NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 71-80

sai can kusan magrib ta ganta kwance kan gadon asibiti, dafe kirjinta tayi ta dinga bin dakin da kallo, a hankali idonta ya sauka kan Aliyu dake xaune kusa 

da ita ya jinginar kansa da kujerar da yake kai idonsa a lumshe, kokarin tashi ta shiga yi hakan ya sa shi bude ido, da sauri ya mike ya dawo kusa da ita da 

damuwa yace “Stay still Iman kinga ruwa ne a hannun ki, how are you feeling now?” ta kalli drip din hannunta har sannan tana rike da kirjinta da kyar tace 

“It’s hurting me” yayi kasa da murya yace “Kiyi hakuri xai daina Iman you are still under medication, koma ki kwanta plss” taki kwanciya ta hade kai da 

gadon, hawaye ne ya shiga sakko mata, a hankali yace “Iman?” Ta ki dagowa, hakan yasa ya tsaya yana kallonta cike da tausayi, cike da karfin hali ya ji tace 

“What about shureim….” Yana kallonta murya can kasa yace “I went to pick him in the evening na tarar neighbor din ki ya je ya dauke sa” Bata ce komai ba 

kuma bata dago ba yace “Let me call a nurse… Ina xuwa” daga haka ya fita dakin, ita dai har sannan bata dago ba hawaye kawai take kamar an bude tap, tare 

da wata baturiyar nurse ya dawo, ta duddubata ta fita, a hankali Aliyu yace “Iman kukan me kike plss?” ta kallesa hawaye na ci gaba da sakko mata ta kasa 

cewa komai, rikicewa yayi ya dawo kusa da ita sosai, yace “Don Allah Iman tell me whats wrong, me ya faru, me ne ke damun ki? Ur Bp isn’t encouraging, ur 

condition don’t need this, Tell me what ur problem is Plsss, ko an maki wani abu ne” ta goge idonta a hankali bata ce komai ba, Bude kofar ward din aka yi 

Maryam ta shigo tare da mum dinta, Hajiya Mariya ta karaso da damuwa tace “Sannu Khadijah, ya jikin naki yanxu?” a hankali cikin sanyi tace “Da sauki Mumy, 

Ina yini” Hajiya Mariya tace “Lafiya lau, Ina Shureim din” Aliyu yace “Neighbor dinta ya dauke sa schl daxu” Maryam ta ajiye basket din abincin hannunta 

tana kallonta tace “Allah ya sauwake murya can kasa Khadijah tace “Nagode Maryam” Hajiya Mariya tace “Nan xata kwana, ko xa su yi discharging dinta?” Aliyu 

yace “Sai gobe da safe” Hajiya Mariya tace “Toh shkkn sai Maryam ta kwana tare da ita” Shiru Aliyu yayi ya rasa me xai ce don bai so haka ba, Hajiya Mariya 

ta ja kujera ya xauna ta bude basket din don debar ma Khadijah abinci, sai kusan karfe takwas ta bar asibitin tare da Aliyu ba don ya so ba, suna fita babu 

dadewa wayar Maryam ya fara ring, dauka tayi ganin Jawahir ke kiranta ta d’an wara ido ta daga kafin ta ce komai taji muryar khaleel, xaro ido tayi tace 

“Ina yini Dr?” Yace “Lafiya lau ya kike, I want to ask plss Maryam, Kun hadu da Khadijah schl yau?” Maryam tace “Gata nan  ai muna asibiti bata da lafiya, 

she collapsed daxu a cafteria but da sauki yanxu she’s recovering” khaleel bai san lkcn da ya mike ba, jawahir dake kwance Shureim a gefenta dai sai 

kallonsa take, ya jira har Maryam tayi shiru kafin a hankali yace “Wani asibitin ku ke?” Ta fada masa sunan asibitin yace “Toh xan xo yanxu” daga haka ya 

katse wayar, yana kallon jawahir yace “Xan je duba Khadijah clinic yanxu she is sick, I will be back soon” jawahir dai bata ce komai ba ya nufi kofa, 

Shureim ya sauka daga kan gadon da sauri yace “Uncle ni xan bi ka” jawahir ta jawo sa jikinta tace “Don’t worry yanxu xai dawo” a parlor khaleel ya dau 

makullin motarsa ya bar gidan ya nufi asibitn da Maryam ta gaya masa, yana parking a haraban hospital din ya fito ya kira Maryam don da wayar jawahir ya 

taho, Maryam na daga kiran yace “Ina waje Maryam” ward number ta fada masa yace “Thanks” daga haka ya katse wayar ya shiga asibitin, ya fi seconds talatin a 

bakin kofar ya kasa budewa, can ya murda a hankali ya shiga ward din, Kwance Khadijah take idonta lumshe, Maryam ta mike ganinsa tace “Sannu da xuwa Dr” 

yace “Yauwa Thanks” karasowa yayi bakin gadon yana kallonta, Maryam tace “Ina jin ta koma bacci” shiru yayi bai ce komai ba yana kallonta har lokacin don 

yasan ba bacci take ba, he really want Maryam to excuse them but he don’t know how to make the approach, kamar kuwa Maryam tasan abinda ke ransa ta mike ta 

dau wayarta tace “Doctor bari inyi making wani call in dawo yanxu” ya kalleta yace “Alryt” daga haka ta nufi kofa ta fita ta rufe kofar, ya lumshe ido ya 

bude ya xauna gefen gadon ya kamo hannunta  ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace “I know you are awake Khadijah, look at me plss”

Khadijah bata yarda ta bude ido ba, ya dinga kallonta, a hankali yace “Baxa ki kalleni ba Khadijah” dauke kanta tayi ta juya masa baya, mikewa yyi ya koma 

kujera ya xauna yana kallonta, bayan wani lkci yace “Shkkn since you don’t want to see me bari in tashi inyi wucewata” a hankali ta juyo tana kallonsa, 

tausayinta ya dinga ji har ransa ya taso ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace “Ki gaya min ko na maki wani abun ne Khadijah, bana 

son wani abu ya same ki saboda ni, tell me ur mind plss…”  Tana kallonsa da kyau tace “What is in my mind da xan gaya maka?” A hankali yace “Noo, ai ke 

xaki fada I don’t knw what you are thinking of me… Say out ur mind Khadijah” ta hade rai tace “Kana tunanin saboda kai nake rashin lafiya a nan?” Ya buda 

ido sosai yace “Noo ba abinda nake nufi ba kenan” Tace “Toh ciwo ne kawai Allah ya sakko min, so I just have to say Alhmdllh” Ya langwabar da kai yace “Toh 

Allah ya sauwake” tace “Ameen” yace “Kin ci abinci?” Kai ta gyada masa tace “Su Maryam sun kawo min” Wayarta dake ajiye yyi haske alamar kira khaleel ya 

dauka ya mika mata ta karba, ganin barrister ke kiranta ta daga ta sa a handsfree ta kai kunne, da damuwa yace “Ina kika shiga Amira, I have been calling 

since but no response” ta koma ta kwanta a hankali tace “Kayi hakuri plss, yau tun da na tashi nake jin ciwon ciki, sai bayan da naje schl sai ya matsa min 

aka taho dani clinic…. Am even stil at the clinic” Sudais yace “Subhanallah, wani irin ciwon ciki ne haka?” Ta d’an buda ido tace “Aa ni ma ban sani ba, 

kawai dai ciwon ciki” yace “Ko dai… Ko dai na period ne?” xaro ido tayi don ita har mancewa take akwai wani abu wai shi al’ada, tun da ta haifi su Shureim 

ta daina, sai dai tayi bai fi sau daya ko biyu a shekara ba shi ma na kwana biyu, Amma fa tana shan axaba sosai don wani lkcn har tunani take kila mutuwa 

xata yi, yace “Uhm shine koh?” Yar dariya tayi tace “Ae ni bana yi” yace “Bakya me?” Tace “Uhm abinda ka fada mana” yace “Are you serious?” Tace “Ehh” yace 

“Maa sha Allah, kice doubling sadaki xan yi kenan” Boye fuskarta tayi da gado don ba karamin dariya da kunya ya bata ba ga khaleel a xaune, shi dae Khaleel 

idanuwansa na kan wayar hannunsa da yake dannawa yana saurarensu, ta dago a hankali tace “Koh?” Yace “Ehh mana, ai ku special ne cikin mata, and you are 

rare….” tace “Uhmm” lkci daya khaleel ya mike ya nufi kofa ta bi sa da Harara har ya fice, Barrister yace “But hope ciwon cikin da sauki sosai yanxu?” Ta 

gyada kai tace “Naji sauki amma sai gobe xa ayi discharging dina” yace “Toh wa ya kawo ki asibitin?” Da har xata ce Aliyu sai kuma tayi shiru, da sauri tace 

“Maryam da na baka labari ranan, ita ce ta kawo nii, luckily ta shigo cafteria lkcn ta gan ni kawai muka wuce clinic” Yace “Toh Allah ya kara lafiya, how 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button