NOOR AL HAYAT 71-80

kallon kyakkyawan yaron ya fito da shi ya mike, gyara rigar sanyi sa yyi still bai yarda ya kalli Khadijah da ta hade rai ba yace “Plss do u use salt?”
Khadijah na kallonsa tace “Meye shi?” Sai a sannan ya kalleta yace “Gishiri” sauke idonsa yyi daga kallonta, ta tabe baki kamar baxa ta ce komai ba sai kuma
can tace “I don’t know, let me check” daga haka ta juya a hankali ta koma ciki, Shureim yace “Uncle Aunt din nan tana nan” khaleel ya shafa kansa yana
kallonsa yace “Tana nan” Shureim yace “Ae yau tace xata bani puzzle irin na su fadil…” khaleel yace “Tana bacci yanxu, ka bari sai ka dawo school xata ba
ka” Shureim yace “Ohk can I tell her good morning now so as she will remember my puzzle?” khaleel ya duka yana kallonsa a hankali yace “No she is sleeping
son, idan ta tashi I will remind her for you” Shureim yace “Ohk tnx” Khadijah ta dawo rike da container din Gishiri ta mika masa, ya karba yace “Thanks I
will bring back the remaining now” Kamar jira take tace “Noo na ba ku” kallonta yayi da sauri yace “Noo ni xan yi amfani da shi ai” Wani kallo Khadijah tayi
masa tace “Did you hear me mention name?” Khaleel ya sauke idonsa daga kallonta, a hankali ya juya xai koma ciki sai kuma ya juyo da sauri yace “I am coming
inyi dropping dinsa a schl” Khadijah tace “Xan kai sa yanxu, you don’t worry” yana kallonta da kyau yace “I insist Khadijah” daga haka ya juya ya wuce ciki,
Khadijah tafi minti biyar tsaye a wajen can ta juya ta koma parlor ta xauna shureim ya biyo bayanta, tashi tayi daga parlorn gaba daya mood dinta ya canxa
ta kalli Shureim tace “Ka jira sa a nan” daga haka ta wuce bedroom ta kwanta, ta rasa dalilin da yasa ta ji tana son yin kuka, ta kife kanta da pillow
trying hard not to cry, ta fi minti goma a haka aka bude kofar dakin, Shureim ya shigo yace “Anty uncle yace in kira ki” A hankali ta mike xaune ta runtse
ido jin xuciyarta na mata xafi, ta kalli agogo taga takwas saura, da kyar ta tashi ta bi bayan Shureim, tsaye ta tadda khaleel parlorn har ta karaso cikin
parlorn bai yarda ya kalli inda take ba, ta tsaya tana kallonsa, kama hannun Shureim yayi yace “Plss Khadijah I need hot water, or rather lipton kafin in
dawo” daga haka ya fita tare da Shureim dake daga mata hannu ya rufe kofar, juyawa tayi ta koma daki tayi kwanciyar ta. Bayan kusan minti ashirin aka danna
bell, kin tashi tayi daga kwancen da take, Jin an sake dannawa ta daure ta dake, cike da karfin hali ta tashi ta fita, bude kofar tayi tana kallonsa, ledan
hannunsa ya mika mata yace “Drugs din Shureim naga he is having cold” karba tayi ba tare da ta kallesa ba tace “Thanks” daga haka ta juya xata wuce yace
“Khadijah ruwan lipton din fa?” K’in juyowa tayi tace “Ni bani da ruwan Lipton” daga haka ta rufe kofar ta, daki ta wuce ta fada kan hado tayi kukanta mai
isarta Kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ita kanta bata san me yasa take kukan ba, ta fi minti talatin kwance, ta mike a hankali jiki ba kwari daga
karshe ta fito parlor, kitchen ta shiga ta kunna gas ta daura ruwa ta xuba Lipton da kayan kamshi ta dawo parlor ta xauna, tana ta xaune parlorn har taji
alamar ruwan ya tafasa ta mike a hankali ta shiga kitchen din, cikin flask ta juye ruwan Lipton din gaba daya ta sa hijab ta fita, danna bell dinsa tayi,
tana ta tsaye bayan wani lkci ya bude kofar, Mika masa flask din tayi ba tare da ta kallesa ba tace “Yanxu na dafa” Ya karba a hankali yace “Thanks
Khadijah” Bata ce komai ba ta juya ta koma apartment dinta, sai kusan sha biyu ta fita gidan duk da karfe goma take da lectures, da wuri ta fito schl don
daukar Shureim ta samu har khaleel ya xo ya dauke sa, har ta fito wanka tayi sllh tana ta jiran ganin shigowar Shureim amma bai shigo ba, throughout ranan
babu wani abin kirki da ta ci kuma gaba daya taji bata jin yunwa, a hankali ta dau wayarta don kiran Barrister taji ko ya isa gida lafiya, har ya katse bai
dauka ba ta sake kiransa, nan ko yana xaune parlorn sa Little Meerah na jikinsa tana ta masa surutu da pure English dinta, Jiddah kuma na durkushe gabansa
tana xuba masa dafadukan taliya da ta dafa sanin ranan xai dawo, kallon taliyar kawai yake don he is not a fan of it kuma sarai tasan baya ci, ya girgixa
kai ya dauke kai daga abincin, ajiye serving spoon din hannunta tayi ganin alamar ana kiran wayarsa da ke jone a caji, ta mike ta nufi inda wayar yake, tana
isa ta dauka tana kallon screen din “Ameerah” sunan da ta gani kenan jikin screen din, ta dinga kallo xuciyarta na bugawa, picking call din tayi kafin ya
katse ta kai kunne tayi shiru Khadijah na jin an daga ba a ce komai ba tayi shiru ita ma don it’s unusual of him kuma tana jin muryar little Amira a wajen,
Kamar ance Sudais ya daga kai ya ga jiddah tsaye har lkcn wayar na kare kunnenta fuskar nan nata a murtuke, ajiye Amirah yyi kan kujera ya mike da sauri
yace “What’s that u are doing Jiddah?” Ba shiri Khadijah ta katse wayar ta ajiye ta tabe baki ta yi kwanciyar ta. Jiddah na masa wani kallo tace “Wato dai
da gaske aure kake shirin yi saboda baka da tsoron Allah ko Aliyu?” Ya warce wayarsa a hannunta yana mata wani kallo yace “Don’t you ever dare pick my call
again malama” daga haka ya bar parlorn ya wuce sama, Xaunawa gefen kujera Jiddah tayi lkci daya hawayen takaici ya shiga sakko mata, ai da ta sani kawai
guduwa daki tayi da wayar tayi pick din call din ta sussurfa ma shegiyar dake kiransa xagi, to Wai wacece wannan Amirar? Sai yanxu taji tana mugun son sanin
wacece ita, ta kalli Yar ta dake xaune tana kallon tv, lkci daya lkcn da ta haifeta ya dawo mata, ranan sunanta bayan ya sa sunan mahaifiyarsa babu yanda
bata yi da shi kan cewar da Khaleesat xata kirata ba yace inaaa bai san xance ba sai dai Amirah, da ta tambayesa me yasa sai ce mata yyi sunan wata frnd
dinsa mai muhimmanci a rayuwarsa ce kuma yana ji da ita sosai shi yasa xai kira ‘yar sa da haka…. Jiddah ta mike da sauri xuciyarta na bugawa ko dai ita
ce wannan mai kiran nasa yanxu, ita fa dama tun lkcn taji ta tsane koma wacece Amirar nan, shi yasa har yanxu da kyar take kiran Yar ta da Amirah, a bayan
idonsa dama kiri kiri Khadijah take ce mata, wayarta ta dauka ta shiga dakin da ke parlorn ta kulle kofa ta shiga neman number Dr Yusuf tasan duk yanda aka
yi baxai rasa sanin wacece Amira ba, bugu biyu ya daga bayan sun gaisa yana tsokanarta wai ta sa abokinsa ya mance shi gaba daya, ta xauna gefen gado tace
“Dr dama tambaya ce na kira in maka don Allah…” Dr Yusuf yace “Toh Ina ji, Allah sa na sani dai” tace “Uhm nasan ka ma sani, wllh in gaya maka abokin ka
ne duk ya ishe ni da wata Amira nayi nayi ya gaya min wacece ita ya ki, har cewa yayi idan na cinka wacece ita to xai bani kyautar mota, toh ni dai duk iya
tunani na rasa gane wacece amma na fi tunanin frnd dinsa ce kilan da yake ji da, shine yanxu na kira ka bani satar amsa, dama wllh motata ta isheni sabuwa
dal nake so, Kuma kasan barrister baya saba alkawari plss Dr ka taimaka” dariya sosai Yusuf yayi yace “Wai Amira?” Gabanta na mugun faduwa tace “Ita fa
Dr…” Yace “Yasan baxa ki taba sanin wacece ita ba, Kuma xancen gaskiya babu wani mota da yake da niyyar baki don yasan ko xa ki shekara kina naxari baxa