KannywoodLabaraiLilin BabaUmmi Rahab

An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Yayin da mutane suke ta jita-jita da surutai akan cewa ‘yan fim ba sa auren junan su, Lilin Baba da Ummi Rahab zasu karya wannan rantsuwar ta’yan fim ba sa auren juna, don yanzu haka an sanya ranar auren su.

A rana Juma’a, 4 ga watan Maris Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa batun sa ranar auren nasu.

An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Yanzu haka duk wasu shirye-shirye sun kankama akan cewa Lilin Baba zai angwance da amaryarsa, Ummi Rahab bayan sallah mai zuwa.

Tashar Tsakar Gida ta samu labari akan cewa manyan jarumai kamar Ali Nuhu ne suka shige wa mawakin gaba akan neman auren auren Ummi kuma an ba su auren ta.

Ba don wani akasi da aka samu ba da tuni an daura auren kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta tattauna da daya daga cikin waliyyan amarya, Yasir Ahmad wanda ya tabbatar da cewa za a daura auren bayan sallah.

Baya ga hakan, akwai wani bidiyo da jaruma Umma Shehu ta wallafa wanda ya kara tabbatar da hakan wanda aka ga Lilin Baba da Amaryar tasa cike da farin ciki, a karkashi ta sanya “our next couple”.

Daga LabarunHausa

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button