NOOR AL HAYAT 71-80

ki san wacece ita ba, it’s not even possible, Ni kuma yanxu idan na gaya maki kika fada masa he will suspect ni na gaya maki don duk abokansa babu wanda
yasan ta sai ni….” Jiddah tace “Haba Doctor, shi kansa yasan ai alkawari yayi baxai saba ba, Ni dai fa damuwata mota, don Allah ka gaya min ai bai san ina
da number ka ba he won’t suspect anything” Yusuf yyi murmushi yace “Toh xan gaya maki indai sabuwar mota kike ma” ta baxa kunne tace “Yauwa nagode sosai Dr”
nan Dr Yusuf ya fara bata labarin Khadijah tiryan tiryan babu abinda ya boye a duk labarin har ranan da Mami ta rabasu na karshe. Gaba daya xufa ya dinga
karyo ma Jiddah taji cikinta ya hautsine, Jin Yusuf yace “Hello” cike da karfin hali tayi dariya tace “Ikon Allah, Allah sarki, to nagode Dr Allah saka da
alkhairi Allah ya barka da Amina, sabuwar mota kam dole a ban” daga haka tayi masa sallama ta katse wayar dai dai lkcn da aka bude kofar dakin kafin ya kai
ga shigowa tayi saurin boye wayar hannunta, ya shigo yana kallonta yace “Files da na bari kan dinning kafin nayi tafiya, Ina kika ajiye min?”
✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Shiru Jiddah tayi ta tallabi chin dinta tana kallonsa lkci daya kuma tana murmushi, Sudais ya hade rai yace “Magana fa nake maki jiddah?” Ta tabe baki tace
“Amira na ba ta kai maka daki, kaje ka tambaye ta” wani kallo ya dinga mata yace “Amirar xaki ba files jiddah?” Cikin halin ko in kula tace “Ita, ko bata
isa aike bane, Beside if they are that important ai baxa ka bar su yashe a dinning area ba” Girgixa kai yyi ya juya ya fice daga dakin, tayi wani murmushi
mai sauti tana girgixa kafarta, lkci daya murmushin yayi fading a fuskarta, da ajinsa, da kyansa, da iliminsa da kudinsa duk fadin duniyar nan ya rasa warce
xai kawo mata matsayin kishiya sai warce ta taba cikin shege ta haife yaran… Wani dariya ta kwashe har da kyakyatawa ta mike tana wani murmushi tace
“Abomination” daga haka ta fice daga dakin, sai dai fa jin ranta take fess. Har khadijah ta fara bacci Shureim ya shigo dakin, ta dinga kallonsa har ya iso
inda take yace “Anty cire min uniform” mikewa xaune tayi ta shiga cire masa uniform din jikinsa tace “Have u eaten?” Ya gyada kai yace “Uncle ya bani
cornflakes” Khadijah na kallonsa tace “Are you okay with it?” Ya wara ido yace “Ehh Anty, ai da yawa ya bani, shi kuma ya sha tea” Khadijah bata ce komai ba
ta dinga laluba aljihun wandon sa jin akwai abu a ciki ta fiddo Chocolate tana kallonsa tace “Wa ya baka?” ya karba da sauri yace “Aunt din nan ce ta bani,
tace min xata siya min puzzles amma bata siya ba she is sick, she is even sleeping at the room” Khadijah ta ajiye kayan bata ce komai ba, ya kamo hannunta
yace “Anty will you go and check her?” Wani kallo ta dinga masa strictly tace “If I should slap you….” A hankali ya koma baya yace “Anty kiyi hakuri” tana
hararansa ta nuna masa bayi tace “Wuce kayi alwala” ba musu ya wuce da sauri, ta mike don fiddo masa kayan da xai sa, magungunan sa da khaleel ya siyo masa
daxu da safe ta basa sannan ta ce yaje parlor yayi assignment dinsa, ta hada socks dinsa xata shiga bayi ta wanke wayarta yayi ring ta dawo tana kallon
wayar taga Barrister ke kiranta, ta karasa ta dau wayar ta xauna gefen gado sannan tayi pick din call din ta kai kunne, a hankali yace “Am sorry you called
bana kusa Amira” tace “Ba komai, ka isa lafiya?” Yace “Lafiya Alhmdllh dear” tace “Ya Amira fah?” Yace “She’s fine, how about my son” tace “Yana assignment”
yace “Ohk ba shi mu gaisa” mikewa tayi ta fita parlor ta ba Shureim wayar tace “Abba yana son maka magana” ya karbi wayar yana kallonta yace “Anty waye
Abba?” Harara ta watsa masa tace “C’mon answer ur call…” ya kai kunne a hankali yayi sallama, Barrister dake jin su yayi murmushi yace “How you boy?” Yace
“Am fine Abba” Barrister yace “Ka je schl yau?” Ya gyada kai yace “Ehh na je” yace “Good, always aim good grades sai in siya maka Bicycle” ya wara ido yace
“My two uncles sun ce xa su siya min bicycle, kaga am having three now, sai in ajiye ma Sudais daya, in ba su fadeel daya, Ni kuma…” Khadijah ta kwace
wayar hannunsa ta koma daki, ta kai kunne a hankali tace “You need rest barrister, ya kamata ka huta, hope ka ci abinci?” Yace “Me yasa kika amshe wayar?”
Tace “He is talking off hook” yace “Baki son dai in san two uncles din nasa” ta wara ido tace “Aliyu da Dr Ayman yake referring as two uncles fah?”
Barrister yayi murmushi yace “Alryt then” ta langwabar da kai tace “Toh ka ci abinci?” Yace “Eh yanxu xan ci” tace “Toh shkkn, kaje ka ci, a shafa min kan
Namecy na” yace “Ohk, will do that in sha Allah, thanks love” daga haka ya katse wayar, tayi murmushi ta ajiye ta kwashi socks din Shureim ta shiga bayi don
wanke su. Washegari gaba daya bata da lectures ranan, da wuri ta shirya Shureim ta tafi kai sa makaranta don bata son khaleel ya xo yace xai kai sa, tana
dawowa ta rufe kofar ta ta wuce bedroom ta kwanta, sai kusan sha daya ta tashi daga baccin da tayi, yunwan da take ji yasa ta wuce kitchen don neman abinda
xata ci, ta kunna gas ta daura ruwa ta dauko indomie da kwai taji kamar motsi a baya, ta isa gun window ta tsaya kafin ta leka a hankali, tsaye ta ga
Jawahir… khaleel na bayanta ya rungumota fuskarsa dai dai nata, yana d’aga karamin weight da hannu daya, Khadijah ta sauke idonta a hankali ta juya ta bar
wajen, kashe gas din tayi ta fice kitchen din gaba daya ta wuce daki ta kulle ta fada kan gado. Ta fi awa uku a haka, har lkcn sllh yayi ta kasa tashi, cike
da karfin hali ta mike daga karshe tana runtse ido ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta sa hijab ta dau karamar jakarta da waya
ta fita, tana kokarin rufe apartment dinta Khaleel ya fito, bata kalli inda yake ba ta gama rufewa ta juya xata wuce yana kallonta yace “What’s wrong with
you Khadijah, are u sick….” da kyar tace “No, i am okay” daga haka ta wuce waje ya bi ta da kallo, cab ta tsayar a waje ta shiga, kawai gani tayi ya ajiye
ta schl, ita dai bata san ya aka yi ta ce masa can xata ba, ta fito ta basa kudinsa ta wuce ciki, cafteria ta nufa direct tana shiga ta xauna ta hade kai da
table jin numfashinta na sama, ba a dau lkci ba Maryam ta shigo cafterian da frnds dinta xa su ci abinci, tana ganin Khadijah ta gane ta duk da kanta a kife
yake har lkcn, ta isa kusa da ita tace “Hi Khadijah are u okay?” Da kyar Khadijah ta dago kanta, Maryam ta dinga kallonta ganin yanda idonta ya kada tace
“Subhanallah baki da lafiya ne?” Kasa bata amsa Khadijah tayi, kana ganinta kasan she is in pain, Maryam ta fiddo wayarta a jaka da sauri ta shiga kiran
Aliyu sanin yana within area din makarantar, Yana dauka tace “Ya Aliyu kana kusa ne plss, yanxu na shigo cafteria naga Khadijah kamar bata da lafiya, and
she is not even responding, ko xaka taho yanxu plss….” Bata gama maganar ba Aliyu ya katse wayar, ta ja kujera ta xauna kusa da Khadijah tana kallonta da
damuwa tace “Sannu Khadijah” frnds dinta turawa sai sannun suke mata su ma, Aliyu ne ya shigo cafterian ya karaso kusa da ita da sauri yana kallonta yace
“Iman…. what’s wrong, are you okay?” Tun Khadijah ma ganinsa bibbiyu a gabanta har daga karshe ta daina ganinsa kwata kwata, Bata sake bude ido ba Kuma