Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 22

Kashe Ac din dakin Aunty tayi ta sauke curtains ta dawo ta xauna kusa da shi tace “Sannu, ko dai a kira Dr? amma daga ina kake haka?” Girgixa mata kai kawai yayi don bai jin ma xai iya magana, ta mike ta fita don daukan wayarta ta kira Dr din, Tana cikin dialing number likitan ta kalli Ummi tace “Baya jin dadi ne wllh” Ummi tace “Ikon Allah, to Allah ya sauwake” Aunty na gama kiran likitan ta koma daki….. Abu kamar wasa Abuturrab har da karin ruwa, he was so weak and sick, sae bayan isha family Dr din nasu ya bar gidan. Karfe goma da yan mintuna wayar Abuturrab dake gaban mirror din dakin Aunty ya fara ring Aunty ta dau wayar ganin Ahmad ne ta kyabe baki ta dauka don tun daxu yake kira, bayan ya gaisheta yace “Ya tashi Aunty?” A takaice tace “Aa….. ko minti sha biyar ban yi da fitowa daga dakin ba” Ahmad ya d’an yi shiru sannan yace “Amma jikin da sauki?” Tace “Eh toh amma har yanxu his temperature is high” Yace “Toh Allah ya sauwake, likitan ya tafi?” Aunty tace “Ehh” Yace “Toh Allah ya bashi lafiya” Aunty tace “Ameen” daga yayi mata sallama ya katse wayar, Aunty ta ajiye wayar ta koma bangaren Abuturrab ta bude kofar dakinsa, tsaye taga Ummi a dakin kusa da shi tana kallonsa, Aunty tace “Ya tashi ne?” Ummi ta juyo tace “Aa” Aunty ta karasa kusa da shi ta xauna ta sauke duvet din tana kallonsa ta kai hannu goshinsa, taji har sannan da xafi, juyawa Ummi tayi ta fita daga dakin… a hankali Abuturrab ya bude idonsa da yayi masa nauyi sbda ciwon kai, ji yake kamar ana sara masa goshinsa, Aunty tace “Sannu son, ya jikin?” Bai iya ya bata amsa ba ya sake lumshe ido, tace “Baka ci komai ba, in hado maka shayi?” Girgixa mata kai yayi, bai sake bude idonsa ba har ta ga alamar ya koma bacci, ta mike ta fita daga dakin ta kulle masa kofar. Can cikin dare Abuturrab ya farka, da kyar ya mike xaune coz he was pressed, ko hasken fitilan dakin bai so don kara masa ciwon kai yake yi, ya kalli drip din hannunsa da ya kusa rabi, ya mike tsaye da kyar yana jin jiri ya kashe ruwan ya bar cannula din kadai a hannunsa bayan yyi disconnecting dinsa daga jikin ruwan, kamar me counting steps dinsa ya nufi bandaki ya shiga duk da jirin da yake ji, da alwalansa ya fito ya xauna gefen gado ya dafe kansa, ko kadan bai son tuna komai da ya faru yau, it’s making him down and weak, Bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo ya daga kai da sauri, tace “Ka tashi Abuturrab, sannu ya jikin” A hankali yace “Alhmdlh” Ta karasa kusa da shi tana dialing number Ahmad don kiransa ne ma ya tasheta yana fara ring tace “Duk abokinka ya takurani gashi nan ni dai” Tana fadin haka ta mika ma Abuturrab wayar, ya amsa ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Ahmad yace “How are you feeling captain?” Cikin sanyin murya yace “Alhmdlh” Ahmad yace “Ka samu ka ci wani abun kuwa?” Abuturrab yace “I will take tea now” Ahmad yace “Do so plss, Dr Shariff din ya baka drugs ne?” Abuturrab yace “I just woke up ban sani ba” Ahmad yace “Ohk, ruwan yayi rabi yanxu?” Abuturrab ya kalli drip din sannan yace “Almost” Ahmad yace “Toh Allah ya sauwake” Abuturrab yace “Ameen” sallama Ahmad yyi masa ya katse wayar, ba a dau lkci ba Aunty ta dawo dakin rike da cup din tea ta mika ma Abuturrab tace “Gashi ka samu ka sha” Ba musu ya amsa, tana nan tsaye sai da ta tabbatar ya sha shayin sannan ta amshi cup din ta fita, Mikewa yayi ya koma bathroom ya wanke bakinsa ya fito ya dau pray mat ya shimfida ya hau sannan ya tada sllh, ko da Aunty ta dawo dakin ganin yana sallah ta koma dakinta, ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike a hankali ya dauke darduman ya koma kan gado, mayar da ruwan yyi ya kashe wuta ya kwanta ya lullube jikinsa yana jin kamar wani sabon xaxxabin xai sake rufesa. Da asuba duk yanda Abuturrab ya so tashi yin sllh kasawa yyi, Karfe shidda da yan mintuna Aunty ta shigo dakin, ta kunna wuta ta karasa gun gadon ta cire duvet din da ya rufe har kansa da shi, bude ido yyi a hankali, tace “Ka samu kayi sallah kuwa?” Girgixa mata kai yayi, tace “Da ka daure ka tashi, amma how are you feeling now?” A hankali yace “Alhamdulillah” mikewa yyi xaune, tace “Let me get u something to take sai ka sha magungunan idan ka idar da sallahn” Fita tayi dakin, yayi karfin halin tashi ya cire ruwan da ya rage kiris ya kare sannan ya shiga bandaki, yana sallah ta dawo dakin, ta ajiye masa cup din shayi da ledan drugs din ta nemi waje ta xauna har ya idar da sallahn sannan ta sa ya dau shayin da ta hada masa ya sha…. Karfe goma na safen Abuturrab na bedroom dinsa hannunsa rike da bowl din pepper soup, Ummi ce tsaye dakin tana kallonsa, ko minti biyar ba ayi da fitan family Dr dinsu daga dakin ba, bayan few minutes ya d’an kalli Ummin tasa, ji yayi gabansa ya fadi sosai, a hankali yace “Why don’t u sit Ummi?” Ummi tace “Am okay here” Ba tare da ya kalleta ba yace “Aunty fa?” Tace “She is in the kitchen” Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din hannunsa a hankali, Ummi tace “Kun yi magana da Abban naka? Ya kira kana bacci daxu” Ya gyada kai yace “Ehh Aunty ta bani mun yi waya” Tace “Ohk” Juyawa tayi ta fita dakin ya bi ta da kallo, lkci daya jikinsa yyi sanyi, ya ajiye bowl din hannunsa ya jingina da gadon da yake xaune, he needs someone to talk to about this unfavorable issue, he needs to share this with someone that’s understandable, who will this be, rike kansa yayi yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…. Xuwa yamma Abuturrab ya d’an samu saukin ciwon kan dake damunsa, ya fito wanka kenan yana goge kansa da karamin towel din hannunsa aka bude kofar dakin, Ahmad ne ya shigo dakin hade da sallama, ganin Abuturrab a tsaye, ya tsaya daga bakin kofar ya rike waist dinsa yace “This is better, and I’m glad i saw u this way” Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad ya d’an yi murmushi yace “Medical report dae ya xama na gaske yanxu kenan” Abuturrab ya kallesa yace “Ka taho min dashi?” Ahmad ya karasa ya xauna gefen gado yace “How are you feeling now?” Abuturrab ya nufi gaban mirror a hankali yace “Alhamdulillah” Ahmad yace “But dama baka jin dadi ne, coz naga sickness din yyi striking dinka so hard, you look lean….” Ta madubi Abuturrab ke kallonsa bai ce komai ba, Ahmad yace “Ba shiru xaka min ba, i left my work for ur sake na biyo train” Abuturrab yace “Da baka dawo ba ma ni xan kiraka ka dawo, i have been expecting you” Ahmad yace “Hope you are feeling much better now?” A hankali Abuturrab yace “Not at all…. We need to talk Ahmad” Keenly Ahmad ke kallonsa cause he can see how worried and confuse he looks, Mikewa Ahmad yyi ya karasa kusa da shi yace “Tell me what’s wrong Captain?” Kasa ce masa komai Abuturrab yayi, Ahmad ya koma ya xauna yace “To ka gama shiryawa mu yi magana” Yana kallon Abuturrab har ya gama shiryawa ya dawo ya xauna gefen gadon shi ma, Ahmad yace “Me ke faruwa tell me” Abuturrab ya shafa kansa a hankali kamar me tunanin ta inda xai fara, bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo rike da bowl din fruit salad biyu, murmushi tayi ganin Abuturrab tace “Alhmdlh, son jiki yayi kyau, you are looking much much better and healthier now” Abuturrab yyi murmushin karfin hali bai dai ce komai ba, ta karasa ta mika masa Bowl daya na fruit salad din tace “I made this for u” Amsa yayi yace “Thank you Aunty” Kujeran dakin ta xauna tana shan fruit salad din daya bowl din hannunta tace “Abbanku ma ya kara kira yanxu nace da sauki, shi ma duk ya damu” Ahmad da ya d’an hade rai yace “Ina yini…” Ba tare da ta kallesa ba tace “Lafiya lau” magana ta ci gaba da yi da Abuturrab dake shan fruit din hannunsa, Ahmad ya mike yace “Alright Captain, sai ka xo can gidan namu, i will be leaving now” Abuturrab ya kallesa da sauri, ta gefen ido Aunty ta harari Ahmad tana ci gaba da shan fruits salad dinta, Abuturrab yace “Ai nace maka nima xan fita Ina son in sha iskan waje” Ahmad yace “Okay ka sameni mota idan ka gama, i will wait” daga haka yace ma Aunty “Sai anjima” ko tankasa bata yi ba har ya fita ya kulle kofar dakin, Aunty tace “Yaushe har ka farfado xaka wani fita Abuturrab? Shi Ahmad din bashi da hankali ne ko don ya xo lkcn da jikinka yayi kyau, kana fama da kanka ina wani fita idan ba neman magana ba?” Abuturrab ya shafa kansa yace “Aunty na gaji da xaman gidan ne, ni nace masa mu fita, ba shi ba” Ta tabe baki tace “Toh ai shkkn….” Bayan kusan minti ashirin Abuturrab ya fita xuwa gun Ahmad bayan ya sanar ma Ummi xai je gidansu Ahmad din, Sbda yanda idonsa ya fada yasa shi saka bak’in spec dinsa, kananun kaya ne jikinsa wani sanyayyen kamshi na tashi jikinsa, kana ganinsa kasan he is still recovering, he still looks weak, Kallonsa kawai Ahmad yake yi har ya karaso ya shiga front seat, Ahmad na kallonsa da d’an damuwa yace “Wai malaria ne ya kamaka haka Captain, ka rame fa, kamar wanda yayi sati a kwance” Captain bai ce masa komai ba, Ahmad ya tada motar suka bar layin. Karfe biyar da few minutes suka isa gidansu Ahmad, Abuturrab yace “Ka bar motar a waje ba dadewa xan yi ba xaka maida ni gida ynxu” Hakan yasa Ahmad yyi parking a waje, Abuturrab ya bude motar ya sauka ya nufi cikin compound din, Ahmad ma ya sauka ya rufe motarsa ya bi bayansa, sosai gaban Abuturrab ya fadi bayan ya shiga compound din sun yi ido hudu da Jiddah dake tsaye ta jingina da bango a bakin tap din dake cikin compound din ta tara bucket…..

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button