Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 31

[7/10, 9:35 PM] +234 704 076 8969: Mamuhgee 31
Bata sanarwa kowa dawowar tata yau na Dan Haka suna sauka taxi Suka dauka zuwa gida,
Gidansu Sofia suka fara biyawa aka sauke Sofia din kafin aka wuce da ita gida.,
Su Cindy dasuka ganta sunfi kowa farin cikin dawowarta suka hau farin ciki da murna,

Mum Na’ima dake main hall(babban palon gidan) zaune tana amsa waya ta aje tareda miqewa tsaye ta ware hannuwanta fuskarta daukeda farin ciki tace”

My baby is back,Masha Allah, Masha Allah.

Qarasowa Laylan tayi tana sake lallausan murmushi itama ta rungumeta a natse Yana cewe”

I missed you mum.

I missed you too Honey,
Yaya hanya?

Lfy kalau mum,na sameku lfy?
Ya Nigeria?

Wata Yar dariya tayi tana cewa”

Nigeria kalau,zanma sake komawa Inshallah Nan bada dadewa sosai ba.

Okay mum Bari naje nayi wanka da sallah.

Bedroom dinta ta nufa tareda siddika dake Jan suitcases dinta cikin murnar dawowarta, Cindy Kuma tuni ta Isa dakin Dan gyarasa kafin tashigo.

Dayake ba wani aiki bane gyaran dakin sbd komai nata na Nan fes zaune a inda yake kamar tananan gashi dama duk bayan kwana daya sai Cindy tayi gyran dakin idan tana aikin gidan Dan Haka ko data shigo Cindyn tagama komai sai qamshi da sanyin Air-con tana toilet tana wankewa.

Saida Siddika tagama cire duka kayan akwatinan data dawo dasu ta jere Mata su tsaf a closet ta fidda masu datti da zata fita dasu,
Handbags da shoes dinta data dawo dasu duka harsu sai data jera komai a gurin zamansa kafin suka fice Suka bar Mata dakin ta tube tafada toilet tayo wanka da alwala.

Data fito sai data fara sallar magriba kafin ta shirya cikin A line frowy dress red kala,ta daure kanta da qaramin silky scarf ta zuro slippers ta fito qamshin posses da volentino na tashi jikinta ta ahankali,
Kitchen ta nufa tana zuwa ta tadda sun Gama komai tuni aka shirya dining Dan Haka Madara ta saka Cindy dimama Mata Takoma gefe ta tsaya suna fira,
ALLAH ya hada jininta sosai da Cindy akwai shaquwa a tsakaninsu Dan sosai suke sakewa suhi firarsu,

Labarin gidan Cindy keta Bata tana saurarenta daukeda murmushi Kan fuskarta,
So take ta tambaya Cindyn ko Abban na gari Amma Bata buqatan hada damar da wani tunani ko kafa akan sanin alaqarta dashi ko kadan sai Bata tambaya din ba sukaci gaba da zancensu har tagama ta zuba Mata a cup ta dauko ta fito zuwa dining sbd lokacin cin Daren yayi tasan mum tana dining din yanzu.

Tun daga kofar dining room data sako Kai ciki qamshin Bois elite yashiga hancinta ahankali,
Lumshe ido tayin ahankali tareda sauke boyayyan numfashi kafin ta qaraso dining din,

Kallo daya yayi Masa da idanuwanta sbd Jin alamar idanuwansa dake yawo akanta,
Ahankali ta dauke Kai tareda zaunawa cikin murya Mai siririn sauti tace”

Barka da fitowa Abba.

Sai daya Mata wani kallon seconds shiga kafin ya dauke nasa idanun akanta ya amsa a natse cikin wata irin kamewa da cewa,

Kindawo lfy?
How was the trip?

Alhmdlh” ta furta tana maida kallonta Kan mum Na’ima data serving dinsa tayi nata tafara ci,
Laylah ta kalleta bsywb ta zuba nata abincin kadan tafara ci kenan mum Na’ima ta dago ta kalleta fuska a sake Sosai tace”

Laylah munyi kewanki a dining kafin ki dawo dinnan,
Gskia next time bazan Bari ki sake tafiya Mai tsawo irin wannan ba, infact ma tafiyan daya wuce sati dayama bazan Bari ba sai aure kawai idan anmiki Zaki tafi gidan wani ki……

Tari ne Mara sauti sosai ya Kama Turakin ba tsammani,
Ya dauki ruwa Mara sanyi dake gabansa yasha ahankali tareda daukan tissues yagoge bakinsa batareda ya dago ya kalla kowaccensuba yaci gaba dacin Abincin nasa a kame.

Satar kallon gefen dayake Laylah kafin ta kalli mum din tana sake murmushi tace”

Mum ba yanzu zanyi aurebafa..

Wata qaramar dariya Ms Na’ima tayi Jin dadin zancen Laylan Dan kuwa har qasan ranta Bata son Laylah tayi aure ko kadan yanzu batareda dukiyan Anne da Turakin tazo hannunta ba ta hanyar Laylan sbd tana Gama karatu tasan dole wasu dukiyan zasu Shiga hannunta sbd ilimin iya kula da huldodin dukiyan data yalwatu dashi Dan Haka tasan tana aure mijinda Laylan zata aura zai iya finta samun dukiyar ita data raineta ta qarfafa Mata gwiwar samun ilimin shiyasa kwata kwata Bata qaunar ko saurayi taga laylah tayi yanzu, idanma shekarunta da lafiyarta sunkai tafara buqatuwa da namiji tayi watsewarta da mazan yafi komai sauki ita Bai dameta ba Amma dai bazata taba barin Laylan tayi aure yanzuba,

Fuskarta cikeda farin cikin zancen Laylah tace”

Hakane my princess,
To Ina fatan kinji dadin Florida sosai?
Baku takura kanku duka da karatuba keda Sofia Kun shaqata kunji dadin garin?

Shiru Laylah tayi tareda Dan dakatawa daga tauna abincin Dake bakinta ta dauki ruwa tana kaiwa bakinta,

Ganin reaction dinta yasa mum Na’ima tunanin wani abun ta aikata a Florida Kuma tunaninta baije Kan komaiba sai Kan saurayi kokuma abin dayafi tsayawa a iya saurayi kawai sai abun yai Mata Dan Dadi kadan ta murmushi Kan fuskarta tana kallon Laylan wani iri tace”

Wani Al’amari Mai Dadi yafaru acan kena…….

Ruwan datashane Suka dawo Mata da sauri tana tari ta dauki tissue da sauri tana goge jikinta ta kalli inda Abban yake zaune taga ya zuba Mata mayun idanuwansa ko a jikinsa saima Kamar dadin tambayar da akai matan yaji ganin yanayin data shiga yasashi miqewa yabar dining din tabisa da ido a sirrance harya fice
Ta waiwayo ta kalli mum har lokacin tarinta Bai tsayaba tace”

Mum please…

Dariya Ms Na’ima tayi tana cewa”

Ok ok am just kidding kinji,
Nadauka nasamu siriki ne acan har kunyi nisa shiyasa.

Kai tsaye tace”

No mum,banda ko wane saurayi haryanzu.

Tare suka fito da mum din daga dining room tana ganin mum ta nufi hanyar Hawa sama ta dauke Kai tareda nufar dakinta tashige tana daukan wayarta dataga alamar shigowan sako ko Kira.

Massage ne yashigo wayar ta zauna tana budewa..

“You look great today, sleep well”

Numfashi ta sauke ahankali murmushi na saukar Mata saidai zuciyarta nashiga wani yanayi na sanyin jiki Dan haka kiss emoji kawai ta tura Masa tareda miqewa ta sauya kayanta zuwa na bacci tazo ta kwanta Dan bacci ma taji tanaji kawai.

Washe gari ba school sbd saisun kwana biyu da dawowa kafin su fara zuwa Dan Haka da wuri tayi wanka ta nufi kitchen da ita sukai aikin breakfast,
Bayan angama komai ankai dining sai data dafa green tea ta hada daban takai dining din kafin takoma dakinta ta sauya pink gown din dake jikinta zuwa Riga Da pencil skirt na Burberry red ta dawo dining din.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button