Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 35

Mamuhgee 35_*
Suna fitowa waje Momy taja Sa’adah suka nufa inda zasu zauna taje ta siyo Mata ginger drink Mai zafi suka zauna suna magana.

Itama zama tayi a can gefe tareda fidda wayarta jiki amace ta Rasa wa zata Kira saiga Kiran Anne ya shigo wayarta wani sanyayyan murmushi ne ya sauka Kan kyakkyawar fuskarta ta dauki wayar anatse cikin farin cikin Jin Annen tafara sauke nannauyan numfashi tace”

Nagode Anne.

Murmushi Annen tasake Jin irin numfashin da Laylan tasake na samun saukin damuwa kafin tace”

Kina asibitin ne haryanzu tareda Momynku kenan?

Sunkuyar da Kai tayi takuma sauke wani numfashin kafin ta dago ta saci kallonsu anty Sa’adahn yanda Momy ke magana da ita cikin tsananin kauna da kulawa irin ta mahaifiya zuwa ga yarta,
Jin tayi idanuwanta suna kokarin cikowa da hawaye akaro na farko dataji kewa da maraicin rashin uwa,

A da rayuwarta batasan Jin Dadi,yanci ko walwalaba,
Batasan wani kwanciyar hankaliba ko wata yancinda har zatai kewar uwa,
Batada lokacin kanta batada na mahaifinta koyaushe rayuwarta acikin hidima da dawainiyar Momy da Anty Sa’adah da dangin Momy take,
Bata samu yancin kewan tata mahaifiyarba sai yanzu datai rayuwar yanci,
gata,
Jin dadi da kwanciyar hankali,
Tabbas itadin marainiyace badan Anne da Abba turakiba harma da mum Na’ima dake kishiyarta sun Bata kauna da kulawar da Bayan abbanta da anty Sa’adah Babu Wanda ya taba kaunarta Haka…
Meyasa Momy bazata kaunacetaba Koda so dayane?
Aranta har Koda yaushe Momy zataci gaba da zama uwa gareta Koda bazata taba kaunartaba ko yafe Mata laifin mahaifiyarta datake kallonta dashi…

Kokarin maida hawayenta tayi a sanyaye tace”

Anne inason zanbiyosu Abba idan an sallamesu.

Murmushi Annen takuma Yi a natse tace”

Karatun naki fa?
Kinriga kin fara Haka Zakiyi hakuri ki lallaba ki Gama kafin kidawo
Koba komai dawowarki ai Dole ne idan har za’a sanarda Na’ima matsayinki zamanki acan nada hadari,
Dan Haka kici gaba da kiyayewa karkiyi maganar da kowa Koda Wasa fa,
Ba yanzune lokacinda zata saniba sbd akwai zafi kishi Sosai agun Na’ima kici gaba da rayuwanki bakida alaqan komai da Turakin Bayan ta Abbanki ayanzun tunda nanma bakowa yasan matsayinki agunsa dinba saikin Gama karatun tukuna Zaki dawo kafin ayi komai kowa ya shaida ke matarsace…

Tsit Laylan tayi sbd batada bakin mgana akan maganar Anne Dake gargadarta akan ta tsaya a alaqar abba da ‘yar riqonsa tsakaninta da Abba Turakin,
Kunyar kantama taji ta kamata sosai tunowa da dabatai barin cikin data samuba tayaya zata fuskanci kowa da cikin?
Ko sama da qasa zata hade tasan bazata fadawa mum Na’ima cikin waye ajikintaba,
Annenma batasan tayaya zata iya Bari ta hada Ido da itaba da ciki ajikinta,uwa uba Anty Sa’adah da afarko take Masa kallon mijintane…..gasu umma Jamila da Suma Suka Fado Mata arai
matuqar kuwa sukaji cikin jikinta na Wanda sukasan mijin anty Sa’adah ne umma Jamila zata iya ratayeta sbd irin tsanar datake Mata da bakin dasuke Mata Mai jinin cin Amana..

Wato tabbas akwai tashin hankali idanda cikin Bai fita ba,
Hakama akwai masifa Mai girma agabanta idan ta kuskura tsautsayi yasata samun wani cikin…

Wannan tunanin ya daga hankalinta matuqa sbd duka wannan tunanin baizo kantaba sai yanzu da maganar Anne ta tunatar da ita,
Shin yazatai da rayuwarta duk cikin Abban ya bulla ajikinta bayan Babu Wanda yakawota yace gatanan ankawota gurin mijinta,
Daga sama zancen Aurenta dashi ya bayyanar mata…..

Gama wayarta tayi da Anne ba’a cikin nutsuwartaba sbd yanzu Kam komai ya tsaya Mata akai,
Uwa take buqata ayanzun kamar Momy Dake dawainiyar Sa’adah Dan ta kwanta jikinta ta sanar da ita abinda yake faruwa a rayuwarta,
Anty Sa’adah ce tamkar uwa gareta wani lokacin,
Ita kadai take iya fadawa komai Amma Momy bazata taba barinta sakewa da itaba saboda tasan itama tayi kewar yarta Dan Haka take kallonsu daga nesa cikin burgewa da suna kulawa da juna….

Fitowa yayi daga dakin Abban wayarsa a hannunsa Yana kokarin daga Kiran daya shigo wayar idanuwansa suka sauka akanta jikinta duk amace ya zubawa su momyn Ido…

Yana iya hango yanayinda take ciki na kallon datakewa su momyn,

Wani iri yaji har cikin ransa na yanda take a kadaice tana musu kallo daga nesa..,

Jin kamar zuciyarsa bazata iya daukaba yasashi dauke Kai daga kallon gurin ya nufi inda take
Tun kafin ya qaraso taji qamshinsa na tunkarota ta Dan waiwayo ta zuba Masa fararen idanuwanta dasuka Tara hawaye saidai Basu saukaba tafara kokarin maidawa tareda sauke Kai daga kallonsa..

Yana zuwa Inda take a natse ya furta”

muje sanyi Yana sauka,
Mahmoud yariga yayi bacci.

Kallon inda su Momy suke tayi tana cewa”

Inaso zanbi su Momy da Anty Sa’adah Nima na kwana gurin Momy.

Kallonta ya juyo yayi dakyau kafin ya dauke ido Yana kashe wayar hannunsa yace”

Kin tabbata Zaki iya binta?

Gyada Kai tayi Ahankali tana Dan dagowa ta kallesa.

Ba musu yabarta Akan tabi su momyn yatafi A Abdoul yakaisa gida yadawo ya daukesu zuwa gidan momyn.

Da A Abdoul yayi parking suka fito harda Laylan daga mota
A Abdoul kuwa juya motar yayi ya wuce,
suna kokarin shiga gidan Momy da Bata lurada harda Laylan ta sauka motarba ta tsaya tareda kallonta takuma dauke Kai lokaci daya tana cikin yanayinta na rashin son doguwar magana da Laylan tace”

1sitting room 1bedroom ne
Ki koma masaukinki zamu matsu da yawa.

Kasa motsawa Laylah tayi sbd wani irin yanayi daya shigeta
Ta sauke Kai Dan dama Bata wani dago Kai gaban momyn Sosai..

Anty Sa’adah da tun a asibiti take fama da momyn itama jikinta saiya mutu cikin rashin Jin dadin abunda momyn ta fada tace”

Momy tariga tazo Kuma zakice ta koma?
Zata iya kwanciya a Palo Mana,
Nima a palon Zan kwana
Zan kwana tareda ita.

Wani kallo momyn tayiwa Sa’adah Kai tsaye tace”

Nafada cewan zamu matsu bance Babu gurin kwanan bane,
Idan ankwanan zamu matsu a gidan shine maganata,
Meye na damuwa tunda tanada masaukin dayafi nan
Takoma can koba komai kowa zaifi sakewa a inda yake…..

Magana anty Sa’adah tasake bude Baki zatai Laylah ta riqe hannunta cikin nutsuwa tareda girgiza Mata Kai cikin sanyin jiki tace”

Saida safe Momy,
Anty Sa’adah good night.

Juyawa tayi tabar gurin tafara takawa ahankali tana tafiya saiga taxi ta tare tashige batareda ta waiwayoba.
Sai data Shiga mota hawayen dake idonta suka gangaro
Ta Sanya hannu ta share ahankali sbd har zuciyarta tayi kewan kasancewa dasu yanda suka saba,
Ita da anty Sa’adah da momyn.,
Taso yau dai Rana daya su kwana guri daya tayiwa Momy hidiman data Saba Kona dare dayane sbd tasan ita kanta momyn bazata Rasa kewan hidiman datake Mataba Koda sau dayane.

Akwai nisa Dan Haka ko data Isa gida qarfe goma ta Dan wuce,
Kai tsaye ta saka codes din kofar ta bude tashigo,,
Yana zaune palon sanyeda white pyjamas Yana Shan redbull drink ahankali idanuwansa Kan tv Amma da alamar ba kallon yakeba
Kaman yasan zata dawo din shiyasa yake zaune apalon.

Waiwayowa kadan yayi ya kalleta bayan ya kalli time,
Ya Dan rufe idonsa ya bude batareda ya iya cewa komaiba saidai zuciyarsa ta dauki ‘daci,

Ya kalli fuskarta datake kokarin boye damuwarta yaga yanda idanuwanta suka sauya ya dauke Kai tareda aje drink din hannunsa batareda yace komaiba,

A qaidarsa Abu yayi tsananin Bata ransa baya magana dauke ido yake akai sbd kaucewa fitina shiyasa ba’a Gane fushinsa da bacin ransa a saukake.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button