Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 28

Rufewa Laylah kofa tayi tareda matsawa ta juya tabar gurin gabaki daya
Yana zuwa A Abdoul ya bude Masa dayan bangaren yashige ya rufe ya zagaya yashiga gaba ya tada motar suka bar asibitin.

Suna Isa gidan ga mamakinta saitaga har ankira home cleaner tagama gyare koina a gidan sai sanyin Air-con da qamshin hayaqin humidifier Dake fita.

Daga Palo A Abdoul ya tsaya tareda kallon Mai aikin data Gama komai har abinci yace zata iya tafiya akan sai gobe idan tadawo sbd ta kamfanin da aka daukota ake payment din kudin hidimar dazatai na tsawon sati uku da aka biya.

Bayan fitar A Abdoul da Rosalie bedroom dinta ta nufa
Shima dayan bedroom din ya nufa Wanda dama Bata taba shigaba Dan jikinta ya Bata nasa ne sbd tunda sukazo dakin a refe yake bai taba buduwaba.

Zama tayi bakin gadon dakinta tareda Ciro wayarta ahankali ta kunna massages din anty Sa’adah da Anne Suka fara shigowa hardana Mum Na’ima da Cindy.

Daya bayan daya taringa Binsu tana Kira suna jimawa suna magana kafin tagama da kowannensu ta aje wayar Bayan ta sanyata silent Babu kuma Wanda yasanda tayi gangancin fadawa tayi rashin lafiya bare asalin maye rashin lafiyar.

Ta bangaren A Abdoul duniyace tadawo Masa sabuwa ranar sbd duk da cikin Ms Laylah ya bare garesa wani babban farin cikine tunda alamu ya nuna Sir turakinsa nada Rabon samun haihuwa da magaji sbd har cikin ransa yanajin duk wani radadin damuwar Turaki Kamar yanda yake Jin farin cikinsa har cikin tsakiyar ransa Dan Haka wani irin farin ciki yake ciki ayau din Dan Haka ya Kira Anne yaso fesa Mata labarin saidai akai rashin sa’ar Anty Sa’adah ta dauka wayar saiya kasa sanar Mata Dan kuwa komai daya danganci Turaki da Laylah abin kiyayewane sbd Abune na sirri kuskure daya akai wani yaji Wanda Bai kamata yaji ba za’a iya samun matsala Dan kuwa Ms Na’ima a yanda yasan wasu halayenta da Turaki da kowama Bai saniba zata iya kisan Laylan kokuma abinda yake kwatancin kisan,
Yasan alaqar Laylah da Sa’adah Mai tsananin girma ce saidai bayan Anne bazai iya fadawa kowa hakan ba Dan Haka tunda ta dauka annenma yafasa fada Mata saiya waske ya bige da fira ahankali da Sa’adahn wadda mamakinsa yasata biye Masa har suka dauka lokaci Mai tsayi sosai suna wayar batareda sun sani ba.

Bacci takwanta tayi sai yamma sosai ta farka lokacin taji saukin jikin nata sosai ta sauko gadon ta nufa toilet tayo wanka tana fitowa body oil kawai ta shafa ta sako guntun wando da singlet fara ta zuro slippers ta fito tana qamshin Valentino.
Gabaki daya ta manta da waye a gidan bayan ita ta nufi kitchen ta dauki qaramin kwalin Madara tayi heating dinta Tai zafi sosai ta dauka ta bude ta zuba a cup tafara Sha ahankali sbd zafinta sosai ta fito Palo tana kokarin Isa kujera ta zauna taga mutum yafito sanye cikin fararen Paul Smith T-shirt da farin wando sumar kansa data fuskarsa ta kwanta sai sheqi takeyi duk da alamar Babu abinda ya shafa wanka kawai yayi..

Tsabar rudewa data kamata da faduwar gaban ta manta da Yana gidan cup din hannunta kufce Mata yayi tayi saurin riqewa tareda sakin qaramar qara sbd zubewar da madarar Mai zafi a kirjinta…

Kallon inda madarar ta zube Mata yayi da mamakin rashin kulawarta tayi yawa.

Aje cup tayi akan dining datake kusa tareda daukan tissue Dake gurin hannunta na Dan rawa sbd Jin takunsa na kusantato alamar Nan yayo
Dak saita sake rikicewa Tama Rasa ta Yaya zatai amfani da tissue din ta aje da sauri ta juyo zata bar gurin tajita kirjinsa ya tokare ta sbd tsayuwarsa daf da ita
Ta sauke Kai tareda Dan qanqame dining din data dafa daga bayanta sbd sun matse sosai har sai data dafa dining din ta baya.

Ahankali yakai fararen hannunsa datake bi da kallon Ina Suka nufa ya zaro tissue Mai yawa ahankali ya nufi kirjinta inda madarar ta zuba sosai gashi ba bra ajikinta
Singlet din jikintama farace da Dan transparent Dan Haka madarar na zuba ta lafe a jikinta tana bayyanarda siffar kirjin nata..

Yana Dora tissue din da hannunsa akai tayi saurin rintse ido tana Jan wani irin Numfashi Mara sauti…
Idanuwansa ya zubawa gurin Yana sake gogawa ahankali kamar Wanda ke gudun yaga fatar jikinta Idan ya goga da qarfi….

Yana sake zura hannu cikin rigar Dan gogawa wani shock yasata kasa riqe dining din dasuke jingine ta saki sukai baya ya tarota tareda dafe dining din shi Yana kallon idanuwanta dake rintse kirjinta na bugawa da wani irin qarfi Yana sama da qasa ahankali…

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button