NOOR AL HAYAT 71-80

“Amma dai ka santa koh?” Kawu yace “Toh meye amfanin sanin nata, Yarinyar da rabon da na sa ta ido yau xai yi shekara goma sha, tana can tana yawon duniya
da kishiyar babarta” Sudais ya san xa ayi hakan shi yasa ma ya fara xuwa shi kadai, bai taho da kowa nasa ba dama Kuma bai sa ran Kawunta xai yarda ya daura
mata aure ba” Sudais yyi murmushi yana kallonsa da kyau yace “Kawu dama ba wai lallai sai kai xaka daura mata aure ba, Kar ka mance babu abinda kudi basa yi
a duniya, kawai dai dama an sa na xo ne don a fita hakkin ka a matsayin ka na wan mahaifinta, bayan haka Kuma kawu yanxu xaka iya damka ma Khadijah gadon ta
na mahaifinta tunda ta mallaki hankalinta?” Da mugun mamaki Kawu Jibril ke kallonsa baki bude, can ya mike da kyar yace “Kai a uban wa xaka xo min da xancen
gadonta??” Mikewa Sudais yyi ya tako har gabansa ya fiddo Id card dinsa yana masa wani kallo yace “Ni a lawyer mai xaman kansa…. Barrister Aliyu Umar, don
haka nake maka gargadi kawu kar ka yarda magana ta kai mu ga shiga kotu baxai maka kyau ba… 10 years kamar yanda ka fada is enough.. hand over her
properties to her” Daga haka Sudais ya juya ya fita kawu ya bi sa da kallo cikinsa na kara baki sake…. Yau Khadijah ta gama exams tana bedroom tana ta
shirye shiryen kayan da xata koma Nigeria da, Shureim kuma na parlor ta bar sa yana bacci taji kamar an bude kofa, juyawa tayi da sauri don bata ma san
kofar a bude yake ba, tayi saurin daukan hijab xata fita suka kusa cin karo bakin kofar dakin.
Komawa baya khadijah tayi tana kallonsa, ya shigo xai rufe kofar ta xaro ido tace “Meye haka Doctor” rufewa yyi ya yana tahowa kusa da ita yace “Tell me why
you are avoiding me Khadijah” wani kallo tayi masa tana komawa baya tace “Avoiding din ka kamar ya, bayan gaisuwar da nake maka me kuma kake so daga
gareni?” Ganin ya kusa isketa ta juya da sauri xata shige bathroom, yyi hanxarin rikota ya juyo da ita yana kallonta, wani kara tayi ya matseta jikinsa yana
mata wani kallo, lkci daya jikinta ya dau rawa tace “Stop it plss Dr, meye haka don Allah ka bari ni bana soo…” yace “Is it a crime don nayi aure?” Sake
baki tayi tana kallonsa, can ta hade rai tace “Ban gane ba?” Yace “Ehh tunda nayi aure kika kara dasa min rashin mutunci a kan na da, I showed interest in
marrying you kika yi shunning dina, me kuma kike son in maki Khadijah? Tell me me kike so?” A hankali tace “Let go of me now!” ba musu ya saketa yana
kallonta, juyowa tayi tana facing dinsa da kyau tace “Ai da kana so na kamar yanda kake ikirari ko me xan ce maka baxai hana ka abinda ke a ranka a kai na
ba, kuma abinda yasa baka wani damu ba shine saboda kana da warce kake so da aure… so don’t tell me dat Ayman” Ya shafa kai yana mata kallon mamaki, bude
kofar parlorn suka ji aka yi, a tare suka kalli door din dakin, ya nufi kofar ya bude ta bi bayansa, tsaye suka ga Jawahir a parlorn ta rike waist da hannu,
Khaleel ya karaso kusa da ita kamar mai tausayin kasa ya tsaya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ta taka ta tafi gun Khadijah dake tsaye bata karaso
cikin parlorn ba, wani kallo Jawahir ta dinga mata kafin tayi wani murmushi tace “Khadijah kike kowa? Let me warn you first before taking any action….”
Strictly tana mata wani shegen kallo tace “Stay Away from my husband, I repeat my self stay away from him you bitch, idan ma kina da wani kuduri a kansa a
ranki ne to kiyi maxa ki goge don wllh ya fi karfin ki nesa nesa ba kusa ba, shi ba sa’an ki bane, shi ba sa’an auren ki ba ne, and let me advice you as a
lady…. idan aure kike so ki rufa ma kanki asiri ki koma gidan uban ‘ya yan ki wllh hakan kadai ne rufin asirin ki, ke bari ma kiji abinda baki sani ba, da
Khaleel ya aure ki a matsayin kishiyata gwara ya auro min budurwa kamar ni mu goga, banda naci da ba kai wahala Ina ke ina Khaleel kina baxawarar, ragowar
wani???” Tsawa Khaleel yyi mata ya isa kusa da ita lkci daya idanuwansa suka sauya xuwa ja yace “Kina da hankali Juwairiyya? Kin san wacece ita kike fadi
mata wannan maganan gabana?” Wani kallo ta masa ta daga masa hannu tace “Spare me Malam ba da kai nake ba da sa’ata nake, keep ur mouth shut… ban kuma
damu in san wacece ba, tunda ta shanye ka ni bai gagareni in kwatar maka yan cin ka ba” Fincikota Khaleel yyi a mugun fusace yace “Did you knw I can give u
a dirty slap now?” Jawahir tayi dariya tace “Wllh ka mare ni in rama a kanta, wai ma a kan shegiyar mai makale ma maxajen mutane xaka ce xaka mareni
Khaleel?” Kasa ce mata komai Khaleel yyi, can ya runtse ido ya turata yace “Ina guje maki ranan da xaki ji kunya Jawahir, ranan da xaki kasa kallon idanuwan
warce kike ma rashin mutunci yanxu, Kuma bayan kin san ta kina ji kina gani xan aureta in hada ku….” Khadijah tayi wani murmushi bata ce komai ba ta juya
a hankali ta koma daki ta rufe kofar ta sa key, tafi minti goma kwance kan gado, ita kanta ta rasa me ya hanata yin kuka, kalmomi hudu suka tsaya mata a
lkcn, Bitch, Baxawara, ragowar wani, mai makale ma maxan mutane, yanxu jiddah ma kallon da take mata kenan koh?? wani murmushin tayi ta kai hannunta
fuskarta jin abu na sauka taji hawaye ne, cikin pillow ta cusa kanta bata sake dagowa ba sai kusan karfe dayan dare shima ta dalilin sanyin dake neman mata
illa, da kyar ta mike jikinta na rawa ta fiddo kayan sanyi ta sa, Shureim ya fado mata ta fita parlor da sauri, kwance ta gansa kan kujera ya takure waje
daya yana rawar sanyi duk da kayan sanyin jikinsa, ta isa kusa da shi ta daukesa ta rungume sa ta karasa gun kofa ta sa key sannan ta kashe wutan parlorn ta
wuce daki, kwantar da Shureim tayi ta rufa masa duvet ta wuce bathroom ta sa ruwan dumi tayi alwala ta fito, sai kusan karfe biyu da wani abu ta kwanta
bacci me nauyi ya dauketa. Tun da tayi sllh asuba take ta shirya sauran kayansu, tana gamawa ta tada Shureim ta shirya sa ta basa tea da sauran cake dake
gidan, ita ma ta shirya, wayarta ta dauka ta shiga scrolling call log a hankali tana neman number Aliyu duk da bata yi saving ba amma tasan number, ta fi
second goma tana kallon number can tayi dialing, bugu biyu ya daga, a hankali yace “Iman, hope all is well?” ta gyada kai kawai tace “Ina kwana” yace
“Lafiya lau, Ina Shureim” ta kalli Shureim dake gefenta a xaune, murya can kasa tace “Airport xaka xo ka kai mu pls, if we won’t inconvenience you”
Aliyu yace “Sure, yau xaku tafi Nigeria din?” Tace “Ehh” yace “Toh gani xuwa yanxu” daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti sha biyar tana xaune ta
rungume Shureim kai kana ganinta kasan she is just weak, duk ta xama kamar mara lafiya alhalin babu inda ke mata ciwo, da ta tuna maganganun da Jawahir ta
gaya mata jiya da yamma sai tayi murmushin takaici, mikewa tayi ganin kiran Aliyu ta dau karamin jakarta suka fito bayan ta tabbatar komai na gidan ta kashe
ta kulle kofar apartment din, ta nufi waje rike da hannun Shureim, Kayan sanyi ne jikinsa shi ma yana jingine jikin mota ya rungume hannunsa, yana ganin
Shureim ya isa kusa da shi ya daga sa ya rungumesa a hankali yace “Good morning sweetheart” murmushi yaron yayi yace “Good morning uncle” kallon khadijah