NOOR AL HAYAT 71-80

haka na tsaya da mamaki Ina kallonta don nasan Safeenah na daki ai” Ita dai Khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Wata mata dake kusa da ita tace
“Dama haka Allah ke ikon sa ai, tashi ki shiga ciki yan mata suna can gaba daya” warce ta bude mata kofar ne ta kai ta har dakin da jawahir da yan uwanta
suke, Khadijah dai gabanta sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, da sallama ta shiga dakin bayan yarinyar ta bude mata kofa, suka hada ido da Jawahir dake
xaune gefen gado tana danna wayarta, sosai tayi kyau sai wani glowing chocolate skin din ta yake, hannayenta sun sha lalle, kai kana ganinta ka ga amarya,
Khadijah ta sunkuyar da kanta, Maryam ce ta fara mikewa ganinta tace “Lah Khadijah ashe kin dawo” Khadijah ta kirkiri murmushi tace “Ehh ban dade da dawowa
ba” Maryam tace “Ayya, Sannu da dawowa, ga waje ki xauna” Bata kai ga xama ba Deejah ta fito daga bayi tana ganinta ta rungume ta da murna tace “Khadijah
har na gaji da jiran ganin yaushe xa ki dawo, gashi babu mai number ki, Sannu da xuwa” Khadijah tace “Ayya ni ban san jiya xa ku taho ba ina gidan frnd dita
ce” A hankali Khadijah ta xauna Deejah ta xauna kusa da ita tana kallonta da fara’a tace “Mun taho rakiyar amarya” Khadijah ta kalli jawahir a hankali tace
“Sannu Amarya, Allah ya bada xaman lafiya” sai a sannan jawahir ta kara kallonta babu yabo babu fallasa tace “Ameen” Deejah sai kallon jawahir take alamar
bata ji dadin yanda ta amsa mata ba, ita kanta Maryam dauke kanta kawai tayi, Safeenah ta shigo dakin tace “Lahh ashe har kin shigo” Khadijah tayi murmushi
tace “Eh na shigo” ta karaso ta xauna ita ma tace “Su Anty Deejah na ta labarin ki a Nigeria sai gashi yau na gan ki, kin lura da kamar da muke yi kuwa?”
Dariya ta ba Khadijah, Maryam da Deejah ma suka yi dariya ban da Jawahir da ta tsuke fuska, A hankali Khadijah tace “Ikon Allah kenan” Safeenah tace
“Gaskiya ne, Ammin mu na gaishe ki” Khadijah tayi murmushi tace “Na amsa sosai” hira suka dinga yi dakin banda Khadijah da sai dai tayi murmushi idan sun
kallota, duk a takure take ta kagu ta tashi ta wuce amma ta kasa tashi, agogo ta kalla ganin uku ya wuce tayi karfin halin mikewa tace “Xan dan shiga ciki
ina aiki ne” Safeenah tace “Amma xa ki dawo ai?” Murmushi Khadijah tayi tace “Ehh xan dawo anjima” Rakota suka yi parlor, Khadijah tayi ma wa enda ke xaune
parlor sallama ta bude kofa xata fita suka kusa cin karo da khaleel, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yanda ta daburce shi ma haka, yyi saurin
bata hanya, ganin Deejah da Safeenah na bayanta tayi karfin halin ce masa “Ina yini” yace “Lafiya lau, ya gida” fita tayi daga parlorn bata ce komai ba ta
bude apartment dinta ta shiga ta rufe, ganin la’asar yayi ta daura alwala a bayi tayi sallah sannan ta kwanta, bude data tayi da sauri tunawa da tayi daxu
Barrister yace xai turo mata sako ta duba, ko ya bar Dubai din ma oho, ai ko tana budewa taga messages da ya turo mata da yawa, ta shiga tana kallon message
din, kusan gaba daya hotuna ne, downloading din su ta fara yi, murmushi tayi ganin set na akwatuna ne yace ta xabi wanda take so, a hankali ta dinga
scrolling tana duba boxes din, bbu na banxa gaba dayansu, murmushi tayi masa as reply, sannan ta tura masa message tace duk sun yi kyau sosai, daga haka ta
kashe datan ta, bayan kusan minti goma sai ga kiransa, kuri ta kura ma wayar ido, can ta daga a hankali ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren
yace “Amira” tace “Na’am good day” yace “Thanks, I saw ur reply, kuma ni ba tambayar ki nayi ko sun yi kyau ba” Yar dariya tayi tace “Barrister amma ai kai
ma kasan sun yi kyau” yace “My question is wanne kika fi so” tayi murmushi tace “Uhm ni ban san wanne xan ce ba barrister” yace “Ask ur frnds then” tace
“Toh xan tambaya” yace “Ina fa jiran ki kafin gobe, don goben xan bar Dubai” a hankali tace “Toh barrister” daga haka yayi mata sallama ya katse wayar ta
koma ta kwanta a sanyaye, juye juye ta dinga yi tana kokarin bata ba damuwar dake neman dirar mata a xuciya space ba, can ta mike jin ta fara jin yunwa,
kitchen ta tafi ta daura ruwan xafi don tafasa na shayi, kamar ance ta leka window taga khaleel xaune waje doing nothing, hada ido suka yi tayi saurin dauke
kanta ta ci gaba da abinda take, tasowa yayi a hankali ya iso kusa da windown ya tsaya yana kallonta, trying her best not to look toward his direction tace
“Wishing a happy married life, Allah bada xaman lafiya” kallonta kawai yake, can a hankali yace “Khadijah” kashe gas dinta tayi ba tare da ta kalli inda
yake ba ta nufi kofar fita kitchen din ya bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar. Shayin da bata sha ba kenan tana ta xaune parlor wayarta ya fara ring,
dauka tayi ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tayi shiru, “Ki fito muna waje” abinda Aliyu yace mata kenan, ta mike a hankali ta tafi daki ta dauko
hijab dinta ta sa ta fita, Tana isa kusa da motar ta bude ganin bashi da alamar fitowa ta fiddo Shureim tana kallonsa, xata wuce yace “Jira ki karbi sakon
Mumy” Bata ce komai ba ta tsaya ya fito ya bude bayan mota ya ciro wani leda ya bata, amsa tayi tace “Mun gode Allah saka da alkhairi” Har ta juya xata tafi
sai kuma ta tsaya tana kallonsa ta basa wayarta tace “Ka sa min number ta sai in kirata in mata godiya” karbar wayar yayi ya sa mata digit din Mumy ya mika
mata, ta amsa tace “Thanks” yace “Don’t forget ki tambayeta jikin Anty Khadijah idan Kin kirata” tace “Har yanxu bata samu sauki ba?” Yace “She is still at
the hospital” Shiru Khadijah tayi, lkci daya jikinta yayi sanyi, can tace “Toh Allah ya bata lafiya” Yace “Ameen” Cike da karfin hali tace “Ya jikin iklima
fa?” Ya shafa kansa yace “Tana can family din babanta, ban samu xuwa dubata ba coz I spent only three days kuma throughout Zaria nake ta tafiya gun Anty
Khadijah” Khadijah tace “Toh Allah ya sauwake, idan muka yi hutu soon xan je gida sae in je in duba Anty Khadijah da Umma” Yace “Alryt” shiru ta kara yi,
sai kuma ta kallesa tace “Ina son tambayar ka pls” yana kallonta ya rungume hannunsa yace “Ina jin ki”
✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Khadijah tace “Ya dangartakar ku da su Deejah?” Ya d’an yi shiru yana tunani kafin yace “Wacece Deejah kuma?” Ta kallesa tace “Deejah ce baka sani ba?”
Buda ido yyi yace “Ohh wai warce kika tarar gida ranan da na kai ki kike nufi, kawar Maryam” Khadijah tace “Ehh” yace “I think, noo they are just family
frnds kawai, Dad din Maryam da dad dinsu are just good frnds, childhood frnds if I am not mistaken, that’s just it” Khadijah tace “Toh Maryam fa?” Ya shafa
kansa yace “Her mum kanwar Abbana ce, dad dinta kuma was once under my dad, so Maryam is my cousin” Khadijah tace “Ohk” yana kallonta yace “But why did you
ask?” Wani kallo tayi masa tace “Is there anything wrong with me asking?” Murmushi yayi yace “Not at all, yaushe xa ku fara exams?” Tace “Nan da 3wks” yace
“Ohk Allah ya kai mu” tace “Ameen” daga haka ta kama hannun Shureim dake tsinkar flowers ta nufi cikin gida, Aliyu ya bi su da kallo Shureim na daga masa
hannu har suka shiga cikin gidan. Da daddare Khadijah na bedroom tana karatu bayan Shureim yayi bacci taji an danna bell, sosai gabanta ya fadi ta kalli