Mamuhgee 42_*
Yasan Ms Na’ima Bata Nan ta tafi Nigeria sbd ta sanar Masa da suna waya akan zata tafin, Bai Saba hanata fita ko tafiyaba shiyasa baice komaiba Bayan Allah yakai lafiya Dan fitarta Bata fada Masa dama tafiyarce dai wasu lokutan take sanar Masa bayan tagama tsara abarta.
Hutawa yayi sosai bayan dawowarsa wannan tafiyar sbd sakewar dasuka samu dagasu saisu sai Cindy wadda take tamkar secretary din Laylah Dan yanzu maganinta ma Sofia ta damqa Mata ita ke Bata anan gida tana Sha Amma a dakinta yake boye sbd gudun tsautsayi.
Samun wannan sabuwar damar dasukai yasa suqa qarasa lalacewa juna Dan kuwa yanzu tamkar wasu chewing gum suke musamman da cikinta yaqe qara Masa Jin nutsuwa da ita duk da baisan tana daukeda cikinba,
Itama cikin yasa taqarasa lalace masa,
Babu inda basa shaaninsu musamman dayake ba sauran wata kunya a tsakaninsu bayan kamewarsa Dake motsawa wani lokacin musamman idan Yana tuno Amininsa sai yanajin wani iri duk ranarda shaidar abinda ke faruwa tsakaninsu ta fita wato ciki idan tasamu.
*Babbar ranar farin cikinta tasameta ne lokacinda Abban ya sanar Mata an sallami abbanta sbd saukin daya samu Yana iya magana yanzu harma da motsa jikinsa yayi komai
Tafiya ce kawai bayayi yanzu Yana Kan kujera sai antura Amman tafiyarma zaiyi ahankali wata Inshallah.
Rumgumesa tayi tana kukan farin cikin samun lafiyar abbanta,
Jin takeyi inama zata zauna guri daya da abbanta,
L.A Suka tafi inda mum tuni ta wuce samun labarin tsautsayin Sa’adah Dan Haka ba kowa agurinsa Saida suka Isa,
Harhada komai sukai Suka Gama duk wasu formalities na sallamar Suka tarkata suka kaisa wani lafiyayyan hotel da Turaki yasa A Abdoul yayi Masa booking.
Acan suka barta ta wuni da abbanta suna magana akan yanda zamanta yake da Ms Na’ima cewan batasan ita Matar Turakin bace.
Abba Bai wani ja zancen da tsayiba sbd yanda zancen ke sanyata kasa hada ido dashi,
Hakama shima zancen baya Jin sakewa acikinsa tunda ‘yarsa ake magana da Amininsa dayasan haryanxu baigama karban aurenba,
Ya riqeta ne saboda inganta rayuwarta harma data ‘yar uwarta,har abada bazai daina gode Masa akan hakanba,
A taqaicema ya karba auren ne sbd halinda shi yake ciki yanzu kuma tabbas bazai takura Aminin nasaba zai basa tabbacin zai iya sauwakewa Laylan aurensa tunda ba Kamar taimakone yayiwa Wanda yake halin ciwo da rashin gata,
Yanzu Kuma alhamdllh yasamu lafiya, Kuma Laylan tasamu ilimi Mai zurfi ko ahaka zasu iya tallafar rayuwarsu.
Da wannan tunanin Abban ya yankewa kansa shawaran idan ya natsa bayan komawarsa guda zai bawa Turaki damar ya sallami Laylan tunda dama Babu Wanda yasan da aurenta dashi Kuma yasan bazai taba karbanta amatsayin matarsaba sbd shi da Zainab Dan ‘yarsu tamkar ‘yarsa daya haifane.
Sai dare A Abdoul yazo ya dauketa suka koma gida sbd Turakin Bai dawo gurin abbanba barinta yayi ta sake da mahaifinta suyi magana yanda yakamata sbd a kusancinsa da ita yagama fahimtar irin girman kauna dake tsakaninta da Abbanta Wanda duk ya kalli hakan ranarda ya biyawa Mahmoud sadakin zainab take Fado Masa Rai irin yanda suke tsananin son junansu baitaba saka ran ya biya sadakin da za’a hadu a Haifa Masa Mata bane…
Bayan sun kwanta tana cikin jikinsa kwance da wata qaramar fingilalliyar rigar bacci data Gama barkewa ta Samanta sbd irin yamutsar dasuka Gama Amma dayake tanason bacci da rigar sbd rashin nauyinta yasa ta maidata ahakan sbd saman ne ya Gama fincike hannuwan rigar dasuke sirara.
Cikin sigar roko da Yar yarinta ta bude Baki ahankali tace”
Abba, zanbi Abbana Nima Dan Allah naje Nigeria..
Ahankali ya lumshe fararen idanuwansa masu Dan girma ya budesu akan bakinta da yayi maganar kafin ya bude Baki ahankali cikin nutsuwa yace”
No.
Marairaice murya tayi tareda sake shigewa jikinsa tana zagaya hannuwanta zuwa bayansa tasake Dan rugumarsa Suka manne fiyeda yanda suke tace”
Please Abbahhh.
Nayi kewan gida,dasu Anne,
Inason bin Abbana gida Dan Allah.
Zakije Amma ba yanzu ba saikin Gama exams dinki tukuna na wannan session din,
Karki manta kina last year dinki.
Sanyi jikinta yayi tace”
To waye zai kaisa gidan tunda momy ta tafi?
Tare zamu tafi Inshallah gobe Zaki koma Atlanta daga Nan zamu wuce ki zauna gida kiyi karatun exams.
Sanyi jikinta yakuma yi ta kallesa tana Jin kewarsu duk su dukan shida abbanta tun Basu wuce ba ahankali da sanyin murya tace”
I will miss everyday Abbah….
Please kadawo da wuri tunda mum tace ba yanzu zata dawoba zanyi kadaici da yawa bakanan mum batanan ga abbana ma ya tafi.
Kissing lips dinta yayi ahankali tareda gyada Mata Kai batareda ya bude Baki yayi maganaba Dan kewarta zaiyi Kamar sabuwar haihuwa yasani shima saidai ba Daman nunawa shiyasa yake wahala yanzu duk yayi tafiya sbd rashinta Yana azabtar da zuciya,Ruhi da gangar jikinsa.
Da Dan zazzabi ta kwana sbd kadaici data fara tun lokacin da Yar damuwar zuwa gidan dataso Yi,
Har asuba jikinta akwai zafin zazzabi irin Wanda yake Dan damunka Ahankali ahankali,
Da safe guraren 10 Da kansa ya shiryata cikin kayan sanyi da qatuwar jacket Suka Fito yakaita tayi bankwana da abbanta Amma Bai shigaba a mota ya tsaya sbd idan yashiga bazai iya fitowa kaita airport da kansa ba saidai A Abdoul yakaita Dan Haka Bai shigaba Ita kadai tashiga tareda A Abdoul Suka Gama suka fito.
Tunda suka Kama hanyar airport take kwance jikinsa Yana kissing hannunta akai akai har Suka Isa airport din A Abdoul yafita motar yabarsu.
Fuskarta ya Kama yayi kissing bakinta ahankali tareda shafa fuskarta ahankali da muryarsa Mai dadi da aji ciki yace”
Ki kula sosai okay??
Gyada Kai tayi tareda Dan shigewa jikinsa ta rumgumesa yanajin zafin jikinta ahankali.
Dagota yayi ya Kama hannunta Suka fito motar Yana riqe da hannunta A Abdoul na bin bayansu da qaramar suitcase dinta.
Yanayin yanda taketa neman rikice Masa ta sanyashi sauya ra’ayi akan rashin barinta zuwa yasa Basu jira lokacin tashin jirginsu ba suka tafi Suka barta.
Yamma sosai ta iso gida bayan sofia taje har airport ta daukota da motar gidansu sbd zazzabinta qarfi yayi kafin su iso Dan Haka suna isowa gida daqyar da Taimakon sofia tayi sallah Cindy ta kawo tea Mai dumi da cupcakescake taci guda biyu Tasha magani ta kwanta a wahalce.
***Anne ce zaune tareda baqi suna magana saiga isowar baqi halima tazo ta isar Mata dama tagama da baqin zasu tafi ne Dan Haka Kai tsaye aka shigo dasu Momy…
Momy CE tareda Haj Karima Dake zaune a Abujan suka zo gidan,
Tunda momy tadawo tana gidan Haj Karima anan Abuja sbd Sa’adah tana zuwa dubata akai akai,
Bata taba zuwa tareda Haj Karima ba sbd gudun sugano gaskiyar ayi tashin hankali batareda sa’adahnta tagama karatunta tafara aiki Mai kyau ba su Bata Mata gobenta Dan kuwa saninta ne bazasu taba barwa Allah ba Koda Sa’adah bazata aura Turaki ba sunfi son ayi biyu Babu Dan kuwa dukkaninsu qiyayyar mahaifiyar Laylah da Laylah a jininsu take mai qarfin gaske.
Qarasowa sukai Anne na musu barka da zuwa cikin mutuntawa da sakewar fuska.
Mintuna qalilan aka zagayesu da kayan tarban baqi,
Drinks ne masu sanyi da sabon madarar nono Mai sanyi sai dambun Naman kazar sai snacks.
Haj Karima duk gaisawa da firar da Anne ke Dan Jansu hankalinta nakan tsabar dukiya Dake magana koina a gidan,
Ta duba tasake dubawa Babu wani Abu a gidan da bana manya bane Dan Haka ita saima taji hankalinta yakuma tashi akan ayita Mai yiyuwa bazai yiyuba Sa’adah na aure gidan arziki irin wanna ace Basu more Mataba bayan dawainiyar dasukai da uwarta da ubanta ya lalace akwance da sunan ciwo,