Sun Jima ahakan cikin tsananin kewan junansu kafin ta sakesa ahankali ta dago tana kallonsa idonta har lokacin da sauran hawaye tasaka fararen yatsun hannunta Dake sanye da zoben white gold guda biyu marasa hayaniya ta share hawayenta tareda sakin murmushi tana sake kallonsa tace”
Abba Allah yabaka lafiya naji muryanka kaman yanda kowa ke ji muryan mahaifinsa,
Naji ka Kira sunana da bakinka ka sanyani wani aikin.
Kyakkyawan murmushi yasake Mata Yana Dan rufe ido alamar ranar na zuwa Inshallah.
Momy na zaune har lokacin tana jinsu Bata waiwayo ta kallesu ba,
Haka ta wuni tana zaune maqale kusada abbanta har yamma,
Abinci ma aranar itace ta basa sbd tayi tsananin kewar hakan sai gap da magriba Anty Sa’adah ta iso Kuma daga airport direct asibiti tazo Dan Haka tana shigowa da tsananin murna na farin ciki taso tarbanta saidai ganin Momy na zaune Kuma ita ta tarba Yar tata shiyasata dakatawa Bata Isa gurin Sa’adah din ba saidai daga inda take cikin takaita bayyanarda farin cikinta sbd gudun batawa Momy Rai tayiwa anty Sa’adah din barka da zuwa tareda miqewa ta janyo Dan qaramin akwatinta na lv guda daya data zo dashi takai gefe ta aje.
Gurin Abba Sa’adahn tazo cikin nutsuwa da farin cikin ganinsa ta zauna gefensa tana gaidasa tareda Masa ya jiki.z
Zuba Mata idanuwansa yayi Yana kallonta cikin farin ciki tareda tausayinta Mai girma cikin ransa,
Tabbas Sa’adah Mai hakuri da tawakkali ce tunda Bata Bari son abun duniya ya hanata barin Yar uwarta ta auri Wanda akace dinba,
Kawu saidu ya sanar dashi komai Dan Haka har abada bazai daina sakawa Sa’adah albarka ba gode Mata.
Tunda Anty Sa’adah ta iso Momy take Nan Nan da ita sai jikin Laylan yasake yin sanyi tanason sakewa da anty Sa’adahn Amma ta Kama kanta sbd gudun bacin ran momyn.
Ana Gama sallar magriba saiga A Abdoul yayi knocking ahankali yashigo dakin sanye cikin white Balenciaga sleeves da blue Armani trousers sai jacket din sanyi Mai tsayi datakai gwiwarsa,
Qamshin turarensa na D&G na tashi ahankali ya kalli Momy cikin tsananin girmamawa ya gaidata…
Dayake ta Saba dashi sosai sbd komai na dawainiyarsu shi yake zuwa yayi shiyasa sukeda sabo cikin sakewar fuska da kulawa tace”
Lafiya kalau Abdoul, Jiya saika tafi baka Bari nadawo ba.
Murmushi yayi Yana cewa”
Nakira wayanki naji akashe shiyasa na wuce din kawai…
Zatai magana sukaji shigowar Turaki Wanda qamshin turarensa yafara shigowa dakin kafin shi din yashigo Yana sanye cikin navy blue Ralph Lauren Kaftan St, Hasken fatarsa yafito sosai sbd duhun kayan jikin nasa hannunsa dake sanyeda agogon diamond Rolex riqeda wata paper bag da tsadadden turaren dayasan Amininsa Yana amfani dashi tun lokacin Yana lafiyarsa cikin arzkikinsa yasaba duk zaizo gurinsa saiya zo Masa dashi Dan Haka cikin nutsuwarsa da kamewarsa ya qarasa shigowa dakin duk sukai tsit suna Dan rage kallonsu daga kansa,
Sa’adah kallo daya tayi Masa ta Dan sauke Kai tareda bude Baki ta gaidasa cikin girmamawa,
A hankali ya amsa tareda Dan kallon gefen Momy suka gaisa Yana tambayarta jikin Abban Dake kallonsa da dukkanin kauna irin ta Dan uwa na jini dayake jinsa.
Daga inda take zaune ta saci kallon abbanta da Momy harma da anty Sa’adah kafin ta Dan saci kallon gefensa taga yanda kwarjininsa duk yabi ya cika idon dukkanin wainda ke dakin sai Taji kunyar da Babu dalili ta kamata Dan Haka ahankali itama cikin nutsuwa kanta a qasa tace”
Abba barka da shigowa.
Bai waiwayoba ya amsa Mata a gajarce cikin kamewa sbd idan yayi gangancin waiwayowa ya kalleta gurin amsawa za’a iya gane halinda suke ciki Dan Haka gabaki daya hankalinsa na Kan Mahmoud dayake magana dashi.
Miqewa tayi ta sulale ta fito Momy ma dama duk fita zasuyi Dan Haka gabaki dayansu Suka fito dakin aka barsa daga shi sai Abban.