NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 71-80

Khadijah ta sauke idonta kasa tace “Ina gaisheta” lumshe ido yyi ya bude yace “Or xa ki je ku gaisa yanxu, tana son ki sosai, anjima sae in mayar da ke gida 

then u face Ur Dr Ayman…. Sai ki masa bayanin abinda kike nufi ya daina fushi da ke” ta hade rai tace “Ni ba ruwana da shi, bana son sa kuma” tana fadin 

haka ta kife kanta da table ta fara rera kuka, Aliyu ya dinga kallonta ko kiftawa babu, can yyi kasa da murya yace “Toh kiyi hakuri kar ki sake kuka, am 

sure shi ma ba har ransa ya gaya maki haka ba fa” Bata sake cewa komai ba ya biya bill din yana kallonta yace “Tashi mu je” mikewa tayi ya mike shi ma, tana 

gaba yana biye da ita Dr Ayman ya bi su da kallo har suka fita, har suka iso gun motarsa bbu wanda yace komai, ya bude mata motar yana kallonta, a hankali 

ta karaso ta shiga, ya rufe sannan ya xaga ya shiga ya tada motar ya fita eatry din, sae da suka hau saman titi a hankali yace “Mu je ku gaisa da ita Iman?” 

Shiru tayi da farko kafin murya can kasa tace “Toh” yayi murmushi yace “Thanks Ummu Shureim” har suka iso gidan babu wanda yace komai cikin su, yanxu kam ta 

daina jin xugin da take ji a xuciyarta, yayi parking yana kallonta yace “Toh fito” ba musu ta fita shima ya fita, Yana gaba tana biye da shi har suka shiga 

parlorn gidan. Maryam kadai ce parlor tana rubutu a takarda, ganinsu ta mike da mamaki tace “Lahh Khadijah ce gidanmu yau, sannu da xuwa” Khadijah ta xauna 

tana kirkiran murmushi da kyar tace “Yauwa nagode” Aliyu ya wuce sama, Maryam ta bi sa da kallo, kamar yanda Khadijah ke kallonta, tashi tayi daga karshe ta 

dauko mata ruwa da drink ta ajiye gabanta tana tambayarta Shureim, a hankali Khadijah tace “Yana schl” Maryam ta xauna tace “Ayya, kin shiga schl kuwa yau?” 

Khadijah ta gyada kai tace “Daga can nake” Maryam tace “Nima kin ga yanxu na dawo, nama yi ta jiran ya Aliyun don ya ce min xae shigo shi ma amma ban gansa 

ba….” Fitowar Hajiya Mariya ya sa Maryam ta mike tace “Anty yau ga mum Shureim gidan mu” Da murna Hajiya Mariya ta karaso cikin parlorn tace “Wlh kuwa, 

maa Sha Allah, sannu da xuwa Khadijah” Khadijah ta sunkuyar da kanta da ladabi tace “Nagode mumy, Ina yini?” Hajiya Mariya tace “Lafiya lau Khadijah ya 

gidan?” Tace “Alhmdllh” Hajiya Mariya tace “Ya karatun fa?” Khadijah tana wasa da xobenta tace “Alhmdllh Mumy” Hajiya Mariya tace “Maa Sha Allah, Allahu ya 

baku sa’a, Ina Shureim din?” Aliyu da ya shigo parlorn yace “Yana schl Anty” tace “Allah sarki, ashe ya fara schl din a nan, Allah yayi masa albarka ya raya 

sa” Mikewa tayi daga haka tace “Mu je sama kiyi sallah ki ci abinci koh” kasa cewa komai Khadijah tayi ganin ta fara tafiya ta mike ta bi bayanta a sanyaye 

suka haura sama, Maryam na kallon Aliyu tace “Yaya shine ka shanya ni schl koh?” Ya shafa beard dinsa bai ce komai ba, Khadijah na haurawa sama tare da Mumy 

ta juya tana kallonsu, suna hada ido da Aliyu tayi saurin dauke kanta ta shiga dakin da Mumy ta shiga. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh Maryam 

ta shigo dakin rike da tray na abinci ta ajiye mata tace “Ga abinci Khadijah” Khadijah ta xaro ido tace “Wallahi na ci abinci kafin mu xo nan am not hungry” 

Maryam tace “Toh ko kadan ne dai ki ci” Khadijah xata yi magana aka bude kofar, jawahir ce ta fara shigowa, suna hada ido Khadijah ta sunkuyar da kai, 

Jawahir dake ta kallonta ta ajiye jakar hannunta ta fice daga dakin, sosai jikin Maryam yayi, ita dai Khadijah bata sake dago kanta ba, sai ga deejah ma ta 

shigo dakin, ta wara ido ganin Khadijah tace “Wow Khadijah ke ce gidan yau?” Murmushi Khadijah tayi tace “Ina yini” Deejah tace “Lafiya lau, ya lectures? 

Tare da Maryam ku ka xo?” Maryam na yar dariya tace “Ehh mana” Deejah tace “Ayya ya little shureim” Khadijah tace “Yana schl” Deejah tace “Toh maa Sha 

Allah” daga haka ta fita, Khadijah ta kalli agogon dakin don gaba daya hankalin ta yyi kan yaronta sanin ya kusa tashi a schl, ganin Maryam na sllh ta jira 

har ta idar kafin tace mata tayi ma Mumy magana xata wuce, Deejah ce ta dawo dakin tana video call ta iso kusa da Khadijah ta durkusa tana murmushi ta haska 

ta tace “Ammi ki duba fa plss basa kama??” Khadijah ta ki kallon screen din tana murmushi, Deejah tace “Khadijah ki tsaya ku gaisa da Ummar mu pls” sai a 

sannan Khadijah ta kalli screen din wayar, wata matashiyar mata ta gani gaban wayar, a hankali tana kallonta tace “ina yini?” Matar na kallon ta da fara’a 

tace “Lafiya lau yan mata, ya kike ya karatu?” Khadijah tayi murmushi tace “Alhmdllh” matar tace “Maa Sha Allah, Allah yayi maku Albarka ya bada abinda aka 

je nema, sai ayi ta kula kin ji?” Khadijah ta ji dadin addu’ar cikin sanyin murya tace “Ameen mama nagode” matar tayi mata sallama, Deejah ta mike rike da 

wayar tace “Ammi idan Safeenah ta dawo plss ku kira ni in nuna mata duplicate din ta” murmushi kawai Khadijah tayi, Deejah ta fice daga dakin tana ci gaba 

da waya da mum dinta. Khadijah ta kalli Maryam dake kallonta tace “Kice ma Mumy xan wuce” mikewa Maryam tayi tace “Toh” daga haka ta fita, tare suka dawo 

dakin da Mumy tace “Har xa ki koma daughter?” Khadijah tayi murmushi tace “Eh mum, Shureim sun tashi a schl” Hajiya Mariya tace “To maa Sha Allah, mun gode 

da ziyara Khadijah, Allah yi albarka” a tare suka sakko kasa har da Maryam, Mumy ta ba Khadijah sako a leda ta kai ma Shureim, a kunyace ta amsa tace “Allah 

saka da alkhairi mum” Deejah vata ji dadi ba ganin wucewa Khadijah xata yi, tace “Ae ko xan xo gidan ki ko gobe” Yar dariya Khadijah tayi tace “Allah ya kai 

mu” tare da Maryam suka rakota har bakin motar Aliyu don yana cikin motar yana jiranta, daga masu hannu tayi bayan ta shiga tace “Toh nagode, sae anjiman 

mu” Aliyu ya ja motar ya fita cikin gidan, sae da suka dau hanya tace “Xan dau Shureim a schl” yace “I thought as much, naga it’s time” Mamaki Khadijah tayi 

ganin ya dau hanyar makarantar, ta kasa daurewa tace “How did you knw d schl?” D’an murmushi yayi murya can kasa yace “Kin raina irin bond dake tsakanin a 

son and his father?” Shiru Khadijah tayi tana kallonsa, lkci daya ta hade rai ta turo baki tace “Don’t call him ur son, stop calling him that” kallonta yyi, 

A hankali yace “Ko saboda me?” A takaice tace “His father is a barrister” Murmushi yayi bai ce komai ba, he really really don’t want to hurt her da babu 

abinda xai hanasa tambayar ta ko barrister ne yayi mata cikinsu, suna isa schl din bayan yyi parking ta bude motar ta fita don dauko d’an ta ya bi ta da 

kallo, ba a dau lkci ba ta dawo a sanyaye, yace “Where is he?” Ta bude motar ta shiga a hankali tace “Dr ya tafi da shi wai”

Aliyu bai ce komai ba ya tada motar a hankali ya bar premises din school din, har suka isa babu wanda yace komai, yana gama parking ya juya yana kallonta, 

ta bude motar ta fita tace “Nagode” yace “ki gaida min Shureim” ba tare da ta juyo ba tace “Ohkk” Da ido ya bi ta har ta shiga cikin gida, yayi wani 

murmushi ya ja motarsa ya bar wajen, tun da Khadijah ta shiga compound take ta kallon motar khaleel, lkci daya mood dinta ya canxa ta isa apartment dinta ta 

bude jaka ta fiddo makulli ta bude kofar ta shiga. Wanka tayi ta kwanta parlor ta fada duniyar tunani, murda kofar parlorn taji anyi ta mike xaune da sauri, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button