NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 71-80

agogo, a lokacin ma takwas yayi, ta mike a hankali ta isa gun kofar ta tsaya tace “Waye?” Jin muryar mace ta bude kofar, Safeenah ce tsaye bakin kofar tace 

“Khadijah I want to spend the nigh here if it’s ok by you” Khadijah tace “Oh you are welcm” daga haka ta bata hanya ta shigo parlorn tana cewa “Su Anty 

Deejah na takura ni shi sa na yo nan, da dare bai yi ba gidansu Maryam dama xan tafi” Khadijah tayi murmushi tace “To mu shiga ciki” bin bayanta Safeenah 

tayi har suka isa bedroom dinta, Safeenah na kallon Shureim dake bacci tace Woaw brothern ki ne wannan” Murmushi Khadijah tayi bata ce komai ba, can kuma 

tace “Ki hau saman gadon” Safeenah ta hau kan gadon xuwa daya side din tace “Hope baxan takura ku ba” Khadijah ta xauna gefen gadon tace “Haba dai ba wani 

takura” Safeenah tace “Kin san har na fara ba Abban mu labarin ki” Khadijah tayi dariya tace “Haba dai” Safeenah tace “Ehh mana, Ko mijin Jawahir Dr Ayman 

ya din ga kallona jiya da muka xo, da yake bai san ni ba dama tunda ba gida daya muke da jawahir ba, she is my cousin, My father and her mother are having 

same parent” Khadijah tace “Ayya that’s nyc” Safeenah tace “Ke karatu kawai ya kawo ki kasar nan kenan” Khadijah ta gyada kai tace “Na ma kusa gama wa” 

Safeenah tace “Ayya, a Nigeria wani state ku ke da parent din ki?” Khadijah tace “Kaduna” Safeenah ta gyada kai tace “Su jawahir ne ke kaduna mu a Abuja 

muke” Wayar Safeenah ya fara ring ta duba, mike tayi ta koma can karshen gado tace “Let me answer my call Khadijah” daga haka tayi picking call din, 

murmushi Khadijah tayi ta mike don dauko masu rigar sanyi, har ranta taji tana son Safeenah, she’s just free minded, daya side din gadon ta tafi ta kwanta 

bayan ta ajiye ma Safeenah rigar sanyin, ta lumshe ido nan da nan bacci ya dauke ta. Da asuba bayan sun idar da sllh Safeenah ta koma ta kwanta, Khadijah ta 

fita xuwa kitchen tana tunanin abinda xata yi na breakfast ta kai ma su Deejah, Irish tayi deciding ta soya da kwai ta dafa masu ruwan shayi don ita iyakar 

abinda take ci kenan gidan sai indomie ko shinkafa… Gaba daya cimar kasar bai dameta ba shi yasa ko siya bata yi, ta fi ga abincin Nigeria, har ta gama 

abinda take a kitchen Safeenah bacci take, daukan Shureim tayi ta fita daga dakin xuwa wani dakin tayi masa wanka ta dauko Uniform dinsa ta shiryasa ta sa 

masa kayan sanyin sa sannan ta basa Breakfast, wankan tayi ita ma kafin ya gama ta shirya cikin abaya ta yafa mayafinsa ganin da sauran lokaci yasa bata kai 

masu breakfast din ba ta tafi kai Shureim makaranta, tana dawowa ta tarar da Safeenah a parlor, Tace “Har kin tashi?” Safeenah tace “Wllh Dr Ayman ne ya 

tashe ni yanxu shi ya xo neman ki” Khadijah tace “Nema na kuma?” Safeenah tace “Noo xai fita ne yace xai yi dropping brother dinki a schl sai nace kilan kin 

je kai sa” Khadijah tace “Ayya ai daga can nake ma, akwai ruwan xafi bathroom idan xaki yi wanka” Safeenah ta mike tace “A’a bari in je can inyi tunda 

kayana na can din, dama jira nake ki dawo” daga haka ta nufi kofa Khadijah tace “Toh shkkn, Amma xa ki dawo?” Safeenah tayi dariya tace “Eh xan dawo” 

Khadijah tace “in bar maki breakfast din ki a nan kenan” Safeenah tace “Da safen nan fa xa mu wuce Khadijah” Khadijah tace “Da gaske” Safeenah tace “Ehh 

amma can gidansu Maryam xa mu je, Mum dinmu na can anjima da yamma sai mu dau hanyar Naija” Khadijah tace “Ayya to shikenan, idan na fito lectures da yamma 

kila in taho gidansu Maryam sai muyi sallama” Safeenah tace “Ba wani kila, kawai ki taho ku gaisa da Ammin mu tana can gidan ai, plss ki xo wllh ni dai ina 

son ki fa Khadijah I want us to be frnds” dariya Khadijah tayi tace “Toh in sha Allah xan xo” daga haka Safeenah ta wuce, Khadijah ta dau breakfast da ta 

masu a kitchen ta kai masu, a hankali ta bude kofar dake bude ta shiga parlorn, babu kowa parlorn sai ac dake kunne duk da sanyin garin, a hankali ta 

durkusa nan tsakiyar parlorn ta ajiye abubuwan hannunta, tana tunanin shiga daki wata xuciyar na ce mata kawai ta yi wucewarta idan sun fito xa su gani, har 

xata mike sai ga Khaleel ya fito, ya shigo parlorn yana kallonta, dai dai nan Safeenah ta fito daga daki ita ma ganin Khadijah tace “Yauwa Khadijah na bar 

wayata bedroom din ki” Khadijah ta mike da sauri tace “Lah to bari in dauko maki, dama xan taho da flask yanxu” Daga haka ta fita Khaleel ya dinga kallon 

safeenah da bata yarda ta kallesa ba tace “Ina kwana Doctor” yace “Lafiya lau” juyawa yayi ya wuce bedroom dinsa ya xauna kujera yana kallon jawahir da 

shigowar ta dakin kenan ita ma, atamfa ne jikinta ta yafe jikinta da mayafi tayi kyau sosai, a hankali tace “Ina kwana” yace “Lafiya qlau dear, I want to 

ask you something, shud i?” tana kallonsa tace “Ina jin ka” yace “Safeenah naji kamar ake kiran ta koh?” Jawahir na kallonsa tace “Ehh, what about her?” 

yace “Ya ku ke da ita pls?” Jawahir tace “She is my cousin sis, My mum and her father are having same parent, me ya faru?” Kallonta ya dinga yi kafin yace 

“Where do they stay?” Tace “Abuja” yace “Ohk sorry I’m asking this dear, bayan Dad din Safeenah, da Umman ku, da Uncle din ki na Lagos, akwai wasu kawun nan 

ki da ban sani ba ko aunt din ki? ta bangaren mumy fa nake tambayar ki” jawahir ta d’an yi shiru, sai kuma tace “Dama su biyar ne kawai gun maternal grand 

parent dina, kawun mu na Lagos ne babba, sai Abbansu Safeenah, sannan kawu Abdul, sai Ummata da kuma autarsu, but she is late, ta rasu” Khaleel dake ta 

kallonta yace “Since when?” Ta girgixa kai tace “I really don’t know don Umma tace min muna yara lokacin, she is always talking about her younger sis til 

date, seems tana sonta sosai” Khaleel na kallonta har lkcn yace “Kuma tayi aure kafin ta rasu?” Jawahir tace “Gaskiya ban sani ba” Khaleel ya dawo kusa da 

ita yace “Plss do me a favor of asking Umma to tell you more about her” da mamaki Jawahir ke kallonsa tace “But why?” Ya shafa kansa yace “Ke dai ki 

tambayar min ita plss wife” d’an murmushi tayi tace “Toh xan tambayar maka in sha Allah” yace “Yauwa nagode sosai” Khadijah na komawa apartment dinta ta 

dauko wayar Safeenah da flask na Lipton da ta dafa ta dawo apartment din Dr Ayman, har lkcn Safeenah na parlor tana jiranta, bayan ta karbi wayar tace 

“Thanks much Khadijah, baxa ki shigo ku gaisa da su Deejah da jawahir ba?” Khadijah tayi murmushi tace “Toh ina xuwa, xan dawo yanxu” daga haka ta fita, 

tana shiga apartment dinta jakar makarantar ta kawai ta dauka ta bar gidan don bata son sake jamming da khaleel, she just can’t withstand the sight of him. 

Kamar yanda tace ma Safeenah suna gama lectures karfe uku da yan mintuna ta tafi gidansu Maryam tunda ta mata alkawari, Hajiya Mariya taji dadin ganinta 

haka mahaifiyarsu Safeenah, Khadijah na ganinta ta ganeta don ita ce suka yi vid call kwanaki, Safeenah tace “Ammi kin ganta koh” Ammi tayi murmushi tace 

“Ae kam na ganta, ya iyayen naki Khadijah” Khadijah tace “suna lafiya…” Ammi tace “A kaduna ku ke da xama?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh” Hajiya Mariya 

tace “Ina Shureim din Khadijah?” Khadijah tace “Yana schl Mumy” shirye shiryen wucewa Airport suke, Khadijah dai na ta xaune parlor tare da Hajiya Mariya da 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button