Abuturrab ya dauke idonsa hade da daure fuska yana tafiya, murya can kasa Jiddah tace “Ina yini” Bai kara kallon inda take ba balle ya tanka ta, tafiyarsa kawai yake kamar bai ji ta ba, Ta kalli Ahmad da ya shigo compound din shi ma, ta sauke idonta tace “Ina yini?” Murmushi yayi yace “Lafiya lau, sannu da aiki” Juyawa tayi tana kallon ruwan da take jiran ya cika, Ahmad ya bi bayan Abuturrab da har ya kusa main entrance din gidan, babu kowa parlon da Ahmad ya shiga sai kamshin girki dake tashi alamar ana girki a kitchen, bedroom dinsa ya nufa ya tadda Abuturrab a kwance idonsa a lumshe, ya karasa ciki ya kulle kofar yana kallonsa yace “Are you alright?” A hankali Abuturrab ya bude idon sae dai bai ce komai ba, cike da karfin hali ya mike xaune looking so dumbfounded, Ahmad ya xauna yana facing dinsa with seriousness yace “Tell me what is happening Captain, you look disturbed” Abuturrab ya shafa kansa ya lumshe ido wishing all this nonsense would turn out to be a dream, kara bude ido yyi, gathering much courage yace “I am in trouble Ahmad” Tuni yanayin Ahmad ya sauya, ya kafe sa da ido, can yace “Tell me what is it, me ya faru??” Cikin sanyi Abuturrab yace “Yes i will, amma kuma mafita nake nema a wajenka don Allah, and this should be a secret between just i and you for now plsss” Shi dai Ahmad kallonsa kawai yake waiting to here what is this that’s weighing down his frnd har haka, Abuturrab yayi kasa da murya da kyar ya fara magna yace “Yarinyar da kake siyan awara wajenta a hayi, u remember her right?” Bude ido Ahmad yyi sosai yana kallonsa yana jiran jin abinda ya sameta, A hankali Abuturrab ya shiga basa labarin tun daga xuwansa siya ma Umma awara sanda bata da lafiya, abinda ya faru a ranan, har ixuwa yanxu da suke xaune tare da Ahmad a daki, Abuturrab ya share xufan goshinsa yana kallon Ahmad da ya bude baki for almost five minutes now ya kasa rufewa, Abuturrab ya hade rai yace “Don Allah ka daina kallona haka Ahmad ka bani mafita, find a way out for me, i am stuck, ban ta6a shiga rudani iya rayuwata kamar na wannan lokacin ba, what have i done to my self daga taimako??” Sae a sannan Ahmad ya kulle bakin da sauri, wato kawai sae yake ganin labarin da Abuturrab ya basa kamar tatsuniya, or is he dreaming?? Ya kifta ido kusan sau hudu sannan ya kafe Abuturrab da ido, he is finding it hard to believe all what Abuturrab said now, as if counting his words yace “Wait Captain… Wllh kamar fa ban fahimce wannan gajeran labarin nan naka ba, i am confus….” Captain yyi tapping dinsa on a serious note yace “You just have to believe all what i said, duk abinda na gaya maka hakan yake stop confusing ur self” Ahmad na nunasa da yatsa cikin wani expression yace “Are you for real Aliyu??” Abuturrab ya kafe sa da ido regretting everything from the start, Ahmad ya buda ido sosai yana kara digesting din lamarin with shock, he knows Abuturrab have a soft heart, a very soft heart kuwa, yana damuwa sosai da matsalan da ba tasa ba, he prioritized damuwar wasu kan nasa, but he never thought ya kai wannan extent din, bai ta6a tunanin Abuturrab can go this deep ba, what is baffling him more is yanda this time around taimakon nasa yyi sa ga talaka sosai, don Ahmad bai ta6a ganin yayi stressing kan lamarin local people ba, tsakaninsa da su sadaka if the need arize, babu wani magana me tsayi dake hadasa da su, Abuturrab ya hade rai ganin irin kallon da Ahmad ke masa yace “Nayi kuskuren gaya maka damuwata ne da ya sa ka min shiru Ahmad? Don’t u have anything to say to me pls?” Lkci daya yanayin Abuturrab ya kara sauyawa gaba daya, sai yake jin wani sabon xaxxabi xai rufesa, da kyar Ahmad na nunasa yace “You mean you are married now without our knowledge Captain??” Cakumosa Abuturrab yyi a fusace yana huci yace “Wannan kake kira da aure? Haka ake auren dama? Mahaukaci ne ni da xan amince nayi aure yanxu” Ahmad yyi iya kokarin ganin bai yi dariyar da ya taho masa ba ganin how furious Abuturrab was, Turasa Abuturrab yyi ya mike yana jin xufa na keto masa yace “Ka gaya min meye abun yi ynxu, i have never been this confused all my life, what have i done to my self, taimako fa kawai nayi kokarin yi….” Lkci daya idonsa ya kada ya dawo ya xauna ya rike kansa, Wani tausayinsa Ahmad ya ji har ransa, hakan yasa kawai ya kawar da dariyar dake cin sa gaba daya a xuciyarsa, ya kwantar da murya yace “let’s talk brother” Abuturrab ya dago da idanuwansa da suka yi ja yana kallonsa, Ahmad yyi shiru yana tunanin yanda Abuturrab yayi making fool out of him, ko da wasa bai ta6a gaya masa abinda yake yi ba sai da abu ya 6aci, har da raina masa wayo wai shu murhu yake gani a hayi, wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke yyi kasa da murya yace “before i say anything just tell me what u have in mind now about this issue?” A hankali Abuturrab ya kai hannu aljihunsa ya fiddo farar takarda da biro yana kallon Ahmad, Ahmad ya buda ido sosai, lkci daya ya girgixa kai yace “Nooo…. This isn’t a solution, idan ka rubuta takardan nan dole gida xata koma ga axxalumar step mum dinta, kaga anyi ba ayi ba kenan, and at the end wannan mahaukacin kilan yace sae ya aureta…” Abuturrab yace “But I can’t sleep in peace again today in har ina tuna auren warce ke kaina, baxan ta6a samun nutsuwa ba matsawar ban aiwatar da haka ba, me of all people fa?? Where will i start from with that girl, me xanyi da ita a rayuwata?? Ko a mai aiki wllh wllh wllh baxan yi employ dinta ba, baxan bata aiki ba a gida na dai, western education zero, islamic education zero, wayewa zero, tsafta zero, mu’amalat zero, kyau zero…. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Ahmad dake ta kallonsa bbu ko kiftawa ya girgixa kai yana d’an murmushi yace “A bangaren kyau kuma ka so kanka Captain….” a mugun fusace Abuturrab ya fixgosa yace “What the heck…. Kyau xan ci?? Tsaftar fa?? Ilimin fa?? Wait wai kai Ahmad kana tunanin no matter what xan iya xama da local yarinyar nan a matsayin matata? Noo plss… God forbid, this is more like an abomination to me, idan na sake kwana da auren yarinyar nan a kaina yau wllh nasan gobe xan iya xarewa a wuce dani psychiatry” Ahmad ya lumshe ido ya bude yace “Duk na fahimce ka, amma idan ka saketa ynxu Captain ka gaya min meye makomarta? Ina kake son taje? Kasan xamanta tare da maigadin gidan nan da matarsa ba abu bane da xai ja lkci coz daki daya ne da su” Abuturrab ya lumshe ido ya bude yace “I don’t care anymore, saninta da tausayinta ne duk ya ja min plight da nake ciki ynxu…” Ahmad yace “Ohk Now tell me, after the divorce what next, ya xa kayi da lamarinta? Kaga tamkar ka lalata aikin ladan da kayi ne daga farko har karshe” Abuturrab na masa wani kallo yace “What are you insinuating now? Kar in saketa kake nufi ko me?” Ahmad ya daga hannu da sauri yace “Aa ni bance haka ba” Abuturrab ya ja wani tsaki yace “Xan saketa, kuma xan ci gaba da mata taimakon da nayi niyya” Ahmad yace “Good, ta yaya?” Abuturrab yace “Under my roof” Ahmad yace “Elaborate plss” Abuturrab yace “I’m thinking i will have no choice but to explain everything that transpired to my Dad, xan ma Abbana bayanin komai, xan kuma kai sa har gun me anguwan, i don’t want to look foolish, you get? Then he can explain everything to Ummi coz ni baxan iya ba….” Ahmad ya katse sa yace “You are confusing me, kai da kake da intention sakinta yanxu me xai kai magana kuma kunnen Abba?” Abuturrab yace “Don nace xan saketa ba yana nufin ai baxan yi duk abinda nayi niyya a kanta ba, wllh xan saketa without anyone’s knowledge, daga ni sai kai ne xa mu san babu aure tsakanina da ita, amma she will be under my care xan kula da ita har sanda xata samu me aurenta” Ahmad da ke ta kallonsa baki bude yace “Under ur care as how?? a gidanku xaka ajiyeta kenan?” Abuturrab ya girgixa kai yace “A gidana dai” Wani tsaki Ahmad ya ja yace “See the way u are talking like an illiterate plss, ba matarka ba ba komai ba xaka ajiye a gidanka kuna rayuwa tare Captain, ko dai nine ban fahimce abinda kake nufi ba, ka min bayani yanda xan gane” Abuturrab ya masa wani kallo yace “Toh me xamanta a gidana xai kara ko xai rage? Did i look like someone that have anything to do with that girl? Haba Ahmad, don dai ta kwana ta tashi tayi girki ta ci abinci ta tafi boko ko islamiyya, xamanta a gidan nan da rashin xamanta duk daya to me, Monday to Friday ina gun aiki, na dawo sunday and Saturday, wait tell me what u have in mind first” Ahmad yace “Gaskiya baxan yarda da wannan rashin tunanin ba, kana cikakken namiji ka xauna gida daya da mace….” Mikewa Abuturrab yyi looking super angry yace “Amma ka gama da ni Ahmad, mace me tsafta iya tsafta ina xulumi da tunanin yanda xanyi tarayya da ita balle wannan, haba.. haba wannan xagina kayi wllh, ta ina xan fara abinda kake tunani, did you know who i am kuwa Ahmad, me xanyi da warce tayi tsaftar yarinyar nan sau biyar ma balle ita” wani kallo kawai Ahmad ke yi masa Abuturrab yace “You just insulted me wllh, and i am seriously not happy about it” Ahmad ya tabe baki ya ki basa amsa, Abuturrab yace “Sabida wannan kaddaran da ya fada min ma dole nan da lkci ba mai tsayi ba in auri Aneesah” Ahmad yace “Sai ka ajiye su gida daya kenan?” Abuturrab yace “Yes, kaga Aneesah ta samu me taimakonta aikace aikace kenan” Ahmad yace “Gaskiya ne wannan, to yanxu abinda nake son sani shine, idan ka rubuta takardan ba yarinyar xaka yi kenan ko ko ya xaka yi?” Abuturrab yace “I will do the rightful thing, giving her or not giving her” Ahmad yace “To su kuma can iyayen nata xaka bari su san tana wajenka?” Abuturrab yace “There is no need, idan ta samu ‘yan cin kanta xata je garesu watarana” Ahmad ya sauke ajiyar xuciya. Karasawa Abuturrab yyi jikin window yana kallon waje, Ahmad dai sae kallonsa yake, shi har sannan ganin lamarin yake kamar a film, abinda ya fi daure masa kai yanda Abuturrab ya boye masa komai from beginning sae ynxu da abu ya baci, murmushi yyi yana gyada kai yana tunanin irin dariya da tsokanar da xae fara yi ma Abuturrab idan hankalinsa ya kwanta, sae dae deep down him he is so Happy for this young girl don yasan Abuturrab baxae ta6a cutarta ba, with him her future is super bright, komai na rayuwa baxai ji kyashin yi mata ba, maganar sakin da Abuturrab yyi ne kadai bai ji dadi ba har cikin ransa. Ana kiran magrib suka fita tare xuwa masallaci bayan sun yi alwala, Jiddah ce kadai xaune tsakar gida da buta a gabanta, tunda ta hangosu daga nisa tayi kasa da kanta tana alwalanta,, Kallonta kawai Ahmad ke yi yana mamakin yanda ita da gogan suka iya pretending, ko da wasa bata ta6a nuna masa ta san sa ba, murmushi kawai yake yi yana kara jinjina wannan lamari me abun mamaki, Abuturrab dai ko kallon inda take bai yi ba har ya fita gate din, Ahmad yyi murmushi ya bi bayansa, shi dai ya san ko giyar wake Abuturrab ya sha baxai yi accepting yarinyar nan matsayin matarsa ba, bayan an idar da sallah sun fito masallaci Ahmad na kallon Abuturrab yace “She isn’t comfortable staying with the gate man and his wife, may be because daki daya ne, kaga baxai yiwu suna ciki tana ciki ba shi yasa take yawan xaman waje, na lura da hakan” Abuturrab bai ce masa komai ba har suka shiga compound din, sae a sannan yace “Idan na gaida Umma xaka saukeni gida yanxu” Suna bude kofar parlon Abuturrab yyi ido hudu da jiddah tana tsaye daga kusa da kofan parlon, sunkuyar da kanta tayi ta koma gefe cikin sanyin murya tace “Ina yini” Bai ce komai ba ya karasa cikin parlon, Ahmad ya sakar mata murmushi yace “Ki karasa ciki mana, kin tsaya a bakin kofa” Tana jan yatsunta tace “Abinci xan amsa inji Maman Abdallah” Ahmad yace “Toh ki karasa ciki” Ta d’an karasa amma ba can cikin parlon ba tace “Na gaya ma Aunty Huraira tace toh” Umma ce ta fito kitchen ganin jiddah tace “Yau ma jikin kofar kika makale Jiddah?” Jiddah ta sunkuyar da kanta, Umma tace “Ma su sunan ki kuwa suna da sakin jiki ke ban san ya haka ba” Ahmad yace “Bakuwa ku ka yi gidan Umma” Umma tace “Ehh bakuwar Amina ce, gashi har yau taki sakewa” Ahmad ya kalleta yana murmushi yace “Ya sunanki?” A hankali tace “Jiddah” tausayinta Ahmad ya ji har cikin ransa, without allowing that to show… ya buda ido yace “Lahh Ummin Captain ce ashe” Umma tayi murmushi tace “Kai ba Umminka bace kenan?” Ahmad ya shafa kansa yana murmushi ya kalli Abuturrab da ya hade rai kamar bai ta6a dariya ba yana kallon TV, yace “Captain ga mai sunan Ummin mu fa” Umma na kallon Jiddah tace “Karasa kitchen din ki ga ko ta gama xuba maki, kinji” Kitchen din Jiddah ta nufa ta shiga ciki, Abuturrab ya gaida Umma a hankali, amsawa tayi da murmushi tace “Alhmdlh jiki yayi sauki kenan, ai daxu da muka je kana bacci” D’an murmushin karfin hali yayi yace “Naji sauki Umma” Tace “Toh Allah ya kara lafiya Son, bari a kawo maku abinci yanxu” A nan parlon ta barsa shi da Ahmad, Jiddah ta fito rike da abinci, bata yadda ta kallesu ba ta nufi kofa kamar mara gaskiya ta fita… Washegari Thursday karfe tara da yan mintuna Abuturrab ya fito daga bedroom dinsa, Bangaren Abbansa ya nufa, sai da ya bude kofar parlon Abbansa yace “Alhmdlh…. Much better now” sisters dinsa ne xaune parlon suna masa ya jiki kamar baxai amsa ba kuma bayan ya isa bakin kofar parlon Abbansu ya amsa sannan ya shiga parlon da sallama, Aunty ce tare da Abba a parlon, tun da ya shigo Abbansa ke kallonsa, ya xauna kasan carpet yace “Sannu da dawowa Abba” Abba yace “How are you feeling now?” A hankali yace “Alhmdlh na ji sauki” Abba yace “Allah ya kara lafiya” Aunty tace “Jiki kam Alhmdlh, kamar ba shi ba shekaranjiya” Abba na kallonsa yace “Kana stressing kanka da yawa ko, you look stressed out” Abuturrab ya girgixa kai yace “Aa Abba” Aunty tace “Kamata yayi ka dau hutun ko da sati biyu ne ka huta har ka murmure gaba daya, you look so lean” Shi dai Abuturrab murmushi kawai yayi bai ce komai ba, Aunty ta mike ta nufi kofa bayan ta dau tray din da ta kawo ma Abba shayi ta fita, Abba na kallon Abuturrab yace “Hope babu damuwa Aliyu?” A hankali Abuturrab yace “Akwai Abba” Da mamaki Abba ke kallonsa, kafin yace “Talk to me, meye damuwar” Abuturrab ya kallesa lkci daya jikinsa yayi sanyi, cikin sanyin murya yace “Abba i did something….” Sai kuma yayi shiru, Abba ya ajiye cup din hannunsa yana kallonsa da kyau yace “Feel free son, tell me what happened” Abuturrab ya sunkuyar da kansa nan ya sanar ma Abbansa komai tun daga farko, bai boye masa komai ba, Abba couldn’t stop looking at him da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, Abuturrab ya xauna kan kneels dinsa a hankali feeling so remorseful yace “Kayi hakuri Abba, i neva thought things will turn out that way da ban yi komai gaban kaina ba, ban san haka lamarin xai kasance ba, i am sorry father, I don’t know if this means failing you, kayi hakuri Abba…” Abba ya dafa shoulder dinsa ya sauke ajiyar xuciya amma kuma ya rasa ma abinda xai ce masa, da alama ya girgixa sosai da batun shi ma, Abuturrab yace “Xan iya kai ka gun mai anguwan ma so u can believe me 100%, ban ta6a xaton haka abubuwan xa su tafi ba da ban yi ba” Abba ya kara sauke wani ajiyar xuciya yace “Ikon Allah, to Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ka Aliyu, but this is astounding…” Abuturrab yayi shiru bai ce komai ba, Abba ya dinga pondering kan lamarin, sai yake ganin abun kamar a mafarki, his son getting married babu shi, babu yan uwansa, infact unprepared marriage, hakan bai ta6a faruwa a xuri’arsu ba kaf” Abuturrab ya katse ma Abba tunaninsa ta hanyar cewa “Amma xan saketa Abba” Da sauri Abba ya kallesa yace “Why? Ba saboda ka taimaketa ka aikata hakan ba, xaka saketa saboda me kuma?” Da mamaki Abuturrab ke kallon Abbansa, can yace “Abba amma ai ni baxan iya xama da ita as a wife ba, i just can’t Abba, she is not my class” Abba ya dinga kallonsa, Can ya girgixa kai yace “Dole hakan xaka xauna da ita kuwa, before making the decision of marrying her ai ya kamata ka fara naxarin ko xaka iya xama da ita din as wife or not, ka saki yarinya for what reason, i thought it’s ur decision? Ko ka dau aure abun wasa ne, ka xata film ku ka yi acting a wajen ranan, ko kuma wasan yara ku ka yi?” Abuturrab ya marairaice hankalinsa a mugun tashe yace “Abba wllh kawai don in taimaketa a wannan moment din ne yasa na amince da auren ba wani abu ba, naga xa ayi ruining rayuwarta ne yasa na amince Abba, amma kuma nayi niyyar sakinta ai bayan daura auren” Abba na masa wani kallo on a serious note yace “Erase that harebrained idea right away, babu wani sakinta da xaka yi, tunda har aka daura auren shaidu duk sun shaida ka bada sadaki, babu wani abinda ya rage illa kayi accepting fact din ka tare da matarka, kada in sake jin ka yi xancen saki, ba drama ko film din Hausa kuka yi acting ba a wajen” Da mugun mamaki Abuturrab ke kallon Abban nasa baki bude, sanin arguing further won’t favor him yasa yayi shiru, but deep down him yasan in har yana son ci gaba da rayuwarsa yanda yake yi a da to sai ya datse igiyar yarinyar nan a kansa, idan bai saketa ba he will never have peace of mind, he might even turn a Sadist, sakinta kuma da xai yi babu wanda xai bari ya sani, they will stay in the same roof but not as husband and wife, muryar Abbansa ya ji yana cewa “Sai ka karasa gyara gidanka na nan garin ku tare, i will call all my brothers and inform them what happened, since u chose this for ur self” Abuturrab ya ji kamar yayi kuka sanin in har cousins da frnds dinsa suka ga cewar wannan yarinyar ce matarsa ai tasa ta kare kuma, he don’t even want to imagine how they will make jest of him and even laugh at him, yayi narai narai da ido ya marairaice yace “Abba don girman Allah ba sai ka gaya ma kowa wannan abun ba pls I’m begging you Dad” Dariya ya kusa ba ma Abban nasa ganin yanda ya marairaice, wanda he couldn’t help it but laugh, duk da kasancewarsa musulmin kwarai sannan dattijon kwarai ne kadai ya sa ya saduda yayi give up da wannan auren na d’an sa, amma banda haka shi da kansa xai iya sa Abuturrab ya saketa don har cikin ransa bai ji dadin wannan lamarin ba, Lkci daya idanuwan Abuturrab suka kada sosai ya kife kansa da kujera, Abbansa yaji tausayinsa ba kadan ba yana murmushi yyi patting shoulder dinsa cikin kwantar da murya yace “Abu me kyau kayi my son, and i am proud of you, Allah kadai ya san ladanka, kar ka damu it shall be well, Allah yayi maka albarka, and kada ka sake tunanin sakinta a ranka shine xai yi helping matters, ka xauna da ita tunda ka aureta, you won’t regret it in sha Allah coz you’ve got a good heart, nasan wataran xaka yi alfahari da ita….” Da sauri Abuturrab ya dago ya kalli Abbansa da jajayen idonsa, ji yayi xaxxabi na neman kara rufesa, amma tunawa da yayi xai saketa ba tare da sanin kowa ba sai ya ji hankalinsa ya d’an kwanta, Abba yace “Xuwa yaushe xata tare din yanxu?” Abuturrab ya kalli Abbansa a sanyaye, Abba yace “Let me talk to ur mothers about it first, i hope they won’t be disturb much…” Wayarsa ya dauka ya shiga kiran matan nasa, Abuturrab gabansa ya dinga faduwa don bai san yanda Umminsa da Aunty su kuma xa su dau lamarin nan ba, ba a dau lkci ba duk suka shigo, Abuturrab ya kalli Abbansa a hankali yace “Can i excuse my self sir…” Abba yace “Sure dear” Mikewa yayi ya nufi kofa walking slowly, Ummi ta bi sa da kallo, tun a shekaranjiya ta san abu na damunsa yana cin sa har cikin ransa, though tasan da kyar ya gaya mata koma meye da ya shafesa sai dai kishiyarta amma wannan karan ta lura ita din ma bai gaya ma ba, hakan yasa abun ya dameta sosai tun daga jiya bata da nutsuwa, don duk da baya gaya mata sabgarsa in dai xai gaya ma Auntyn da sauki, ko ba komai ita ma tana basa shawaran….. Aunty da ta bi sa da kallo tace “Alhaji ko ya gaya maka damuwarsa, tun safe nake fama da shi yace min ba komai, kuma nasan ba gaskiya bane, and this is so unlike him” Abba ya d’an sauke ajiyar xuciya yace “Kiran da nayi maku kenan yanxu” Duk suka maida hankali kan Abba don jin damuwar Abuturrab din.