NOOR AL HAYAT 71-80

dinta ta dinga jujjuyawa bata ce komai ba sai dai gaba daya tunaninta a lkcn ya tafi kan khaleel, a hankali yace “Kin yi shiru” wani mugun haushin kanta
taji ganin Wanda ya fado mata a rai, d’an tsaki tayi ba tare da ta san tayi hakan ba, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace “Ke da wa kuma??” Da sauri
ta kallesa ta xaro ido tace “Don Allah kayi hakuri barrister wllh ba da kai nake ba, ban san….” Katse ta yayi yace “Nasan ba da ni kike ba Amira, I can
see you are lost in ur thought, tel me what u are thinking of” ta girgixa kai tana kirkiran murmushi tace “Uhn ba komai fa” murmushi yayi yana shafa kansa
yace “Toh shkkn” flask din ya bude ta mike da sauri tace “Bari in xuba maka” daga haka ta karasa budewa ta xuba masa a cikin mug dake kife, kallonsa tayi
taga kallonta kawai yake shi ma, ta sauke kanta kasa a hankali tace “In sa maka Madara?” Ya girgixa kai yace “Noo, I prefer it black” Komawa tayi ta xauna
tana murmushi tace “Toh, what will you take for dinner?” Ya d’an bude ido bayan ya dau Lipton din yace “Da daddare sometimes ina shan tea with irish and
egg” ta langwabar da kai tace “Toh da safe fa?” Yayi murmushi yace “Tea and bread” da mamaki ta kallesa tace “Toh barrister baka cin tuwo ko shinkafa ko dai
any other food?” Yace “Ina ci idan na samu” shiru tayi bata sake cewa komai ba, lkci daya taji tausayinsa don ko bai fito fili ya gaya mata ba ta gane
Matarasa ce bata girki kenan, d’an murmushi tayi tace “Toh xan maka tuwo anjima ka dawo ka karba” ya xaro ido yace “A’a ku mata da bakwa son girki mai
wahala don’t stress ur self dear I will take tea na riga na saba” tace “No, ba ko wace mace ce ke jin kiwiyar girki ba, I am also exceptional, ko mai kake
so xan girka maka anjima” murmushi yayi sosai yace “Toh nagode Amira” Sai biyar saura ya bar gidan, shi ma saboda ya damu bai yi la’asar bane…” Ta rakasa
har bakin motarsa sai da ya wuce sannan ta koma ciki. Kamar yanda ta fada masa kafin magrib har ta gama yi masa tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup, ta
xuba masa a warmer, ganin bai kirata ba har bakwai ita ta kirasa, bayan ya dauka a hankali tace “Barrister baka dawo ka karba ba kuma” yayi kasa da murya
yace “I really don’t want to stress you dear, I learn girka tuwo akwai wahala…” Katse sa tayi tace ” Ni dai ka xo ka amsa na gama, akwai wahala gun
ragwayen mata dai” dariya yayi yace “Ohh really?” Tace “Yea, tun daxu na gama, ka taho ka amsa plss” a hankali yace “Toh gani xuwa Amira, I am proud of you”
murmushi kawai tayi ta katse wayarta, cikin minti goma ya taho amsan abincin ya dinga sa mata albarka har ya tafi. Washegari Saturday da yamma Sudais ya xo
ya fita da ita su xaga gari, duk da sanyin garin, the moment was just waow, ita dai ta san Sudais na sonta fiye da xaton ta but bata san me yasa ta kasa
kwantar da hankalinta ba, he really made her day on Saturday, don babu wani damuwa tare da ita ya maido ta gida, kewan Shureim ma da take ji gaba daya taji
babu shi yanxu. Ranan lahadi da safe tun da ta tashi ta shiga kitchen don girka masa shinkafa da miya, karfe goma ta kirasa, bayan ya dau wayar jin muryarsa
a hankali tace “Bacci kake barrister?” Yace “Uhn am now awake” tace “Kayi hakuri ban san baka tashi ba, ka gaya min address din ka sai in kawo maka
breakfast” ya mike xaune daga kwancen da yake kan gado yace “Noo ba sai kin ba kan ki wahala ba xan shirya yanxu in fito” tace “Toh, kayi hakuri” ya wara
idanuwansa yace “Hakuri kuma dear” murmushi tayi ta katse wayar, bedroom ta wuce ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin kananun kaya, tana
xaune gaban mirror tana gyaran gashinta kawai ta tabe baki ita kadai, yanxu su Maryam gaba daya sun tafi Nigeria biki kenan, d’an tsaki tayi a ranta tace do
I have to care, turo baki tayi ta mike ta daure gashinta ta dau rigar sanyi ta sa da head warmer ta dawo parlor ta xauna.
✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Ranan lahadi da safe Khadijah ta raka Sudais Airport, har ranta ta dinga jin kewarsa bayan ya tafi duk jikinta yayi sanyi, tana tsaye inda xata hau cab a
wajen airport din kamar ance ta kalli gefenta taga khaleel tsaye alamar fitowarsa kenan shi ma daga cikin airport, farar shadda ce jikinsa sai walkiya take,
Khadijah ta dauke kai da sauri tun kan ya kallo inda take ta karasa gun cab da ta gani ta shiga ta fada ma driver din inda xata. Suna isa gida ta fito ta
basa kudin sa sannan ta shiga ciki da sauri ta bude jakarta tana kokarin ciro makulli, dai dai nan khaleel ya shigo gidan, bata yarda ta juya ba ta bude
kofarta ta shige. Daki ta wuce ta tattara reading materials dinta, ta dau kayanta kala biyu da nyt wear ta fito rike da jakarta, kulle apartment dinta tayi
ta wuce kamar warce ake jira a waje tsabar haste din, tana fita ta samu Cab ta hau xuwa gidan Vanessa. Gaba daya ranan a gidan ta yini, sai dai she was just
uncomfortable saboda mazan turawan dake xuwa suke fita gidan, gashi ba isasshen hankali gare su ba duk ta takura, ta so komawa gida da daddare amma saboda
sanyi ta hakura ta kwana gidan, washegari daga gidan ta shirya xuwa sch tare da Vanessa bayan sun yi breakfast, suna gama lectures Vanessa ta sake jan
Khadijah suka koma gidanta, tana xaune parlorn Vanessa bayan tayi magrib idonta a kan takardun hannunta ta jawo wayarta dake ring, number Aliyu ta gani sai
a sannan ta tuna da yaronta ta yi picking kiran, daga daya bangaren yace “How are you Iman” tace “Fyn, how about my son” yace “Naga kin ma mance da shi gaba
daya” ta hade rai tace “Taya xan mance shi?” Murmushi yayi yace “Toh gobe da safe xan kawo shi don ya samu yaje schl” tace “Kun dawo ne?” Yace “Yea daxu da
yamma” shiru ta d’an yi kafin tace “Bring him in the afternoon” yace “Alryt then” daga haka ta katse wayar ta. Ranan talata bayan sun gana lectures misalin
karfe biyu Khadijah ta koma gida, bude kofar apartment dinta tayi a hankali ta shiga sannan ta rufe, gyaran gidan ta shiga yi, bayan ta tsaftace ko ina, ta
bude kofar kitchen xata xubda shara suka yi ido hudu da wata yarinya da ta xo xubda sharan ita ma, yarinyar ce ta fara cewa “Sannu” Khadijah tace “Ina
yini?” Yarinyar tace ” Lafiya lau, jiya da muka xo mun duba baki nan ashe kin dawo” Khadijah ta d’an yi murmushi tace “Ehh yanxu na dawo” yarinyar tace
“Ayya, to Sannu da xuwa” Khadijah tace “Idan na gama xan shigo yanxu” yarinyar tace “Toh sai kin shigo” daga haka Khadijah ta wuce ciki, Allah ma ya san ba
don ranta ya so ta fada haka ba, kawai dai yarinyar ta mata kwarjini ne, and kuma sai taga kamar suna kama, toh ko dai ita ce warce su Deejah ke fadi? Tabe
baki tayi ta wuce bedroom dinta, wanka tayi ta sauya kaya tayi sllhn azahar sannan ta linke Hijab dinta ta yafa mayafi ta fito, a hankali ta danna bell din
apartment din khaleel, bayan wani lkci wata ta bude kofar, Khadijah tace “Ina yini” yarinyar dake ta kallonta ta bata hanya tace “Lafiya lau” shigowa
parlorn Khadijah tayi gabanta na faduwa, few mutane ne parlorn kuma yawanci duk manya ne, ta durkusa jikin kujera a hankali tace “Ina yinin ku” amsa mata
suka yi da fara’a, wata a cikinsu tace “Ikon Allah, ji mai kama da su Maimoon” Yarinyar da ta bude kofar tace “Wllh Anty na xata Safeenah ce ta da farko,