FITAR RANA

FITAR RANA 3

wajejen bayan magrib suka iso cikin garin kaduna lkcin kowa ya gaji acikinsu wasime kam tanata sharban baccin ta batama san ina suka dosa ba.A kofar gate din babban gidan qasimu sukayi horn gidane mai kyau dan madaidaici nan da nan mai gadinsu malam musa ya taho da gudu ya bude musu ƙofar gate tunda sukayi parking taheer ya sabule jikinshi ya shige can cikin dakinshi daganan kuma babu abunda ya kuma sauƙowa dashi.yana shiga dakinsan ya fada akan gadonsa mai laushi shimfide da shuɗiyar zanin gado ahnkli yake mirgina yana maida gajiyayyen numfashi dayake fitowa daga can ƙasar kirjinshi.
zuciyarsa sai bugawa sukeyi atare duk yabi ya rasa kwakkwaran dalilin faruwar haka.
Ya lura a duk yadda yaso ya mance da zancen auren nan a zcyarsa sai yaga ya kasa,ynzu shknan fa yay aure..

kwantaccen gashin kanshi da yay ɓaki yay lufff ya shafa ahankli cikin jan numfashi mai nauyi ya furta…”what the fuck is happening” ta ƙasar maƙoshin sa,wani irin mixed feelings na i cant believe this shi ya mamayeshi yanasa shi jin wata malalaciyar nakaso a dukkanin gabobin jikinshi.
Sosai Ya takune Jan fuskarshi wanda yy kama da kamar zai yi murmushi kamar kuma zaiyi kuka a lokaci guda.

daga nan miƙewa yay gaban wani dan mini freezer ya buɗe ciki ya leka yakai Minti biyu a tsaye a wajen 2 rows ne mai dauƙe da chilled bootle water sai bootle din chapman ansha rabi an bar saura aciki.Ruwan kawai yasaka hannunsa ya dauƙa ya bude goran snn ya kurɓa kadan yanamai lumshe idanunshi jin yadda sanyin ruwan yakebin jikinshi yana sanyayashi after each sip saiya sauƙe ajiyar zuciya sanda yasha iya isarsa snn ya mayar da gorar ya ajiye ya mike ya shige bathrum,acikin dakikan mintina yy wanka yabiya sallolin dake kanshi,tuna wayarsa a kashe yasashi kunnata.,dan kadan yay scrolling da baiga wani abu intresting ba ya ƙara kashewa ya jefar,da kyar yau ya samu yay bacci dan aranshi babu abunda yakeyi face juye juye da tunanin auren da aka dora masa ayau.

A bangaren wasime kuwa saiyau taga babban gida ƙere tunaninta,yo duk kauyensu bataga i irinsa ba,da xuciyarta kawai taketa shagalin hira tana maganganu kai kace nazarin wani abu muhimmi takeyi ,gidane irin na zamani yasha interlocks ga motoci a parke 1,2,3 saida ta tsaya kirgawa tass acikin zuciyarta,motoci guda uku ne harda wanda sukazo aciki making 4 cars,sai kuma jincheng rubber rubber da tagani agefe.,baki bude tace”laaah gidanma harda Achaba? Bakinta ta washe a tunaninta ai zatana xuwa gida tunda a machine kawai taga ake shiga kauyensu data fito,…sai kalle kalle kawai take abunta tana leken wajajen da suka burgeta kamar wawiya,da alama tamance wai yau an dora mata wani abu akanta waishi aure inza a yankata aynxu ma bazata iya tuna afkuwar komi ba .

karshe babban mai aiki kuma nannyn gidan wanda suke ambata da suna Bilti ita ta riƙo hannunta tajata izuwa ciki tayi mata wanka fesss ta shafa mata mai tasa kaya nan danan bacci mai nauyi ya saceta danko abinci bata iyaci ba,washe gari da asubahin fari taheer ya farka ya fice sallahr fajr shikadai danyau bai jin zai iya jiran dad dinsa kamar yadda ya saba dan harynzu basuyi wani dogon hira akan lamarin aurensan ba,kuma yasan da maganganu sosai a bakin mahaifin nasa,shidai baison yay tattaunawa maizurfi, he dont really care inde hakan zabinsu ne shimai musu biyayya ne ako wani irin hali so long as dis marriage bazai hanasa cika burikansa na rayuwa ba.guntun ajiyar zciya ya sauke ayayin dayake sauƙa ahankli daga kan matakala,jallabiya brown ce ajikinshi tasha karin guga ta masa damas ,a hnkli yake takawa alaman baison kowa yaji motsin fitarsa daga gidan,tunda yy alwala ya zauna cikin masallaci bai ƙara fitowa ba,yau sai wajajen bakwai saura ya dawo cikin gidan sallama yy a kofar falonsu,
Abbansa na zaune da jarida a hannu ya amsa,waje ya nema ya zauna a kasa sai ynxu ya lurada innono data fito ta shirya tsafff tana zaune a falon itama tana kallon tv tare da mahaifinsan bazaiwuce suna tattaunawa akan lamarin aurensa ba,wani haɗe ransa yay tamau kmar bai taɓa dariya arayuwarsa ba,mentally ya datse zcyrsa daga bugun datake snn ya dan cixa labbansa a asirce,idanunshi yay rolling snn yy ƙasa dasu a miskilance “Anono kintashi lpya? Da sauri ta amsa shi…lpya lau dahiru Angon jiya har anhito kenan,ajiyar zciya ya sauƙe irinta cikin wuyar nan baice uffan ba
Tahau bada labarin shagalin jiya,da yadda aka tara musu kudi wajen gasar rawan ango da amarya da akayi,amarya ta samu dubu uku cas cas ango ya same dubu biyu da dari biyar,tace Sai dai fa kuyi hkri dashi na sallame yan biki kunsan abun bawai na shirya masa bane,alhj Qasimu yanata murmushi uffan taher baice ba,shikansa yasan jin sallamar san yasata ƙara himman maimaita maganar da sukeyi na batun auren na sa,hirarsa ma a sama sama takomo amsawa tana jaddada masa cewa tabar musu yarinya marainiyan Allah
.tace”nide ba zama zanyi anan ba saiku riƙeta amana inmakun zalunceta Allah na kallonku, nide zan tafi tasha can anjima motar shayibu zaibiyo tashar sai kacewa danka daheru ya ajeni can.,alhj qasimu dake satar kallon dan nasa yaga ya sunkuyar da kansa can ƙasa ya bata shiru,yace babu damuwa mama ai gashi nan yanajinki,”my son kanajinta ko?kau da kai
Taher yy baice uffan ba ya gyara zamansa, suna cikin tattauna haka saiga shigowar matar gidan hannunta dauƙe da flask din ruwan zafi da wainar kwai da kayan karyawa
…ferfesun kan ragone cikin cooler da kayan tande tande an naɗe shi a babban leda wanda innono xata wuce da shi sabida yunwa dan sukansu basu san inata dosa ba zama innono tayi ta ƙarya sann
Ta sassaka musu albarka,tare da zuriarsu.

Ƙarfe Takwas saura wasimé ta farka bacci hannunta bisa baka tana kkrin tare wagegen Hamma daya taso mata hartakai hannunta baki saikuma ta firgita ta sauƙe tahau tattaba jikinta jin duk ta jiƙe da fitsarin datayi a kwance,subuhanalillah!!
da mugun gudu ta sauƙa akan gadon ta riƙe kirjinta dake bugawa da karfi fuskanta tamkar zatay kuka ta doƙa salati” innallahi wa inna ilaihi rajiun na Higa uku !!fitsari nayi,ta tattaba gadon sann ta tattaba jikinta”ayyy ashe fitsari nayi..yau na higga uku,a hargitse ta juyo cikin magagin bacci Da muryan tsoro tana neman innononta.innono
Ano..Cin karo da idon mutum akanta yasata yin tsit ta koma baya a tsomare kamar wata barauniya,”wata mata tagani agabanta sanye da riga da zani da wani baƙin hijabi,gashi Allah ya xuba mata ruwan ciki gaba daya sai taji hanjinta na curewa tsabar tsoro,suna hade ido taji gabanta ya fadi rass duk sai taji ta rude,duk damuwarta fitsarin datayi musu akan’ gadonsu tanayi tana waiwayen wajen,wayyo Allah rabonta datay fitsarin kwance fa yau yakai shekara guda kenan amma meyasa yau taga tayi kuma a gidan mutane?sai satar kallon jikakken gadon take da gefen idanunta da suka firfito tanayi tana damƙe zaninta da hannunta dake karkarwa, kiris ya rage Bilti ta fashe da dariyar yanayinta dan sosai ta bata dariya.

Cikin gyaran murya tace yan mata harkin farka?..zatayi magana bilti ta katse ta cikin sauri “natasheki kiyi sallah kince min toh ko harkinyi sallahn kenan?kanta ta sauƙar ƙasa kirjinta na bugawa fat fat,ta rasa mema zatace daga nan wani shirune ya dauƙe Wajen,murmushi kawai bilti tay snn tajanye hannun ta tay da ita bathrum,”Cire kayanki, ta umarceta sannan ta soma hada ruwan wanka mai dumi a bath,da kyar wasime ta kammala cire kayan nata ta tsaya daga ita sai pants,duk ta kame jikinta waje guda sabida tsoro da kunya jikinta duk rawa yake,haka ta dunkula kayantan a hankli ta ajesu kusa da wani empty bucket tana ta kallan inda tajikasu da fitsarin cikin nisan tunani,”Uuhum uhnmmm
Gyaran muryan matan ya ƙara firgitata ta dago kanta a firgice tace naam ‘brush ta gani a hannun matar sabo dal a ledansa aka budesa,a hnkli tace,”xo nan kiyi maza ki goge bakinki saimu tafiko?tune din lallami datasa yasaka wasime gyada kanta batare da tay niyya ba, Ƙarasowa tayi kamar mai tsoron wani abu ta tsaya agefenta,Sink bilti ta kunna ta mika mata brush din tana kallonta harta kammala yi dakanta,She was bit relieve dataga ta iya batayi wani kuskure ba,bayan nan tayi mata wanka suka jajjaba alwala,.dan karamin towl ta dora mata sann ta jawota dakin ta koma ciki after like 5mint ta dawo ta sameta a inda ta barta tana tsaye,Batace mata uffan ba ta kalli gaban madubi “mikomin vasaline”babu musu maza taje ta dauko ta kawo,tana ajewa bilti ta dan jawota kusa snn ta soma tsantsane mata jiki ahankli snn ta shafa mata mai ta mulƙe ta tass ta gyarata..ganin ta runtse idanunta tana kakkame jikinta yasata sakin numfashi ta kyaleta mamaki da fargaba duk ya cika kirjin wasime,a nutse bilti ta kammala mata komi ya rage saura saka ƙaya saiga sallamar innono ta fado dakin fusknta murtuke,tsaye bilti ta miƙe da dan fara a a fuskanta tace “Kaka karde har an fito,kiyi hkri saura kiris inkammala shiryata,ganin wasime fess fesss yasa innono sakin fuska tana washe baki..”lahhh baiwar Allah harkunyi wanka.. kai sannunki da aiki,karki damu wallh dama ainice mai tafiyar ita kuma wasimé inazata ai tazo gidanta kenan, nima zuwa nay nan indan jira anan,ina ni ina kallon kayan takaici,mtsew Allah yabaka jika mai shegen mulki,”.kinga na shirya zan tafi dayakaini tasha in samu shayibu shine wai saina jirashi yay wanka kuma fa fess jikinshi yake,aikoda na shunshuna dandamalin rigarsa da zai wuceni harwani qamshin inibi yakey,yo saide in hammatar sa ne bai wankeba,kenifa na lura dahiru fa dan walakanci ne dama shide akomi sai anjirashi..neman yayi’ mun kora da haline kawai
A gidan nan..nide ina ƙara baku amanar ƴata yannan kusamin ido sosai akansa karyaga kamar sadaqa aka basa ya wofantar da ita da jan fuskarsa awajen fatashhh kamar anja baya an kalli agogo..

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button