallaba sbd har lokacin bayajin tasamu darajar samun lokacinsa ya waiwayo ahankali ya kalli gefen Mr Omar batareda yayi magana Mr Omar ya matso da sauri Yana kallonsu mum Sarah kafin ya juya ya kalli lailah cikin ‘yat girmamawa ya tausasa murya yace”

Ranki ya dade ko zamuje na maidaki gidanki.

Wani wulaqantaccen kallo tayiwa Mr Omar din zuciyarta na tafasa da cin fuskar da akeson yimata gaban ‘yan aikin gidan ta maida kallonta kan MALEEK zatayi magana ya wuce Yana barin gurin hannun NURU cikin nasa

 zuciya ta taciyota tasha gabansa cikin baqin ciki da bacin Rai me qarfi tace”

MALEEK agabanka bawanka yake wulaqatani 

Harni zaicewa nafito yakaini gida

Wannan tsaban wulaqanci ne gareni bazan daukaba wlh…..

Dakatawa yayi tareda juyowa akaro na farko ya kalleta tun bayan rabuwarsu ya zuba Mata idanuwansa dasuka so rudata daga masifar datake ya bude Baki ahankali yace”

Zakibar gidan Nan yanzu bada Bata lokaciba idan ba akan umarnina Mr Omar yafada hakan Dan Haka kin tabbatar kafin kisan matsayinki agaban masu aiki da ‘yayanki respect yourself and just leave.

Waiwayawa yayi gefen afia data shanye jinin jikinta yace”

Mahaifiyarki har abada bazata taba sake zama Matar mahaifinkiba 

Next time dazan sake fada Miki hakan ki tabbatarda bazakiyi awa goma agidana ba zan aurawa mr Omar ke

Now I gv you 10 min ki tayata kwashe kayanta.

Wucewa yayi yabarsu kowa ya sake dauke wuta musamman afia da lailah datai mutuwar tsaye idanuwanta nayin jajir zuciyarta na kasa gasgata abinda kunnuwanta suka ji..

A haukace tasake Shan gabansa da sauri tana yaqi da hawayen dakeson sauko Mata sbd taurin zuciyarta dake tarwatsewa a haukace tace”

Maleek wlh tallahi ban yardaba bazan bar gidan Nan har abada saidai ka kasheni ka fitarda gawata idan ka…..

Dan motsowa Mr Omar yayi cikin rashin Jin Dadin abindake faruwa gaban dukkanin Yan aikin gidan ba girman maleek bane Dan Haka yana matsowa maleek yayi masa kallo daya ya dakata Yana sauke Kai.

Kai tsaye Maleek ya watsa Mata wani kallo zuwa lokacin bacin ransa yagama bayyana afili sbd yanda idanuwansa suka sauya ya kalleta Yana controlling tsananin bacin ransa yace”

Afia I said I gv you 10 min to help your mother pack and leave.

Wani gigitaccen kuka ya kufcewa afia dukkanin hankalinta na sake tashi da tsananin bacin Rai data hangowa acikin idanuwan mahaifinta.

Lailah ta fizgo afia data Kama hanyar dakinta hado Mata kayanta ta sharara Mata marin data rAsa wazata saukewashi cikin tsananin tashin hankali,baqin ciki da masifa tace”

Babu inda zantafi maleek idan akan wannan trash din sa’ar ‘yarka kake cewa nabar gidan Nan Babu inda zanje zanyi zaman ‘yayana…

Kallonta dukkaninsu ‘yan aikin sukayi cikeda mamaki da kunyar abinda take yiwa kanta suka sauke Kai bame ikon mgn 

Maleek kuwa ahankali ya juyo ya kalli NURU da duk jikinta yagama mutuwa da ciwon dake damunta Dan ita yanzu Bata mamakin duk abinda Lailah zatayi shiyasa ko Kai Bata dagoba ta kalleta duk abindake faruwa.

Dagowa tayi ta kalli MALEEK dake kallonta da cikin wani yanayi ta dago ahankali ta kallesa ya kalli cikin tsakiyar idanuwanta Kai tsaye ya bude Baki yace”

Kina buqatan wani Abu anan din?

Kallonsa takeyi cikin idanuwansa abinda Babu Wanda ya Isa yayi hakan a gidan.

Bata dauke idonta akansaba ta girgiza kai alamar Babu.

Juyawa yayi Kai tsaye da ita ya nufa dakin farhat har lokacin hannunta na cikin nasa.

Mr Omar ya juyo yayiwa masu aikin kallo daya take suka watse

Ya waiwayo ya kalli mum Sarah dake riqeda farhat daketa kuka ahankali sbd tashin hankalin tsoron data shiga ya gyara tsayuwa Kai tsaye yace”

Ms Sarah abawa kowa order suyi packing na kayan sawa kawai kowa zai bar gidan yau.” Yana fadar hakan ya juya ya fice ya nufi mota Yana jiran fitowar maleek da nuru.

Suna Shiga dakin farhat ya saki hannunta ya janyo rigar abayarta dake kan gado ya miqa Mata ta karba jikinta ba karfi ta Sanya ta ya sake kamo hannunta suka fito ta gaban lailah da afia suka wuce 

Farhat dake hannun mum Sarah ta kwace tabiyosu da gudu ta riqe hannun NURU wadda ta tsaya sai alokacin idanuwanta suka fara kokarin cikowa da hawaye ta kalli farhat din tana sake qanqameta ta dago ta kallesa ya kalli hawayen dake kokarin sauko Mata yace”

Zakije da ita?

Gyada Masa Kai tayi da sauri 

Ya kamo hannun farhat din da hannunsa daya suka fice

Suna fitowa Mr Omar ya budewa NURU kofa tafara shiga kafin MALEEK ya zagaya mr Omar din ya bude Masa shima yashiga ya rufe kafin ya kamata hannun farhat ya bude gaba ya sakata ya zagaya ya shiga motar yaja suka bar gidan.

Lailah datayi mutuwar tsaye hannu take neman dorawa akai Amma kunyar ‘yartama data masu aikin ta hanata kurma ihu ta zame kan kujera tana kokarin shanye hawayen dake ciko Mata idanuwa su koma.

Afia kuwa kuka tasake wiwiwi me qarfi tareda zubewa qasa Dan kuwa mum dinta tagama da rayuwarta Kamar yanda tagama da tata Dan kuwa tafi kowa sanin halin dad dinta musamman yau da zallar bacin ransa ya fito danma agaban masu aikine yasa ya Hana fushinsa bayyanuwa.

Mum Sarah na ganin hakan ta juya da sauri tayi ciki ta Isa part din masu aiki tace kowa ya shirya kayansa yanzu yanzu za’a kwashesu zasu bar gidan zuwa sabon gidan NURU.

Da sauri suka mimmiqe suka hau hada ‘yan kayansu na sawa

Mum Sarah din tafito ta nufi harabar gidan ta sanarda securities saqon Mr Omar daga maleek take suma suka tashi dama Babu me wani kayan shirgi komai na gidan a tsari yake har masu Aiki da masu tsaro.

Tana Gama sanarwa kowa ta nufa nata dakin ta jera kayanta cikin akwati tsaf ta fito ta nufa dakinsu farhat ta hadawa NURU da farhat kayan buqatansu cikin Yar karamar akwatin farhat din sai schoolbag din farhat Amma bataga kayan NURU ba dayake suna dakin afia sai Bata daukar Mata kayaba ta fito dasu takai dakinta daganan Babu Wanda yasake fitowa sbd tashin hankalin da masifar dasuka gani tsagwaro atareda lailah.

##MAMUH#

****************

Suna fitowa Kai tsaye wani qaramin underground gidansa dake cikin anguwar suka nufa Wanda keda 2 bedrooms rak da manyan Palo guda biyu sai kitchen me hade da dining acikinsa komai na gidan is milk Mr Omar ne kawai yasanda gidan Babu Wanda yasan gidan nasane Haka gidan komai a kip kip yake anan yake wasu private wayoyinsa da ayyukansa hakama wata maganar me buqatan tsananin sirri anan suke zuwa suyita da Mr Omar.

Parking Mr Omar yayi yafito ya budewa MALEEK yafito kafin yabudewa NURU ita saiya zagaya ya budewa farhat tareda kamo hannunta suka biyo bayan maleek dake gaba tareda NURU dake tafiya ahankali sbd ciwon Mara.

Suna shiga palon NURU ta dago ta kalli koina cikin palon cikeda mamakin tsaruwar gidan da cikin yafi wajenma kyau sosai saidai sbd yanayinta bazata iya qarewa koina kalloba a matse take data samu guri ta kwanta Tasha ruwan zafi masu zafi Sosai ko zata Dan fada Mata tasamu period din ya sauko wahalar ta rage Mata.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button