Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 29

Mamuhgee 29_*
Kallon dayake bin hannuwansa masu goge Mata madarar yasata kasa motsawa jikinta na sake sakewa Musamman da hannunsa yakuma shiga rigarta taja wani sabon numfashin tareda qanqame qugunsa batareda ta saniba…

Ahankali ya Dan rintse idanuwansa tsawon seconds hudu kafin ya bude ya saukesu akan bakinta dake fidda numfashi ahankali…
Kokarin sakinsa take Jin shiru ya dakata da goge Mata jikin ta bude idanuwanta tareda Dan motsawa zata zame batareda ta dago ta kalli fuskarsa ba
Dagata yayi cak ya Dora Kan dining din suna fuskantar juna Amma takasa dagowa har lokacin saima bugun zuciyarta Dake qara tsananta Jin irin kallon dayake Mata,
Tsit gurin yadauka ba motsin komai hakama bataji ya motsaba Dan Haka ta dago ahankali ta kalla fuskarsa idanuwanta suka shiga cikin nata yana tsayen ya zuba Mata su Yana kallo cikin wani Irin yanayi data kasa iya tsayawa fahimtar na meye tana kokarin dauke idanuwanta ya Kama fuskarta yakai tasa ahankali yayi kissing cikin tsakiyar bakinta kafin ya saketa Yana kallon reaction dinta
Tayi saurin sake dauke kanta.

Saukar da ita yayi qasa Suka nufi tsakiyar palon ya saketa tareda zama Kan kujera Yana jinginawa a natse da ya kalleta yace”

Kije ki gyara.

Sai data kallesa kafin ta juya ta nufi dakinta tana gaf da shigewa yakuma cewa”

Idan kin gyara ki dawo zakisha magani da abinci.

Batareda ta waiwayoba ta gyada Kai tareda shigewa bedroom din jiki amatuqar mace.

Rigarta ta cire ta nufi toilet ta goge jikinta sosai da ruwa da towel kafin ta fito
Harta Sanya wata rigar batareda ta Sanya bra ba ta nufi kofa ta tuno
Dan Haka ta dawo ta cire rigar ta Sanya bra ta fito.

Waya yake amsawa ko data fito Dan Haka dining ta nufa Kai tsaye taga abincin da komai a jere Rosalie ta jere kafin ta tafi Dan Haka ta nufa kitchen ta dauko ruwa da orange juice ta kawo dining din takoma ta dauko Madara Mai sanyi tana dawowa ta tararda Yana dining din zaune batai maganaba ta qaraso gabansa zatai serving nasa ya riqe hannunta ya kalleta cikin yanayi na nutsuwa yace”

Barshi ki zauna kawai.

Da kansa ya zubawa kansa macaroni salad din da fries.

Ita Kuma Naman kazar da aka gasa tareda potatoes da veggies takeci ahankali.

Tana gamawa da kansa ya nuna Mata maganin daya aje gabanta yace”

Bismillah ko.

Karba tayi bayan ta saci kallonsa Tasha da madara kafin suka baro dining din hannunsa na riqe da nata saidai takasa kallonsa ya zauna kejera tareda zaunar da ita gefensa ya dauka remote ya kunna TV.

Ita kadai ke kallon duk da zamanta a kusa dashi sosai yasa Bata wani Gane kallon shi hankalinsa nakan wayoyin da yaketayi ahakan har lokaci yaja sosai gashi sai yamma Sosai tatashi Dan Haka batajin wani bacci ta Dan kalla agogo taga karfe kusan goma Sha daya na dare Dan Haka ta zare jikinta daga nashi tareda kokarin miqewa
Ya Dan waigo daga aikin dayake dubawa a iPad ya kalleta a natse ya furta”

Zakiyi bacci?

Gyada Kai tayi tareda miqewa tsaye ahankali ta furta”

Saida safe.

Dakinta ta nufa tashige tareda nufar toilet brush tafara Yi tayo wanka da ruwan zafi tana fitowa rigar bacci dasu pant kawai tasaka ta kwanta take bacci ya dauketa.

Washe gari sai 10 ta fito Bayan tayi wanka sanyeda Free gown tana qamshin Valentino ta kalli koina a palon bataga alamarsa saidai qamshinsa daya Kama gidan Kuma daga zuwansa jiya zuwa yau Dan Haka sai ta nufa kitchen ta bude fridge ta dauka Madara tazo tayi heating dinta ta zuba a cup ta tsaya Nan kitchen ta shanye tareda Biscuits tana kokarin barin kitchen din door alerm dinta yayi qara ta nufa kofar ta bude Kai tsaye sai taga Rosalie ta janye daga kofar tana komawa ciki ta zauna palon tareda daukan wayarta takira Sofia Dan Jin Yaya program dinsu tunda kwana biyu bataje ba.

Tana zaune palon tana kallo tana amsa waya jefi jefi tareda sanar kallon kofar bedroom dinsa Jin ba alamar Yana gidan Dole ta sakewarta har Rosalie tagama gyara koina abin mamaki tana zaune Kuma Rosalie din tashiga dakinsa ta gyaro
Harta wuceta saitaga bazata iya shiruba ta kalli Rosalie din tace daga yanzu iya Palo da bedroom dinta saisu kitchen zata gyara tabar dakin Sir AB TURAKI kamar yanda taji tana kiransa.

Abinci ta miqe taje taci a dining Tasha magani Takoma daki ta kwanta tanajin duk ba Dadi
Kadaici takeji na zama guri daya tasaba da yawo koina suna tareda Sofia gashi sofian tace baza tazo gidanba yanzu.

Batajin komai yanzu lafiya kalau take Jin kanta Dan Haka saita shirya da maraicen taso fita kenan sai gashi ya dawo da alama Kuma kamar wani guri Mai Dan nisa yaje ya dawo Dan Haka saita fasa fitar ta zauna gida.

Tare sukai dinner da daddare yauma shi yabata magani Tasha duk da taji sauki shima da kansa yaga alamar hakan
Dayake akwai gajiya tare dashi bai zauna palon ba suna gamawa ya shige bayan ya rakata har dakinta.

Washe gari ma ko data fito ya fita sbd tayi lattin tashi Kuma Rosalie ma tuni ta iso har tayi aikinta tagama Dan Haka breakfast kawai tayi ta shirya cikin pencil skirt blue da sky blue open neck blouse ta saka blazer akai ta fito rataye da handbag din Lv dayake tayi booking mota tana fitowa motar na isowa ta fada Suka nufi gurin karatunsu.

Ko data Isa Sofia na waje tana amsa waya da sauri ta katse wayar tayo gurinta tana washe dukkanin bakinta tana cewa”

Heyyy…look who’s here,

Murmushi Laylah tasaki tana dauke kallonta daga kan sofian ganin irin kallon datake Mata na gulma tace”

Meyene kike mun wannan kallon?

Dariya sofian tasaki ahankali tana qasa da murya tace”

Hmmmn baby banajin wannan Laylan Dana Saba gani ce
Dan wannan gabaki daya qamshin Wata rayuwar takeyi dabam…

Wani banzan kallo Laylah tasake Mata tana wucewa tace”

Bayan rabuwarmu kwana biyun Nan Kika iya gulma ko?

Ciki suka qarasa suna cigaba da magana
Sofia nason Jin gulma Laylan taqi tsayawa suyi mgn Dole ta hakura har su fito.

Sai 12:30 suka fito ta duba wayarta taga saqo kawai ya rubutu mata

“something urgent came up,will be back soon Inshallah..take care.”

Sake karanta saqon tayi tareda sakin Ajiyar zuciya jikinta na mutuwa ahankali ta kalli sofia Dake kallonta tana jiran taji menene tace”

Ya tafi.

Cikin rashin Jin Dadi sofia tace”

Meyesa ya tafi yanzu munason sabon baby fa….

Wani mugun kallo Laylah ta sakar Mata tana cewa”

Muje gidan Aunt siya yau acan Zan kwana ma.

Motar da Suka tsayar Suka shige Sofia na cewa”

Yes eh gwara muje gurin Aunt siya tana buqatan Baki gyara Mai kyau Dan Bata rabo da irin wainnan kayan tana kawosu daga nijar muje ayiwa Abba gyara.

Banza Laylah tayi Mata har suka Isa gidan
Dayake yau Aunt din tana gida sai Suka baje a gidan sukaita ciye ciyensu
Aunt siya dinma data Gama sanin dai matsayin Sir Turakin akan Laylah ba kunya taringa dura Mata magunguna masu tsananin kyau da inganci duk da Laylan taqi Shan wasu Sam Dan ita kunyar hakan ma taji Wai Tasha wani abin Dan bada gamsarwa ga Wanda takewa kallon uba mijin mum dinta.

Da daddare Haka takuma ganin text dinsa na cewan karta manta ta rufe koina.

Ahankali wani boyayyan sanyi ya sauka a zuciyarta ta aje wayar tareda fitowa Tasha Madara Takoma daki ta kwanta zuciyarta na yalwatuwa da farin ciki Wanda take Hana zuciyarta ta yarda na ganin sakonsa ne.

Washe gari suna dawowa daga karatunsu Suka sake bajewa sukaci ciye ciyen Aunt siya
Anan dai suka wuni suna Abu daya sai dare tayi wanka ta kwanta Bayan tagama waya da Anty Sa’adah dake sanar da ita wani labarin na yawan kiran da A Abdoul ke Mata yanzu.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button