NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 71-80

about shureim ko tare ku ke a asibitin?” Ta girgixa kai tace “Noo yana gun neighbors dina” Barrister yace “Ohk, I will send the hospital bill yanxu kin ji” 

da sauri tace “Nooo, ‘yan gidansu Maryam sun biya ma, don’t bother plss my barrister” yace “Toh idan na turo sai kiyi pepper soup da yawa ke da Shureim ku 

ci, clear?” murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace “Yea, sai da safe dear, Allah ya kara lafiya” a hankali tace “Ameen nagode sosai” lumshe ido yayi ya 

katse wayar, Khadijah ta mike xaune a hankali, gaba daya taji ta samu relieve kamar an cire mata ciwon, Maryam ce ta dawo ward din tace “Ashe kin tashi 

Khadijah” d’an murmushi Khadijah tayi tace “Ehh” Maryam tace “Ohk, Dr Ayman yace in fada maki ya wuce sai da safe” Khadijah tace “Ohk, I was making call ya 

fita” sosai Khadijah ta sake da Maryam suka dinga hira a ward din har Maryam ta dinga mamaki ganin ashe dai tana magana haka, sai kusan karfe sha daya duk 

suka kwanta. Washegari karfe bakwai na safe Aliyu ya xo clinic din, Khadijah na bathroom tana wanke baki da sabon toothbrush da Maryam ta kawo mata da 

paste, Maryam suka gaisa da Aliyu yana kallonta yace “Ya jikin nata?” Maryam tace “Ai kam taji sauki sosai” dai dai nan Khadijah ta fito ta karaso tana 

kallonsa a hankali tace “Good morning” yace “Morning Iman ya jikin?” Tace “Naji sauki sosai, thanks for ur care” yayi murmushi har ransa yaji dadin yanda ya 

ganta unlike yesterday, ya ajiye breakfast da Hajiya Mariya ta bada ya kawo masu, Khadijah ta xauna gefen gadon tana kallonsa tace “Plss ina son kaje can 

gida I don’t want to inconvenience anybody sae ka dau Shureim kayi dropping dinsa schl” Yana shafa kansa yace “Dr Ayman din baxae kai sa ba?” Tace “Toh ni 

bari in je in daukesa in ajiye sa schl idan baxa ka je ba, Kuma ai nasan da Dr Ayman din” murmushi yayi yace “Aa ae bn ce baxan je ba malama” turo baki tayi 

ya juya ya fita ward din din Maryam ta bi sa da kallo, Mikewa tayi daga karshe ta hada ma Khadijah shayi da ya kawo ta bata da kwai, Khadijah ta amsa tace 

“Nagode” daga haka ta fara shan shayin da spoon, bayan kusan awa daya Aliyu ya dawo ward din, kujera ya ja ya xauna ya jinginar da kansa da kujerar yace 

“Dama kawai don ki bani wahala ne kika ce in tafi koh?” Tana kallonsa tace “Me ya faru” murmushi kawai yayi ya dago yana kallonta, ta ci gaba da Shan 

shayinta, mikewa yayi yace “Anyi discharging din ki yanxu, we can leave” tace “Toh bill din fah, am not with money, ko idan mun je gida sai in baka, nawa ne 

kudin?” Ya fi minti daya yana kallonta kafin ya juya ya fita ward din, Maryam ta d’an yi murmushi tace “Haba dai ya biya ai Khadijah….” Khadijah ta sakko 

kan gadon ta dau mayafinta da wayarta da jaka tace “Toh nagode” Maryam ta dau kayan shayin da ya kawo suka fita waje, a haraban asibitin suka tadda shi yana 

jiransu cikin mota, Maryam ce ta shiga gaban motar Khadijah ta shiga back seat suka bar asibitin, da Khadijah ta daga kai sai su hada ido da Aliyu yana 

kallonta ta madubi, ta daga kai yayi sau uku sai su hada ido, ji tayi gaba daya she is uncomfortable, ta matsa a hankali ta koma can karshen motar tana 

kallon waje, dai dai gidanta yayi parking ta bude motar ta fito ta xagayo ta inda Maryam take tace “Nagode sosai Maryam, ki taya ni yi ma Mumy godiya in sha 

Allah xan shigo anjima da yamma ko gobe, Allah saka da alkhairi” Maryam ta d’an yi murmushi tace “Ba komai, sai kin xo” kallon Aliyu dake ta kallonta tayi, 

da kamar baxa ta ce masa komai ba sai kuma tace “Thanks” daga haka ta juya xata wuce ciki, a hankali yace “Anjima xan kawo maki drugs din ki Iman” tace 

“Ohk” tana fadin haka ta shiga gida ya ja motar suka bar street din. Tun daga wannan rana gaba daya Khadijah ta ajiye khaleel da jawahir gefe daya, 

tsakaninta da su gaisuwa faram faram ita kanta tayi mamakin yanda har ta sake ma jawahir yanxu duk da ita sai wani daure mata take, Lkci daya Khadijah ta 

yakice khaleel gaba daya a ranta, ko don tashin dare da take yawan yi tana rokon Allah ya cire duk wani connection dake tsakaninta da shi a xuciyarta ne, 

yanxu tun safe in ta fita gidan dama sai yamma take dawowa kuma duk ta dawo xata tarar khaleel ya dauko shureim, wani lkcn basa ma sanin ta dawo, yanxu kam 

ita kanta tasan ta rage damuwa sosai, jarabawarta kawai ta sa gaba, duk bayan kwana biyu ta kan je gidansu Maryam gaida Hajiya Mariya, kuma duk taje sai sun 

hadu da Aliyu, wani lkcn ta amince ya maido ta gida wani lkcn kuma tace baxata hau motarsa ba shi dai kam sai dai yayi murmushi baxai ce komai ba, sai ta 

tafi tayi ta tausayin sa bata san dalili ba, har xuciyarta take ganin Aliyu kamar little Sudais dinta cos the little boy have all his fathers quality, Kuma 

tasan saboda Aliyu yasa ta sa ma kanta dangana haka, Wani rama khaleel yake da shi kansa bai san dalilinsa ba, gaba daya ba shi da sukuni, yanxu kam sure 

yasan Jawahir and Khadijah are cousins daga binciken da yayi but bai san ta inda xai billo ba, gaba daya kansa ya kulle, bai taba xaton haka ba, they are 

very close relatives, dauke masa wutan da Khadijah tayi ya fi komai bata masa rai, in har ta gaishesa a gidan to tare ta gansa da jawahir, in ko just haduwa 

suka yi su biyu ko kallon inda yake bata yi, sai ma saurin barin wajen da xata yi, shi dai yasan har sannan bai cire rai da ita ba ko don nuna mata iyakarta 

kan walakancin da tayi masa but how will that be when they are cousins  with his wife Jawahir?? sure it’s not prohibited, but Uhm… A can Nigeria kuwa 

Sudais ya gama hada lefen sa tsaf, komai ya siya sai ya nuna ma Khadijah ta WhatsApp ko yayi mata, Yana gama hada lefen dama ya kai ma jiddah kayan fadar 

kishiya, tun da taga akwatunan hankalinta yayi mugun tashi, ya sanar da ita ko na meye bai tsaya saurarenta ba ya fice, Ta fashe da matsanancin kuka tana 

kallon kayan, yanxu har auren nan ya matso bata samu damar daukar number Khadijah a wayar Barrister ba gaba daya hakan ya faskara duk iya kokarinta, Nan ko 

bata san duk Barrister ya lura da take takenta ba ya canxa yanda yyi saving number Khadijah daga Amira ya mayar Ummu Shureim, Xaunawa jiddah tayi kan kujera 

wata dubara ta fado mata…. Murmushi tayi tana share hawayen ta a hankali tace “Allah ya kai mu ranan auren, ai dai Amarya xata tare koh? Toh a daren 

farkon ta gidan ka xan maku abinda ita xata yi da ta sanin auren ka, kai Kuma xaka gwammace baka aureta ba” wani murmushin ta kuma yi ta wuce daki xuciyarta 

fess, har Allah Allah yake ranan ya xo ta cika aikinta, ta tabbata Khadijah baxata kwana gidan ba Kuma har karshen rayuwarta xata ji baxata iya yafe masa 

ba, ba boka ba malam. Ana saura sati daya Khadijah ta taho hutu Barrister Sudais yaje katsina gun Kawunta bayan Umma ta basa address, ciwon kafa kawu jibril 

ke fama da shi sosai sai dai hakan baya hanasa tafiya, duk yaransa biyu da ya aurar na xaune gida da ya yansu auren ya mutu,  gashi yanxu duk kudin sun ja 

babu komai sai motoci biyu da gidan da yake ciki, kawu na jin abinda ya kawo Sudais bayan sun shiga parlorn sa, ya dinga masa wani kallo yace  “inaaa, you 

are mistaken don bani da wata ya wai Khadijah, ka dai koma ta kai ka gun dangin ubanta amma ba ni ba, tashi ka ban waje malam” Sudais dake ta kallonsa yace 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button